Sayyida Aisha Ahmad Abulfathi

  • Home
  • Sayyida Aisha Ahmad Abulfathi

Sayyida Aisha Ahmad Abulfathi Official Page | Sayyidah Aisha Ahmad Abulfathi…

* 🎙️Brief Lecture ✅
📖Sheikh Ahmad Abulfathi Alyerwawy (RTA)

Available… ✅
(5)

Sheikh Ahmad Abulfathi ya yi alaqa da dukkan Shehunan Ɗariqar Tijjaniyya na Nigeria da wajen Nigeria sun sheda shi mutum...
31/08/2026

Sheikh Ahmad Abulfathi ya yi alaqa da dukkan Shehunan Ɗariqar Tijjaniyya na Nigeria da wajen Nigeria sun sheda shi mutumin Allah ne mai tawadu'u da gudun Duniya.

**WANENE KHALIFA********A zawiya, Khalifa ba kawai magaji bane - shine wanda zai rike amanar Shehu, da Zawiya, da Murida...
31/08/2026

**WANENE KHALIFA**
*
**
***

A zawiya, Khalifa ba kawai magaji bane - shine wanda zai rike amanar Shehu, da Zawiya, da Muridai bayan wafati.

Saboda haka malamai na Darikar Tijjaniyya sun ce, wanda za'a zaba Khalifa dole ne ya kasance da wadannan siffofi:

ABUBUWAN DA AKE BUQATA GA KOWANNE KHALIFA
1. ilimi ingantacce
2. Tsoron Allah da Aiki da Ilimi
3. Halayen kirki da Hakuri
4. Yarda da Jama'a da Shura
5. Jajircewa wajen hidimar Zawiya

1. Ilimi ingantacce
Ya zama masanin addini, musamman:
• Ilimin Tauhidi, Fiqhu da Tasawwuf • Sanin sharuddan Wird, Lazimi, Wazifa da zikirin Juma'a na Tijjaniyya • Sanin tarihin Shehu Ahmad Tijjani (RA) da khalifofinsa
Jahili ba zai iya jagorantar Zawiya ba, zai bata Muridai.

2. Tsoron Allah da Aiki da Ilimi
• Mai gaskiya, amana, da tawadu'u • Baya bin son zuciya, baya neman duniya da suna • Abin koyi ne a ibada - sallah a kan lokaci, azkar, da kiyamul lail

SHEHU IBRAHIM (RTA A) yace: "Khalifa ba wanda yafi kowa shekaru bane, wanda yafi kowa tsoron Allah ne."

3. Halayen kirki da Hakuri
• Mai hakuri da Muridai - manya da kanana • Mai afuwa, mai yafewa, baya rama zargi • Mai adalci, baya nuna bambanci tsakanin masu kudi da talakawa • Mai iya hada kan jama'a, ba mai rarraba kawuna ba

4. Yarda da Jama'a da Shura
A Tijjaniyya, Khalifa ba'a dorashi da karfi. Dole ne: 👇👇
• Ya kasance wanda Shehu ya yi wasici da shi kafin wafati, ko kuma • Manyan Muqaddamai da dattawan Zawiya sun zauna sun yi shura sun yarda da shi • Mafi yawan Muridai suna kaunar sa kuma suna da kwarin gwiwa a gare shi

5. Jajircewa wajen hidimar Zawiya
• Zai iya tsayawa ya kula da Zawiya - bude ta a kan lokaci, karantarwa, tarbiyya • Baya barin Zawiya ta zama kasuwanci ko gidan siyasa • Yana da himmar yada addini, ba tara dukiya ba

A takaice, Khalifan da ya cancanta shine wanda idan ka gan shi ka tuna da Shehu - a iliminsa, a dabi'unsa, da kuma a yadda yake tausaya wa mutane.

Ba wai dan Shehu bane, ba wai mai kudi bane, ba wai wanda yafi kowa shekaru a Zawiya ba - sai wanda Allah ya zaba da tsoronSa da ilimi.

Allah ya bamu albarkacin Shehunnan mu, ya sanya mu cikin masu rike amanar su da gaskiya.

30/08/2026

Jan Hankali Ga Almajirai da Masoya..‼️‼️

Sayyida Aisha Ahmad Abulfathi

30/08/2026

DAN TSOKACI.‼️‼️

Akan bayanin da Khalifah ya yi a filin Maulidi game da Tijjaniyya, tare da jan hankalin almajirai da masoya Shehu Abulfathi (RTA).

