Ya Ku Ƴan Uwa

Ya Ku Ƴan Uwa Mu gudu tare, mu tsira tare!

18/08/2023

Yau 1 ga watan Safar na shekaran 1445 H.

26/07/2023
10 Ga Watan Al-Muharram...Ranar Ashura.An Kar6o Daga Ibn Abbas R.A, Cewa Ma'aiki S.A.W Ya Zo Garin Madina, Sai Ya Sami Y...
24/07/2023

10 Ga Watan Al-Muharram...Ranar Ashura.
An Kar6o Daga Ibn Abbas R.A, Cewa Ma'aiki S.A.W Ya Zo Garin Madina, Sai Ya Sami Yahudawa Suna Azumin Ranar Ashura,Sai Ma'aiki S.A.W Yace Musu : Meyasa Kuke Azumtar Wannan Rana ? Sai S**a Ce : Ai Wannan Rana Ce Mai Girma, A Cikinta Allah Ya Tserar Da Annabi Musa Da Mutanan sa, Kuma Ya Lumar Da Fir'auna Da Mutanan sa, Sai Annabi Musa Yake Azumtar Ranar Dan Yin Godiya Ga Allah, Mu Ma Sai Muke Yi,Sai Ma'aiki S.A.W Yace : To Ai Mu Muka Fiku Cancanta Da Muyi Koyi Da Annabi Musa Fiye Da Ku, Sai Ma'aiki S.A.W Ya Azumci Wannan Rana, Kuma Yayi Umarni Da A Ringa Azumtarta.

Bukhari

09/07/2023

HAƘƘIN MAƘWABTAKA

Da yawa mukan manta da haƙƙin Maƙwabtaka, ka ga mutum gidansa hani,an amma maƙwabcinsa yana cikin halin ha'ula'i, kuma babu rawunsa bai damu ba ko kaɗan.

Bal wani ma murna yake yi maƙocinsa yana cikin tsanani, saboda dama babu jituwa tsakaninsu.

Manzon Allah s.a.w ya yi rantsuwa da Allah cewa duk wanda ya ci ya ƙoshi alhali maƙocinsa yana cikin tsananin yunwa ba tare da ya damu ya taimaka masa ba, to wannan mutumin ba mumini ba ne.

Kamar yadda Manzon Allah s.a.w ya ba mu labarin tsananta wasiyyar da Mala'ika Jibril ya yi masa a kan kula da haƙƙin maƙwabci, saboda yawan maimaita masa wasiyyar da ba ta muhimmanci har sai da Manzon Allah s.a.w ya yi tsammanin Jibril zai ce maƙwabci zai gaji dukiyar maƙwabcinsa idan ya mutu.

Mu kula da haƙƙin Maƙwabtaka ƴan uwa.

✍️ Sheikh Muhammad Auwal Nuhu Allemawy

25/06/2023
19/06/2023

Assalamu Alaikum

Yau Litini 19 ga watan June, 2023 shine yazo dai-dai da 1 ga watan Zhul Hijjah 1444H kamar yadda Sarkin Musulmin Nigeria Mai Martaba Alhaji Muhammad Sa'ad Abubakar, CFR, mni ya sanar a daren jiya. Bayan haka, ranar Laraba 28 ga watan June, 2023 ranar Eidul Adha 1444H.
Muna fatan Allah ya amsa ibadun mu.

18/06/2023

ASSALAMU ALAYKUM

Yau Lahadi, 29 Zhul-Qa'adah, 1444H wanda yayi dai-dai da 18 June, 2023. A yau za'a nemi jinjirin watan Zhul Hijjah 1444H. Allah yasa mu dace da dukkan alherin da yake cikin wannan watan.

اللهم تقبل الله منا جميعا صالح الأعمال

Abokanku na da tasiri a rayuwanku. Ku yi mu'amala da mutanen kirk masu nagarta.
02/06/2023

Abokanku na da tasiri a rayuwanku. Ku yi mu'amala da mutanen kirk masu nagarta.

Address

Zaria

Telephone

+2349067710614

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Ya Ku Ƴan Uwa posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share