Assawab Foundation

Directions Website

Assawab Foundation Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Assawab Foundation, Religious Center, Sokoto.

Assawab Foundation cibiya ce domin taimakon al'umma, koyarda addinin musulunci, bincike, fadakarwa, tarbiyantarwa da yada karatukan malaman sunnah a yanar gizo da kafafen sadarwa.
𝐌𝐚𝐧𝐮𝐟𝐚𝐫 𝐦𝐮

RANAR MASOYA TSAKANI YAUDARA DA GASKIYATARIHI DA ASALIN RANAR MASOYA //01   Ranar masoya  (Valentine’s Day ko Saint Vale...
11/02/2024

RANAR MASOYA TSAKANI YAUDARA DA GASKIYA

TARIHI DA ASALIN RANAR MASOYA //01

Ranar masoya (Valentine’s Day ko Saint Valentine’s ko feast Saint Valentine) kamar yanda suke kira a turance, rana ce da ake yin bikin ta duk shekara 14 ga Fabriru (February). Ta samo asali ne daga bikin kiristoci don karrama mamacin su da suke gani a matsayin shahidi a addinin su, mai suna Saint Valentine daga baya sai abin ya koma bikin al’ada, haka zalika bikin ya kasance cikin wasu mahimmanci al’adu da addini, da ake murna akan nuna soyayya da kauna a bangaroran duniya da dama.

Tarihin kiristoci na Cocin Katolika (Catholic Church) ya nuna cewa akwai mutane uku ko ma fiye da mutum daya, da aka radawa suna da Saint Valentine. Sai dai Valentine dinda ake karramawa a 14th February sune Valentine din Romawa wato (Valentinus presb M. Romae) da Valentine din Terni wato (Valentinus ep. Interamnensis m. Romae) kuma dukkanin su an kashe su ne. Kazalika tarihi ya nuna cewa Valentine na daya daga cikin wadanda suke hidimtawa coci a karni na 3 a yankin Romawa.

Dalilin da yasa aka kashe wadannan Valentine shi ne, lokacin da Sarkin sarakuna na wannan lokacin wato Claudius II ya yanke shawarar cewa maza marasa aure sun fi waɗanda suke da mata da iyalai himma aharkar soja, sai ya haramta aure ga samarin sojoji. Da Saint Valentine ya fahimci rashin adalci ga dokar, sai ya bijirewa Sarki Claudius, ya ci gaba da aurar da matasa masoya a asirce, da aka gano abinda Valentine ke aikatawa, sai Sarki Claudius ya ba da umarnin a kashe shi. Akwai ma su ganin cewa, Valentine Terni Bishof ne wanda daga sunan shi ne aka samo bikin wannan ranar, shima Sarki Claudius 2 ya sa an fille kansa.

A nan za mu dakata, za mu ci gaba a rubutu na gaba.

Allah ya ba mu ikon fahimta da fa'idantuwa. Amin

Bashir Umar Rk

11/01/2024

Saƙonni daga Alqur'ani //06

Allah madaukakin Sarki yana cewa:

وَسَارِعُوٓا۟ إِلَىٰ مَغْفِرَةٍ مِّن رَّبِّكُمْ وَجَنَّةٍ عَرْضُهَا ٱلسَّمَٰوَٰتُ وَٱلْأَرْضُ أُعِدَّتْ لِلْمُتَّقِينَ

"ku yi gaugawa zuwa ga neman gafara daga Ubangijinku da wata Aljanna wadda faɗinta (dai dai da) sammai da ƙasa ne, an yi tattalinta domin masu taƙawa" [Ali-Imran: 133]

Mu yi gaugawa zuwa tuba, saboda mutuwa bata jira!

Gobe zan tuba, gobe zan fara zuwa majalisin Qur'ani, gobe zan je wajen tafsiri ko wani karatun addini... Goben zata zo, ba zamu yi ko dai daga cikin abubuwan da mukayi niyyar yi ba.

Amma dan gane da dogon buri, dukka nimmu muna kudurta cewa mutuwa nesa take!

Mu yi gaugawa zuwa tuba; domin jinkiri na ɗan lokaci na iya haramta maka Aljanna.

Allah yasa mu dace.

