25/05/2026
🌙✨ FALALAR GOMAN FARKON ZUL-HIJJAH ✨🌙
🕋 Goman farko na watan Zul-Hijjah su ne mafi alherin kwanaki a duniya, kwanaki ne na rahama, gafara da yawaitar lada.
Daga cikin falalolinsu akwai:
1️⃣ Allah Ya fifita waɗannan kwanaki akan sauran kwanaki.
2️⃣ Ayyukan alheri a cikinsu sun fi soyuwa wajen Allah. 🤍
3️⃣ Yawaita zikiri kamar:
Subhanallah
Alhamdulillah
Allahu Akbar
La ilaha illallah
4️⃣ Azumin ranar Arfa yana kankare zunuban shekara biyu.
5️⃣ Addu’a a cikin waɗannan kwanaki tana da girman karɓuwa. 🤲
6️⃣ Karatun Alƙur’ani yana ƙara haske da nutsuwa ga zuciya. 📖✨
7️⃣ Sadaka tana jawo albarka da rahamar Allah.
8️⃣ Tuba da istigfari suna kawo gafara da tsarkake zuciya.
9️⃣ Layya tana daga cikin manyan sunnonin wannan wata mai albarka.
🔟 Ranar Arfa rana ce ta ‘yanta bayin Allah daga wuta. 🕋🤍
🤲 Allah Ya sa mu dace da ibada, Ya karɓi ayyukanmu, Ya gafarta mana baki ɗaya.
Ameen