15/04/2026
MACE TANA TASIRI AKAN MIJINTA, LALACEWAR SA KO SHIRYUWAR SA
Alhassanul Basriy Allah ya masa rahama yana cewa "Nazo wurin wani mai sayarda tufafi a Makkah inaso zan saya tufafi awurinsa sai na taradda shi yana yaba kayansa yana kuma rantsuwa, sai na wuce na barshi naqi saya awurinsa, Nace baya dacewa in saya awurin wannan gara in saya awurin waninsa.
π Bayan shekara biyu sai naje aikin hajji, sai na sake zuwa wurinsa zan saya tufafi awannan karon sai na tarar dashi baya yabon kayansa baya kuma rantsuwa, sai nace masa; shin ba kaine wancan mutumin da nazo wurinsa ba shekarun baya?? So yace; eh nine. Sai nace masa; Ya akayi yanzu na ganka baka yabon kayanka baka kuma rantsuwa??
Sai yace min "Na kasance inada mata, idan nazo mata da kudi dan kadan banyi ciniki sosai ba, sai ta raina shi, idan nazo mata da mai yawan ma shima sai ta karantashi, kwatsam sai Allah ya kasheta.
Sai na auri wata mata bayanta, ita kuma aduk lokacin da zan fito da safe zuwa kasuwa sai ta k**a rigana tacemin; ya kai wane, kaji tsoron Allah kada ka ciyar damu sai da halal, idan ka zo mana da kadan zamu mai dashi mai yawa, idan baka dawo da komai ba zan tayaka hada wasu tufafin (har mu samu mu sayar).
Ψ§ΩΩ
Ψ¬Ψ§ΩΨ³Ψ© ΩΨ¬ΩΨ§ΩΨ± Ψ§ΩΨΉΩΩ
ΩΩΨ―ΩΩΩΨ±Ω Ω₯/Ω’Ω₯Ω‘