Gabatarwa: 𝙱𝚊𝚜𝚑𝚒𝚛 𝚄𝚖𝚊𝚛 𝚁𝚔 (Abu Nafees Rk )

Assᴀᴡᴀʙ ғᴏᴜɴᴅᴀᴛɪᴏɴ 𝑡𝑎𝑘𝑢 𝑐𝑒 𝑑𝑜𝑚𝑖𝑛 𝑓𝑎𝑑𝑎𝑘𝑎𝑟𝑤𝑎 𝑑𝑎 𝑡𝑎𝑟𝑏𝑖𝑦𝑎𝑛𝑡𝑎𝑟𝑤𝑎.

09/01/2024

Saƙonni daga Alqur'ani //05

Akwai abin lura cikin ƙissar Annabi Zakariyya, lokacin da ya kira Ubangijinsa a boye, ya ce Ya Ubangiji!

Ƙassa na sunyi rauni,
Kaina ya fitar da furfura,
Matata ta kasance bakararriya. [Maryam: 2 - 5]

Yasan da cewa sabubba suna canja kaddarar mutane, amma basu canja hukuncin Allah.

Sai ya daga hannayensa ya yi addu'a:

"فَهَبْ لِى مِن لَّدُنكَ وَلِيًّا"

"...Ka ba ni wani mataimaki daga wajenKa" [Maryam: 5]

Sai ga ijaba ta zo masa:

يَٰزَكَرِيَّآ إِنَّا نُبَشِّرُكَ بِغُلَٰمٍ ٱسْمُهُ ۥ يَحْيَىٰ لَمْ نَجْعَل لَّهُ ۥ مِن قَبْلُ سَمِيًّا

[Allah Ya karɓa] "Ya zakariyya! Lalle ne Mu, Muna yi maka bushara da wani yaro, sunansa Yahaya. Ba Mu sanya masa wani takwara ba a gabani" [Maryam: 7].

NB: Darasi a nan, duk wanda ya rataya ko jingina zuciyarsa da al'amarinsa zuwa ga sabubba kawai, to Allah zai bar shi ga iya sabubban!

Haka zalika, duk wanda ya rataya ko jingina zuciyarsa zuwa ga Allah, to haƙiƙa Allah yayi masa tanadin sabubban da zai yi riƙo da su.

Gabatarwa: 𝙱𝚊𝚜𝚑𝚒𝚛 𝚄𝚖𝚊𝚛 𝚁𝚔 ( Abu Nafees Rk )

Assᴀᴡᴀʙ ғᴏᴜɴᴅᴀᴛɪᴏɴ 𝑡𝑎𝑘𝑢 𝑐𝑒 𝑑𝑜𝑚𝑖𝑛 𝑓𝑎𝑑𝑎𝑘𝑎𝑟𝑤𝑎 𝑑𝑎 𝑡𝑎𝑟𝑏𝑖𝑦𝑎𝑛𝑡𝑎𝑟𝑤𝑎.

08/01/2024

Saƙonni daga Alqur'ani //04

Mutuwa ita ce tekun da kowa zai sha daga gare sa, kuma rigar da kowa zai saka, mumini da fajiri, Annabi da shugaba mai karfin iko, aljani da mala'ika, babu wanda zai dauwama sai Allah kawai!

كُلُّ نَفْسٍ ذَآئِقَةُ ٱلْمَوْتِ ۗ وَنَبْلُوكُم بِٱلشَّرِّ وَٱلْخَيْرِ فِتْنَةً ۖ وَإِلَيْنَا تُرْجَعُونَ

"Kowane rai mai ɗanɗanar mutuwa ne. Kuma Muna jarraba ku da sharri da alheri domin fitina. Kuma zuwa gare Mu ake mayar da ku"

Mutuwa ba ita ce karshen labari ba, akasin haka; ita farkon labarin ne kawai!

Mutuwa kawai ta isa wa'azi a gare mu👌

Allah yasa mu yi karshe mai kyau.

𝙱𝚊𝚜𝚑𝚒𝚛 𝚄𝚖𝚊𝚛 𝚁𝚔 (𝑨𝒃𝒖 𝑵𝒂𝒇𝒆𝒆𝒔)

Assᴀᴡᴀʙ ғᴏᴜɴᴅᴀᴛɪᴏɴ 𝑡𝑎𝑘𝑢 𝑐𝑒 𝑑𝑜𝑚𝑖𝑛 𝑓𝑎𝑑𝑎𝑘𝑎𝑟𝑤𝑎 𝑑𝑎 𝑡𝑎𝑟𝑏𝑖𝑦𝑎𝑛𝑡𝑎𝑟𝑤𝑎.

