21/10/2023
Wannan shine abinda zai faru idan DAJJAL ya bayyana a Duniya! 👇
Idan Dajjal ya fito dubunnan YAHUDAWA za su bi shi, su yi tururuwa a kansa, da nufin yaƙar Musulmi.
Daga nan sai Annabi Isa (a.s) ya sauko, a dai dai wannan lokacin Musulmin duniya za su bi shi don yaƙar DAJJAL da mabiyansa. Annabi Isah zai kira Yahudawa zuwa Musulunci, baya son komai daga gare su a lokacin sai su karɓi Musulunci.
Wasu daga cikinsu za su Musulunta, wasu kuma za su ci gaba da zama mabiya addinin Yahudanci, sannan yaƙin da Manzon Allah (ﷺ) ya ambata a cikin Hadisi zai wakana.
Manzon Allah (ﷺ) Yace: "Al-ƙiyama ba za ta tsaya ba har sai Musulmai sun yaƙi Yahudawa suna masu kashe su, har sai Bayahude ya ɓoye a bayan dutse da itatuwa suna kuka da neman ceto sai dutse yace: Ya kai Musulmi kazo akwai wani Bayahude yana ɓoye a bayana kazo gashi ka kashe shi"
Allah Maɗaukakin Sarki zai girmama Musulmi a wannan yaƙin da wannan mu'ujiza, wato duwatsu da bishiyoyi za su yi magana su kira Musulmi da su zo su kashe Yahudawan da za su fake a bayansu.
Wannan yaƙi da Musulmi zasu yi ƙarkashin jagorancin Annabi Isah (a.s) ɗaya daga cikin manzannin Allah masu daraja, zai kasance a kan DAJJAL ne da magoya bayansa (Kafirai) da s**a taru don yaƙar Musulmi.
Wannan yana nuni da cewa zai kasance yaƙi ne na adalci wanda Allah ya yarda da shi, kamar yadda ya faru a dukkannin yaƙunan Musulunci da nufin ɗaukaka kalmar Allah a doron ƙasa.
Yazo a cikin Hadisin da Musulim ya ruwaito Manzon Allah ﷺ Yace: "Duk wanda ya yi yaƙi domin kalmar Allah ta tabbata a (doron ƙasa) toh, haƙiƙa shine ya ke yaƙi a tafarkin Allah"
Allah ka ɗaukaka darajar Addinin Musulunci da Musulmi baki ɗaya! Allahumma Ameen 🤲
~A_sada_Wannan shine abinda zai faru idan DAJJAL ya bayyana a Duniya! 👇
Idan Dajjal ya fito dubunnan YAHUDAWA za su bi shi, su yi tururuwa a kansa, da nufin yaƙar Musulmi.
Daga nan sai Annabi Isa (a.s) ya sauko, a dai dai wannan lokacin Musulmin duniya za su bi shi don yaƙar DAJJAL da mabiyansa. Annabi I ~{A_sada modachi}