26/08/2026
Ranar Harshen Hausa ta Duniya!
Sheikh (Dr) Muhammad Nasir Kabara ya bada gudunmawa gagaruma wajen haɓɓaka da bun ƙasa Harshen Hausa a Nigeria da Africa. Yayi amfani da Harshen Hausa wajen koyar da Sunna ta Annabi (S.A.W) da kuma yaɗa aƙidar Ash'ariya, mazhabar Malikiya da kuma koyar da sufanci duk acikin Harshen Hausa don sauƙaƙawa ɗaliban ilimi. Wasu daga cikin nasarorin da ya samu cikin bunƙasa Harshen Hausa sun haɗa da:
1) Shine mutum na farko a duniya da ya fara fassara Alƙur'ani zuwa Harshen Hausa acikin mujjaladai 4. Ya sawa Tafsirin suna da, " IHSANUL MANNAN" Yayi hakane don kusanto da ma'anonin Alƙurani mai girma ga ɗalibai da kuma bunƙasa Harshen Hausa.
2) Ya fassara baban littafin nan da yake koyar da ƙaunar Annabi (S.A.W) na Qad Iyad, " KITABU SHIFA FI TA'ARIFI HUQUQUL MUSTAPHA " shima Sheikh Nasir Kabara shine mutum na farko da ya fassara littafin zuwa Harshen Hausa don koyar da ƙaunar Annabi (S.A.W) ga al'ummar Hausawa da kuma bunƙasa Harshen.
3) Yana da Diwani kala-kala na waƙoƙi daya rera cikin Harshen Hausa don koyar da ilimin Tauhidi, Fiqhu, Sufanci da ragowar ilimai cikin Harshen Hausa. Wanda ya bada gudunmawa ga al'umma musulmai inda s**a koyi rukunan musulunci cikin waƙe na Hausa, wanda Sheikh Nasir Kabara ya bada gudunmawa.
4) Hakana, Yana da Diwani mai suna , " JAMI'U KANZUL MUDALSAM" wanda ya rubuta cikin Harshen Hausa.
Akwai abubuwa masu tarin yawa daga cikin gudunmawar da ya bada wajen haɓɓaka Harshen Hausa da inganta shi. Allah Ya ƙara Rahama ga Sheikh (Dr) Muhammad Nasir Kabara.
~Sheikh Sidi Musal Qasiyuni Kabara.