07/01/2024

Saƙonni daga Alqur'ani //03

Wannan duniyar; gidan noma ne ba gidan girbi ba, kuma gidan Jarabawa ce ba gidan sakamako ba.

Yana daga cikin jarabawar ubangiji mai tsarki ga bayinsa; ya saukar masu da musibu: Rasa masoya musiba ce, hasarar dukiya musiba ce, haka kuma; mugun makwabci, fajirar mata, da shugaba azzalumi; dukkanin su musiba ce!

Wanda yayi hakuri, haƙiƙa ya ci Jarabawa! Wanda yayi fushi, haƙiƙa ya faɗi Jarabawa!

Kuma mutane ba za su tsira daga musiba ba, hatta annabawa, sun kasance sune s**a fi kowa jarabtuwa da wahala.

Kai dai yi riƙo da fadar Allah madaukakin Sarki da yake cewa:

وَٱسْتَعِينُوا۟ بِٱلصَّبْرِ وَٱلصَّلَوٰةِ ۚ وَإِنَّهَا لَكَبِيرَةٌ إِلَّا عَلَى ٱلْخَٰشِعِينَ

"Kuma ku nemi taimako da yin haƙuri, da sallah. Kuma lalle ne ita (salla), haƙiƙa, mai girma ce face fa a kan masu tsoron Allah" [Baƙara: 45].

Gabatarwa: 𝙱𝚊𝚜𝚑𝚒𝚛 𝚄𝚖𝚊𝚛 𝚁𝚔 (𝑨𝒃𝒖 𝑵𝒂𝒇𝒆𝒆𝒔)

https://chat.whatsapp.com/GrfclkCGobzGJAZOrMrLcL

Assᴀᴡᴀʙ ғᴏᴜɴᴅᴀᴛɪᴏɴ 𝑡𝑎𝑘𝑢 𝑐𝑒 𝑑𝑜𝑚𝑖𝑛 𝑓𝑎𝑑𝑎𝑘𝑎𝑟𝑤𝑎 𝑑𝑎 𝑡𝑎𝑟𝑏𝑖𝑦𝑎𝑛𝑡𝑎𝑟𝑤𝑎

06/01/2024

Saƙonni daga Alqur'ani mai girma //02

Idan mutane sun jahilci daukakar ka, ko sanin kai waye; kada kaji bacin rai! Ya isheka cewa Allah yasan kowa kuma yasan ko kai waye!

Baka ji fadar Allah madaukaki ba, da yake cewa: "...وَرُسُلًا لَّمْ نَقْصُصْهُمْ عَلَيْكَ..."

"...Da wasu manzanni waɗanda ba Mu ba da labarinsu ba a gare ka... " [Nisa'i: 164]

Manzanni da yawa ba a sansu ba kuma babu labarin su.

Dan uwa! baya cutar da kai dan ba a sanka ba, Allah yasan ko kai waye. 👌👌

05/01/2024

Saƙonni daga Alqur'ani//01

Duk lokacin da kayi zunubi, ka fada a cikin ranka: na faɗi gwagwarmaya ce kawai; amma ban faɗi yaƙi ba!

Kada ka samu zullumi ko damuwa, sake gyara kanka ta hanyar yin arwala tare da yin raka'a biyu.

Allah yana cewa:

"...إِنَّ ٱلْحَسَنَٰتِ يُذْهِبْنَ ٱلسَّيِّـَٔاتِ..."

"Lalle ne ayyukan ƙwarai suna kore mũnãnan ayyuka..." [Hud: 114]

Bayan haka, nemi gafara ga yatsun da ka aikata zunubi da su, karanta Alƙur'ni ga idanun da ka kalli haramun da su... Yi kuka; domin kukan masu tuba a wajen Allah kamar ganawar masu da'a ce ga Allah.
Ka sani cewa; Allah bai kira kansa algafuru ba sai dan yana son ka yi imani ka canja zuwa na kirki.

