Jibwis Gyallesu Zaria

Jibwis Gyallesu Zaria Jibwis Gyallesu Zaria

06/04/2025
05/04/2025

Pray before you are being prayed upon

Innalillahi wa inna ilaihi rajiun Allah yayima Alkali Aminu Jumare rasuwa, Sallar Janazah Masallacin Haruna Danja Tudun ...
27/12/2024

Innalillahi wa inna ilaihi rajiun
Allah yayima Alkali Aminu Jumare rasuwa,
Sallar Janazah Masallacin Haruna Danja Tudun wada Zaria, Bayan sallar Jumua

Allah ya jiqan Malam

17/12/2024
GAYYATAR WA'AZIN ƘASA DA SEMINAN ‘YAN AGAJI A BAUCHI DAGA RANAR 18-22 GA DISAMBA 2024 A BAUCHIShugaban JIBWIS Sheikh Ima...
16/12/2024

GAYYATAR WA'AZIN ƘASA DA SEMINAN ‘YAN AGAJI A BAUCHI DAGA RANAR 18-22 GA DISAMBA 2024 A BAUCHI

Shugaban JIBWIS Sheikh Imam Abdullahi Bala Lau da shugaban majalisar malamai Dokta Ibrahim Jalo Jalingo da daraktan ‘yan agaji Injiniya Mustapha Imam Sitti na farin cikin sanar da bita wato semina ta ‘yan agaji da za a gabatar a makarantar kimiyya da fasaha ta Abubakar Tatari Ali wato Abubakar Tatatari Ali Polytechnic (ATAP) da ke Bauchi daga ranar 18 ga watan nan na Disamba 2024. Taken SEMINA “YAKI DA RASHIN TARBIYYA DA SAMAR DA AIKIN YI GA MATASA”

Za a kuma gudanar da gagarumin wa’azin kasa a ranar Asabar21 ga wata da dare a nan Bauchi inda washegari Lahadi 22 ga wata za a yi taron rufe bitar.

Babban bako na musamman mai girma shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu GCFR.

Mai masaukin baki mai girma gwamnan jihar Bauchi Sanata Bala Abdulkadir Muhammad Kauran Bauchi.

Shugaban taro mai ba wa shugaban kasa shawara ta fuskar tsaro Malam Nuhu Ribadu

Iyayen taro mai martaba sarkin Bauchi Dokta Rilwanu Sulaiman Adamu da mai martaba Sarkin Hadeja Alhaji Adamu Abubakar Maje

Manyan baki ministan lafiya Dokta Muhammad Ali Pate

Ministan harkokin waje Malam Yusuf Tuggar

‘Yan majalisar dattawa na Bauchi Sanata Shehu Buba, Sanata Abdul Ningi da Sanata Sama’ila Kaila da dukkan ‘yan majalisar wakilai.

Babban shugaban kamfanin man fetur na kasa NNPCL Mele Kyari Kolo

Sanata Muhammad Danjuma Goge da

Sanata Abdul’aziz Yari

Malamai da za su gabatar da wa’azi sun hada da:

-Sheikh (Dr) Abdullahi Bala Lau
-Sheikh Dr. Ibrahim Jalo Jalingo
-Sheikh (Dr) Yakubu Musa Hassan Katsina( Sautus-sunnah)
-Sheikh Usman Isa Taliyawa Gombe
-Sheikh Abbas Muhammad Jega
-Sheikh (Dr) Muhammad Kabir Haruna Gombe
-Sheikh Habibu Yahaya Ƙaura
-Sheikh Barista Ibrahim Sabi'u Jibia.
-Sheikh Farfesa Abdullahi Saleh Pakistan
-Sheikh Gambo kyari Maiduguri
-Sheikh Aliyu Abdullahi Telex
-Sheikh Khalid Usman Khalid Jos.
-Sheikh Abdulbasir Isah Unguwan Mai kawo
-Sheikh Dr. Isma'ila Kumo
-Sheikh Dr. Ibrahim Abdullahi R/Lemu
-Sheikh Dr. Ibrahim Idris (Darus-sa'ada)
-Sheikh Dr. Abdulkadir Saleh Kazaure
-Sheikh Abubakar Abdussalam Baban Gwale
-Sheikh Farfesa Zubairu Madaki
-Sheikh Farfesa Mansur Isa Yelwa
-Sheikh Lawan Abubakar Triump

-Alaramma Abubakar Adam Katsina
-Alaramma Ahmad Suleiman Kano
-Alaramma Nasiru Salihu Gwandu
-Alaramma Usman birnin kebbi
-Alaramma Ibrahim Yahuza Bauchi
-Alaramma Bashir Abubakar Gombe
-Alaramma Abdul'azeez Azare da sauran malamai da alarammomi

Sanarwa daga Sakataren JIBWIS na kasa, Sheikh Dr. Muhammad Kabir Haruna Gombe, ta hannun Ofishin kwamitin Labaru na kasa da hadin gwuiwar ofishin Jibwis Social Media, Nigeria

Allah ya bada ikon halarta Amin

Jibwis Nigeria TV
Jibwis Gyallesu Zaria

Address

Panmadina Road Gyallesu Zaria
Zaria

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Jibwis Gyallesu Zaria posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share