Majma'u Ahbab Sheikh Ibrahim Inyass Youths Forum

Majma'u Ahbab Sheikh Ibrahim Inyass Youths Forum This Page Was Created For The Unity And Development Of TIJJANIYYA Followers

ANNUAL NATIONAL MAULUD OF SHEIKH IBRAHIM INYASS R.T.A 2026.Katsina State @2026Signed,Media Team.Majma'u Ahbab Sheikh Ibr...
09/10/2025

ANNUAL NATIONAL MAULUD OF SHEIKH IBRAHIM INYASS R.T.A 2026.

Katsina State
@2026

Signed,
Media Team.
Majma'u Ahbab Sheikh Ibrahim Inyass Youths Forum.

22/09/2025

Big shout out to my newest top fans! Falalu Sani, Yakubu Tahir Chanchangi, Ibrahim Baba Kaunu Nguru, Muhammad Nazir Musa

اَلسَّــــــــــــــــلاَمُ عَلَيْكَ يَــــاشَيْخَنَــا وَ أُسْتَاذَنَـــا وَوَسِيلَتَنَــــــاإِلَى رَبِّنَـــــــــــا...
01/08/2025

اَلسَّــــــــــــــــلاَمُ عَلَيْكَ يَــــاشَيْخَنَــا وَ أُسْتَاذَنَـــا وَوَسِيلَتَنَــــــاإِلَى رَبِّنَـــــــــــا القطب المختـــــوم
والخــــــــاتم المحمدي يــــاسيدنـــاوملانــــــــــا
أحمـــــــــــدالتجـــــــاني رضي الله تعـــــاعنـــه
ورحمــــــــــــــــــــــةالله وبركاتـــــــــــــــــــــــه

Signed,
Media Team,
Majma'u Ahbab Sheikh Ibrahim Inyass Youths Forum.

S U FF A R - S H E H UWallahi tonda naki ban taɓa ganin wannan suffar ta Shehu ba sai yau Shehu mai abun mamaki ♥️ Allah...
08/05/2025

S U FF A R - S H E H U
Wallahi tonda naki ban taɓa ganin wannan suffar ta Shehu ba sai yau Shehu mai abun mamaki ♥️ Allah ya tabbatar da mu a cikin masoya shehu ibrahim ♥️🤲🤲
SUNANSA.
Ibrahim Abdullahi inyass

HAIHUWARSA .
ranar alhamis bayan sallar la,asar 1900

KASARSA .
yana garin daiba cikin kasar Senegal

YAYANSA ADUNIYA.
yaýansa guda 75 yabari aduniya cifa maza da mata

LITATTAFANSA.
litattafansa sunkai guda 75 aduniya wadanda yarubuta da hannunsa daga ciki akwai irinsu kashiful ilbas,diwani,ruhul adab,mukamad dini salasa,Tania,conakiriyya ,dadai sauransu

ALMAJIRANSA MANYA ,

1 Abubakar sirinbay
2 ummaru Faye
3 Usman kone
4 Aliyu side

TAPIYE TAPIYENSA.
yayi tapiye tapiye kasashe daban daban aduniya daga ciki akwai kasar Ghana inda ya musuluntar da arna 4000 a lokachi guda sannan China nanma ya musuluntar da kapirai wajen kimanin 4000 Suma sai Mali,murtaniya,egeip,bukina faso ,iran,Saudi Arabia,Italy,England,Spain,marocco,iraq,Togo,France,agentina,Lebanon,tunisia,cordevoure,India,conkry,honking,bankock,karashi,Malaysia,barzil,chadi,Niger,duwala, dadai sauransu

NIGERIA KUMA YAZO
Lagos ,Kano,katsina,jos,Zaria,okene,kaduna,dadai sauran lunguna

ALMAJIRANSA A NIGERIA.
malam atiku,malam tijjani,malam maihuka,malam yahuza Zaria,malam gibrima,khalipa sanusi, malam Ibrahim sale,malam dahiru bauchi,malam abdullahi dandume, shehu Abubakar Siddiq shehu balarabe zawuyya Gusau shehu balarabe Jega dadai sauransu

BABBAR BAIWAR DA ALLAH YAIMASHI
itace ya haddace Qur'an Yana Dan shekara 7 sannan Yana Dan shekara 20 ya rubuta littapinsa na farko aduniya wato ruhul adab

YA CIKA DUNIYA
da LA'ILAHA ILLA llah MUHAMMADU RASULULLAH da soyayyar annabi s.a.w

KIRANSA
shehu baitaba Kiran mutane da karpin tsiyaba wajen daukaka kalmar Allah aa da kyakkyawar mua'mala yakira mutane yayi koyi da halin abin kaunarsa annabi muhammadu s.a.w

RASUWARSA
yayai jinya a kasar England inda acanne Allah yaimashi rasuwa yanada shekara 75 aduniya ya rasu ranar asabar bayan ya kammala lsallar laasa 1975

ALLAH YABAMU ALBARKACHIN ANNABI MUHAMMADU S.A.W

Barhama NANAN BAI Mutuba

✔ Ciyar da Marayu abinci da Sutura yafi ka dinkawa Ka'aba riga✔ Kasa farin ciki a zuciyar Maraya yafi ka kwana kana Sall...
18/03/2025

✔ Ciyar da Marayu abinci da Sutura yafi ka dinkawa Ka'aba riga

✔ Kasa farin ciki a zuciyar Maraya yafi ka kwana kana Sallah

✔ Kuyi gaggawar aikata alheri karkuce sai kunyi kudi mai yawa

✔A Kyautata niyya idan za'ayi aikin alheri domin asamu yardar Allah.