Daga: Maulana Sayyidi Hashim Abulfathi (RTA)

Sayyida Aisha Ahmad Abulfathi

Mu ’Yan Tijjaniyya ne, Sannan Mu Mabiyan Shehu Tijjani Ne, Mabiyan Shehu Ibrahim. Amma Ko da ’dan Shehu Ne Ya Bar Hanya,...
30/08/2026

Mu ’Yan Tijjaniyya ne, Sannan Mu Mabiyan Shehu Tijjani Ne, Mabiyan Shehu Ibrahim. Amma Ko da ’dan Shehu Ne Ya Bar Hanya, Mu Ba Ma Tare Da Shi.

KHALIFAH Dr ALIYU ABULFATHI

Sayyida Aisha Ahmad Abulfathi

**FAƊAR GASKIYA********ɗaya daga cikin halayyar Shehu abulfathi RTA shine faɗar gaskiya ko'ina kuma mai menene zai biyo ...
30/08/2026

**FAƊAR GASKIYA**
*
**
***
ɗaya daga cikin halayyar Shehu abulfathi RTA shine faɗar gaskiya ko'ina kuma mai menene zai biyo bayanta domin ita gaskiya Gaskiya ce,

ko kai waye indai kayi kuskure to ba shakka Shehu abulfathi RTA zai faɗa mana kuskurenka,

haka kuma Khalifofinsa suke 👇👇

1- Khalifa Alhaji Aliyu abulfathi RTA (Baba Ali) duk lokacin da aka samu Matsala tsakanin muridai ko yarane ko manyane Baba Ali RTA zai faɗa gaskiya mai mai laifi sai dai duk abinda zai faru ya faru, 2003 sun samu matsala da gwamnatin jahar Borno state ya faɗa mata Gaskiya,

2- Shehu muhammadul Arabi abulfathi RTA (Baba Arabi) shima haka idan gidan dake Madina kullum sai kasamu Mutane yana yi musu sulhu kuma ba shine bulama a Madina ba, kawai tsantsar Gaskiyarsace tasa mutane yadda hukuncinsa ko daɗi ko akasinta sbd sun tabbatar bazai yi musu hukunci da son zuciya ba, 🙏

3- professor sheikh Murtadha abulfathi RTA (baye Murtadha) daman shi duk wanda yasan shi ko wajen zama bai yadda ya haɗa mara gaskiya ba, kuma Shehu abulfathi RTA shine yayi mai shaidar haka yace "DUK ABINDA KUKA BA MURTADHA ACIKI TA TABBATA BABU GASKIYA KUMA NIMA BANA CIKIN MARASA GASKIYA"

kuma ya'yan Shehi abulfathi RTA suke maza da matansu Gaskiya itace alkiblarsu basa hada hanya da ƙarya sbd sunsan illarta,

Allah dan sirrin da ka ɓoye tsakanin Manzon Allah S A W da Shehu abulfathi RTA kabamu damar faɗar gaskiya duk ɗacinta

Sayyida Aisha Ahmad Abulfathi

Ni Ba Halifah Kowa Bane Halifah Mahaifina Ne Kuma Banna Bukatar Abinda Yawuce Haka..KHALIFAH Dr ALIYU ABULFATHI..Sayyida...
30/08/2026

Ni Ba Halifah Kowa Bane Halifah Mahaifina Ne Kuma Banna Bukatar Abinda Yawuce Haka..

KHALIFAH Dr ALIYU ABULFATHI..

Sayyida Aisha Ahmad Abulfathi

📢 SANARWA! SANARWA!! SANARWA!!!Insha Allah, gobe Litinin za a gudanar da Sunan Maulidi a Madinatu Sheikh Ahmad Abulfathi...
30/08/2026

📢 SANARWA! SANARWA!! SANARWA!!!

Insha Allah, gobe Litinin za a gudanar da Sunan Maulidi a Madinatu Sheikh Ahmad Abulfathi (RTA), ƙarƙashin jagorancin Khalifa Aliyu Sheikh Ahmad Abulfathi (RTA).

🕙 Za a zauna daga ƙarfe 10:00 na dare har zuwa wayewar gari.

Allah Ya ƙara wa Annabi ﷺ daraja da ɗaukaka.

Amin Ya Rabbal Alamin.

Sayyida Aisha Ahmad Abulfathi

Ma’aboci Tausayi da Karamci…🤍🤍
30/08/2026

Ma’aboci Tausayi da Karamci…🤍🤍

Address

Madinatu Sheirk Ahmad Aliyu Abulfathi

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Sayyida Aisha Ahmad Abulfathi posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Place Of Worship

Send a message to Sayyida Aisha Ahmad Abulfathi:

Shortcuts

  • Want your place of worship to be the top-listed Place Of Worship?

Share