04/10/2026
Da alamu Jam'iyyar APC ta haƙura da ƙuri'un Al'umar hayin dogo Samaru Zaria,
Qungiyar Samaru Youth Empowerment For Sustainable Development (SYEDS) na mika saƙon bangajiya ga mahalarta taron yayen ɗalibanta guda 100 wanda ya gudana yau 4/10/2026 ƙarkashin jagorancin iyayenmu: Prof Adamu Aliyu, Prof Sani Bichi.
Uban taro: former minister of agriculture Sheik Prof Abdullah Ahmad Cigarin Nufe, yanada keken ɗinkin da kuɗi
Mai girma Sarkin hayin dogo Alh Shehu Musa.
Wakilci jami'ar Ahmadu Bello Zaria: Prof Sahalu Junaid, yabada ₦50,000
Muhammad Adamu talba ₦100,000
Alh Mansur Aliyu ₦50,000
Abba tech ₦20,000
Da masu bada dubu goma harzuwa Naira ɗaya mungode Allah yasaka da Al khairi.
Da duk maharta masu kishin Al'ummar su kamar yadda zaku gansu a hotuna, Allah yasaka muku da Al khair da taimakon da kuka bada da shawarwari mungode kuma dafatan kowa ya koma gida lafiya.
Sukuma ƴan siyasa da da aka gayyata tun daga kan kansila, Shugaban ƙaramar hukuma Sabon gari, Ɗan majalisan jiha mai wakiltan mazaɓar Basawa, Ɗan Majalisar wakilai mai wakiltan karamar hukumar Sabon gari, Gwamnan jihar Kaduna Babu wanda yazo babu wanda ya turo wakili hakan na nuna ba'asan amfanin Matasan hayin dogo ba.
Al'umar dake da rumfar zaɓe sama da arba'in a gundumar bomo wanda tayi taron al'umma s**a halarta sama da mutun dubu daya Amma babu wakilcin shuwagabannin su na siyasa, Amma alhamdulillah mun samu wakilcin iyayenmu da matasan yankin masu daraja hakanma yanuna muna da gobe mai kyau kuma yaƙara mana kwarin gwiwa na cewa zamu'iya gyara al'umarmu da kanmu.
Don haka ƙuri'ar Al'umar Hayin Dogo Samaru Zaria gara ku hakura da'ita, indai baza'atallafa wannan al'umma mu mun san inda zamusa ƙuri'un mutun dubu ashirin ɗinmu masu katin zaɓe.