✔ Ayi hankali da Riya, domin tana shiga cikin aikin mutum ta barauniyar hanya.

✔ Sadaqah tana janyo maka samun nasara tare da taimakon Ubangiji acikin dukkan abinda kasa agabanka.

✔ Sadaqah tana sanyawa ka samu gagarumar nasara akan Maqiyanka da mahassadanka. Kuma kaidinsu ba zai cuceka ba.

✔ Idan wani ciwo yana damunka har ka rasa maganinsa, to yawaita sadaqah. In sha Allah ita Sadaqah magani ce, waraka ce, kuma kariya ce daga dukkan cututtuka.

✔ Sadaqah ladanta yana tabbatuwa awajen Allah. Koda dabbobi kayi wa sadaqar, ko tsuntsaye, ko Kwari.

✔ Sadaqah garkuwa ce daga sharrin 'barayi, ko gobara, kuma tana kiyaye masu yinta daga mummunar cikawa.

✔ Babbar sadaqar da zaka fara gabatarwa ayanzu, ita ce kayi "sharing" (wato ya'da) wannan rubutun daga Zauren Fiqhu ba tare da goge koda harafi guda daga ciki ba.

Idan kayi haka da niyyar sadaqah, to duk wanda ya gani ya karanta kaima kana da lada akansa.

Signed by:-
Majma'u Ahbab Sheikh Ibrahim Inyass Youth Forum

AZUMI A WURIN SUFAYE******Allah ya tabbatar da cewa abubuwa guda biyu babu wanda yasan adadin ladan su, sai shi kadai, s...
16/03/2025

AZUMI A WURIN SUFAYE
*
**
***
Allah ya tabbatar da cewa abubuwa guda biyu babu wanda yasan adadin ladan su, sai shi kadai, sune HAQURI da AZUMI. Dalili kuwa, haquri da azumin duk suffar bayin sa ne waliyai, babu wanda kuwa yasan girman su a wajen sa, shiyasa ma in ka taba waliyyin sa, shi da kanshi zai yaqe ka.

A bisa koyarwar Shari'a, Azumi shine kamewa daga ci, sha, kusantar iyali, nisantar ayyukan sharri da kuma qarfafa ayyukan alheri a cikin ranakun wata na tara (ramadan) a watannin arabiya, tsawon kwana 29 zuwa 30.

Amma a wurin sufaye, azumi shine kamewa daga son zuciyar ka, zuwa abinda Allah yake so ta yadda yake so, babu wanin haka.

Wannan muqami ne na waliyai, wayanda ko da yaushe suke kokarin aikata abinda Allah zai ji dadi, da barin duk abinda zaisa Allah yayi fushi dasu. Ba kuma sai a cikin wata daya ba, A'a, kullum cikin haka suke.

Kalmar azumi a larabci shine صوم (Saum).
Harafin ص adadin sa shine 90, Harafin و adadin sa shine 6, adadin م adadin sa shine 40.
90 + 6 + 40 = 136.

136 din nan in ka juya shi zuwa haruffa, zai baka ولي (Waliy) wato waliyyi.

Ko babu yawan azkarai da nafiloli, in ka kame kanka daga biyewa son zuciyar ka, zaka shiga sahun waliyan Allah ma'abota girman daraja.

Dan haka yan'uwa, kamar yadda muke gasa da juna wurin tara abin duniya, ya kamata muyi fiye da haka wurin neman yardar Allah (wulaya).

Amma matakin samun yardar Allah na farko, shine rashin cutar da halittun sa, da kuma yawan yafiya garesu in s**a cuce ka, sai sanin sa sani na haqiqa, sannan kiyaye umurni ko hanin sa gwargwadon iko, Sai dai kash! Hakan ba zai yiwu gareka ba cikin sauki, sai in kayi riqo da Shehu Tijjani RTA.

