08/10/2026
🌙 ALHAMDULILLAH — MURNAR KAMMALA TAFSIRUL QUR’ANI BIL QUR’AN 🌙
Talata, 7 ga watan 10, 2026
Alhamdulillahi Rabbil ‘Alamin!
Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah Subhanahu wa Ta’ala, Ubangijin talikai, wanda Ya ba bayinsa dama, ƙarfi da ikon gudanar da ayyukan alheri.
A yau muna cike da farin ciki da godiya bisa wannan babban ni’ima da Allah Ya kawo mana, inda Peace Ambassador Kadimul Qur’an, Sheikh Yahya Ibrahim Masuss**a , ya samu ikon kammala babban tafsirinsa na Hausa mai taken Tafsirul Qur’ani Bil Qur’an.
Wannan ba ƙaramin tarihi ba ne. Tafsirin Al-Qur’ani aiki ne mai girma wanda yake buƙatar ilimi, haƙuri, jajircewa, tsayin daka da tsoron Allah. Allah ne kaɗai Ya ba shi wannan iko har ya kai ga ƙarshe.
A wannan tafiya an samu ƙalubale, maganganu da s**a, har ma da abubuwan da za su iya karya zuciyar mutum. Amma abin da ya fi komai muhimmanci shi ne cewa Allah Ya ba shi ikon jurewa, ya ci gaba da tafiya, har Allah Ya kai shi ga wannan rana ta kammalawa.
Wannan shi ne darasin da muke koya:
Mai neman gaskiya kada ya bari ƙalubale su hana shi aikata abin da ya yi imani da shi na alheri.
Muna roƙon Allah Subhanahu wa Ta’ala Ya karɓi wannan aiki a matsayin ibada, Ya sanya shi cikin ma’aunin kyawawan ayyuka, Ya amfanar da al’umma da shi, Ya ƙara wa Malam ilimi, hikima, lafiya da tsawon rai cikin biyayya.
Allah Ya saka masa da mafificin alheri bisa wannan gagarumin aiki na Al-Qur’ani.
Muna kuma gode wa dukkan waɗanda s**a kasance tare da wannan tafiya—masu ƙarfafawa, masu addu’a da duk waɗanda s**a taimaka ta kowace hanya.
ALHAMDULILLAH ALA NI’MATIL-QUR’AN 🤲🏽📖
Tafsirul Qur’ani Bil Qur’an — an kammala.
Allah Ya karɓa, Ya albarkace shi, Ya sanya shi haske ga zukata da hujja ga masu karatu. Amin Ya Rabbal ‘Alamin.
Da'awatul Qur'anil Kareem