Allah ya gafarta muna zunuban mu ya yafe muna kurakuran mu. Amin

𝙱𝚊𝚜𝚑𝚒𝚛 𝚄𝚖𝚊𝚛 𝚁𝚔 (𝑨𝒃𝒖 𝑵𝒂𝒇𝒆𝒆𝒔)

https://chat.whatsapp.com/GrfclkCGobzGJAZOrMrLcL

Assᴀᴡᴀʙ ғᴏᴜɴᴅᴀᴛɪᴏɴ 𝑡𝑎𝑘𝑢 𝑐𝑒 𝑑𝑜𝑚𝑖𝑛 𝑓𝑎𝑑𝑎𝑘𝑎𝑟𝑤𝑎 𝑑𝑎 𝑡𝑎𝑟𝑏𝑖𝑦𝑎𝑛𝑡𝑎𝑟𝑤𝑎.

Lalacewar zuciya shi ne mutuwartaIta Zuciya tana najastuwa da rashin lafiya ne da sha'awowin haramun, yawan aikata zunub...
02/01/2024

Lalacewar zuciya shi ne mutuwarta

Ita Zuciya tana najastuwa da rashin lafiya ne da sha'awowin haramun, yawan aikata zunubai kuwa shi ne ke kashe zukatan dayawa daga cikin mutane.

Haka kuma zuciya na tsaftatuwa da tsarkakuwa ne ta hanyar gujewa da nisantar sha'awowin haramun da zunubai da tuba zuwa ga Allah.

Shi kuwa gyara, da raya zuciya sai da kiyaye abubuwa kamar: Karanta Alqur'ni da tadabburi sa, tsayarda sallar dare, zama da mutanen kirki, jajircewa da addu'a kafin ketowar alfijir, takaita cin abinci, cin halal da gujewa haram a koda yaushe; da sauran su.

Manzon Allah ya ce: "...cikin jikin dan Adam akwai wata tsoka, idan ta gyaru dukkan jiki ya gyaru, idan ta lalace dukkan jiki ya lalace"

Ita zuciyar dan Adam tanada wuyar sha'ani, kuma tanada saurin juyawa da canjawa fiye da tunkya yayinda takai makura wajen tafarfasa; shi yasa manzon Allah yake yawan addu'a yana cewa:

اللهم يَا مُقَلِّبَ الْقُلُوبِ ثَبِّتْ قَلْبِي عَلَى دِينِكَ.

اللَّهُمَّ مُصَرِّفَ الْقُلُوبِ صَرِّفْ قُلُوبَنَا عَلَى طَاعَتِكَ.

Yana rokon Allah ya tabbatar da zuciyar shi, ya kare shi daga juyawarta ko canjawarta.

Allah ya warkarda zukatanmu daga duk wasu cututtukan zuciya!

رَبَّنَا لَا تُزِغْ قُلُوبَنَا بَعْدَ إِذْ هَدَيْتَنَا وَهَبْ لَنَا مِنْ لَدُنْكَ رَحْمَةً إِنَّكَ أَنْتَ الْوَهَّابُ!

Ameen thumma Ameen

𝙱𝚊𝚜𝚑𝚒𝚛 𝚄𝚖𝚊𝚛 𝚁𝚔 (𝑨𝒃𝒖 𝑵𝒂𝒇𝒆𝒆𝒔)

https://chat.whatsapp.com/GrfclkCGobzGJAZOrMrLcL

Assᴀᴡᴀʙ ғᴏᴜɴᴅᴀᴛɪᴏɴ 𝑡𝑎𝑘𝑢 𝑐𝑒 𝑑𝑜𝑚𝑖𝑛 𝑓𝑎𝑑𝑎𝑘𝑎𝑟𝑤𝑎 𝑑𝑎 𝑡𝑎𝑟𝑏𝑖𝑦𝑎𝑛𝑡𝑎𝑟𝑤𝑎.

WhatsApp Group Invite

01/01/2024

Assawab Foundation cibiya ce domin taimakon al'umma, koyarda addinin musulunci, bincike, fadakarwa, tarbiyantarwa da yada karatukan malaman sunnah a yanar gizo da kafafen sadarwa.

𝐌𝐚𝐧𝐮𝐟𝐚𝐫 𝐦𝐮:
1. Taimakon Makaratun zaure da na Islamiyoyi.
2. Karantar da litatattafan ilimi daga tushe.
3. Samar da rubuce-rubucen makaloli akan maudu'ai a mahangar musulunci domin:
A. Tarbiyantarwa
B. Fadakarwa
4. Yada karatukan malaman sunnah.

𝗪𝗲𝗯𝘀𝗶𝘁𝗲: www.assawab.org.ng

Har yanzu mu dalibai ne ba malamai ba!

Address

Sokoto
840212

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Assawab Foundation posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

Share