Allah kasa mu fi qarfin zuciyar mu, ka bamu abin masarufi cikin wannan wata mai albarka, ka rufa mana asiri cikin ludufin ka, ka bamu ikon azumtar watan, idan munyi ka karɓa, domin darajar Shehu Ahmadu Tijjani

Signed By
Majma'u Ahbab Sheikh Ibrahim Inyass Youth Forum

MASU ZAGIN MAJAZUBAI******Akwai wani bawan Allah wanda yaje wurin Shehu Ibrahim Niasse RTA, lokacin da Shehu zai tafi as...
20/02/2025

MASU ZAGIN MAJAZUBAI
*
**
***
Akwai wani bawan Allah wanda yaje wurin Shehu Ibrahim Niasse RTA, lokacin da Shehu zai tafi asibiti a turai, sai shehu yace masa "ka jira ni zan je zan dawo", cikin ikon Allah shehu bai dawo ba, a can yayi wafati, amma wannan mutumin yace A'a bai yarda Shehu yayi wafati ba domin Shehu ya ce masa zai dawo, don haka shi yana nan zaune kofar dakin Shehu Ibrahim yana jiran sa, kuma yana wurin zaune tun 1975 fa, dani daku duk mun san wannan mutumin ko labarin sa, don haka ga tambaya:

1. A wani muhalli za ku sa wannan mutumin a risalatul muntaqeem da kuke karantawa yayin da kuka yi nufin cin mutuncin masoya, Jazba ce babu suluki ko suluki ne babu jazba?

2. Idan Shehu baya tare da shi, meyasa ya'ya da almajirai da Sahabban Shehu s**a barshi ya cigaba da zama a inda yake basu kore shi ba?

3. Idan shi ba majazubi bane wanda bai yi suluki ba, ko kuma ba saliki bane wanda bai yi jazba ba, wanene shi?

4. Idan kuka ce inda yake a zaune ba giya yake sha ko zina ba kamar yadda sauran masu da'awar jazba suke yi, toh a wani muhalli za ku sa ayyukan khidir a da'irar sufanci? Domin duk abinda yayi, a zahirin ilimi (Shari'a) saɓon Allah ne.

Wallahi Wallahi Wallahi, Sha'anin sufanci sai shehunnai, kar ka dauka jin larabci ko ijazar da kaje ka siya zai baka damar fahimtar halittun Allah, gwargwadon karewar ka a Allah, gwargwadon fahimtar halittun sa. Akwai majazuban ƙarya kam tabbas, amma babu mai iya gane su sai wanda ya ƙaryata kansa bayan ya gaskata kansa.

Matasa kuje kuyi tarbiya, kar ku mutu cikin mutuwa, mutuwa cikin rayuwa shine riba.

Signed by
Majma'u Ahbab Sheikh Ibrahim Inyass Youth Forum

RANA MAI KAMAR TA YAU LARABA- WANDA YAI DAIDAI DA 👉19/02/1975Maulana Sheikh Muhammadu Ngibirima Zulma Arif (RTA) Ya cika...
19/02/2025

RANA MAI KAMAR TA YAU LARABA- WANDA YAI DAIDAI DA 👉19/02/1975

Maulana Sheikh Muhammadu Ngibirima Zulma Arif (RTA) Ya cika Shekaru 50 Da Komawa Rahmar Ubangiji(S.w.t)

Allah Ya Jaddadamasu Rahama Manyan Bayin Allah.
Signed by
Majma'u Ahbab Sheikh Ibrahim Inyass Youth Forum Association Of Nigeria

Amadadin Daukachin Members Din Majma'u Ahbab Sheikh Ibrahim Inyass Youth Forum Association Of Nigeria.Muna Mika Sakon Ga...
14/02/2025

Amadadin Daukachin Members Din Majma'u Ahbab Sheikh Ibrahim Inyass Youth Forum Association Of Nigeria.

Muna Mika Sakon Gayyatarmu Ga Daukachin Masoyah Shehul Islam Alh.Ibrahim Niasse(R.t.a)

Zuwa Taron Maulud Gidan SAYYIDA AISHAT NIASSE (R.T.A). Mahaifiyan NATIONAL CHAIRMAN

MAJMA'U AHBAB SHEIKH IBRAHIM INYASS ASSOCIATION OF NIGERIA.

Signed By:-

Majma'u Ahbab Sheikh Ibrahim Inyass Youth Forum Association Of Nigeria

06/02/2025

Jawabin Shugaban MAJMAU AHBAB SHEIKH IBRAHIM NIASSE ASSOCIATION OF NIGERIA.

Jikan Shehu Ibrahim Niasse (R.t.a) Nafarko Akasarmu Nigeria.

Signed:-
Majma'u Ahbab Sheikh Ibrahim Inyass Youth Forum

Muna Mika Sakaon Ta'aziyanmu Ga Daukachin Al'ummah Musulmi Masoyah Shehul Islam Alh.Sheikh Ibrahim Bin Haji Abdullahi Ni...
04/02/2025

Muna Mika Sakaon Ta'aziyanmu Ga Daukachin Al'ummah Musulmi Masoyah Shehul Islam

Alh.Sheikh Ibrahim Bin Haji Abdullahi Niasse(R.t.a) Narashin Dan Uwanmu Mal.Abdullah Naibin (Masallachin Unguwar Abuja Takum LGA) Taraba State Adalilin Hadarin Mashin.

Allah Ya Jaddadamasa Rahama.

Signed By

Majma'u Ahbab Sheikh Ibrahim Inyass Youth Forum

Address

No 1 Kusfa By Gambo Sawaba Zaria
Zaria

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Majma'u Ahbab Sheikh Ibrahim Inyass Youths Forum posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Place Of Worship

Send a message to Majma'u Ahbab Sheikh Ibrahim Inyass Youths Forum:

Share