Al-Qur'ani Jirgin Tsira.

Al-Qur'ani Jirgin Tsira. Al-Qur'an

(Cire Tan-Tama 010)Tambaya:Miye Hukuncin Sallar Wanda Yakeda Lalura Ta Yoyon Fitsari Ma'ana Baya Iya Rike Fitsari?Amsa:✍...
30/01/2026

(Cire Tan-Tama 010)
Tambaya:
Miye Hukuncin Sallar Wanda Yakeda Lalura Ta Yoyon Fitsari Ma'ana Baya Iya Rike Fitsari?

Amsa:
✍️Abunda Ake Bukata Kawai Shine A Kowace Sallah Yayi Tsalki Tareda Sake Alwala Sai Yayi Sallah Kuma Sallarsa Tayi In Sha Allahu.

❔To Idan Fitsarin Yazo Yana Cikin Sallah Fa❔

✍️Komai Yawan Fitsarinda Ya Dawo Masa Acikin Sallah Bazai Bata Masa Sallah Ba Sallarsa Tananan In Sha Allahu.
Tunda Uzuri Ne Kuma Yayi Iya Kokarinsa Yayi Tsalki Kuma Yayi Alwala.

Allah Madaukakin Sarki Yana Cewa:
فاتقوا الله ماستطعتم

Ku Kiyaye Dokokin Allah Gwargwadon Iyawarku.

Suratul Tagwabun.

Allahu A'alam.

✅Zaku Iya Copying Da Sharing Domin Yan Uwa Su Amfana.

(Cire Tan-Tama 09)Tambaya:Idan Imam Yana Bada Sallah Bayan Yayi Ruku'u Sai Yaji Tafiyar Mutane Sunaso Su Samu Jam'i Shin...
30/01/2026

(Cire Tan-Tama 09)
Tambaya:
Idan Imam Yana Bada Sallah Bayan Yayi Ruku'u Sai Yaji Tafiyar Mutane Sunaso Su Samu Jam'i Shin Zai Jirasu Ne Ko Zai Tashi Tsaye Batare Da Jiransu Ba?

Amsa:
✍️Abu Na Farko Dai Musani Abunda Ake Butaka Shine Kada A Tayarda Sallah Sai Anjira Jama'a Sun Taru Tukuna Domin A Samu Adadi Mai Yawa Acikin Jam'i.

✍️Abu Na Biyu Kuma Shine Sabaninda Malamai S**ayi Akan Wannan Mas'alar. Har Zuwa Kaso Biyu:

1. Akwai Malamai Irinsu Imam Abu Hanifa Da Malik Da Shafi'iy Sunada Fahimtar Cewa Idan Liman Yana Ruku'u Bazai Jira Kowa Ba Kuma Idan Ya Jira Wani Domin Ya Samu Raka'arda Yake Kanta To Sallarsa Ta Lalace Domin Yayi Wasu Ayyukan Sallah Ba Don Allah Ba

Imam Malik Yace: Idan Imam Yace Zai Jira Wani Mutum To Wani Zai Iya Kara Zuwa Haka Wani Zai Iya Sake Kara Zuwa Kaga Sallah Ta Tsaya Kenan Saboda Haka Bazai Jira Ba.
Saidai Basuda Hujjah Sai Wannan Ijtihadin Dasukayi.

2. Fahimta Ta Biyu Kuma Itace Wasu Malamai Suna Ganin Za'a Iya Jiran Wanda Yake Zuwa Domin Ya Samu Wannan Raka'a Saboda Dalilai Guda 2

🥇Dalili Na Daya Annabi S.a.w Ya Taba Tsawaita Sujuda Saboda Daya Daga Cikin Jikokinsa Hasan Ko Husaini Ya Hau Kan Bayansa Yana Cikin Sujuda.
🥈Dalili Na Biyu Kuma Annabi S.a.w Ya Taba Takaita Sallah Saboda Yaji Kukan Jaririm wata Mata Da Take Sallah A Bayansu.

S**ace Annabi S.a.w Ya Tsawaita Sallah Saboda Wani Mutum Kuma Ya Takaita Saboda Wani Mutum To Kunga Kenan Don Wani Yayi Irin Haka Ba Laifi Bane Ma'ana Dai Zaka Iya Jiran Mai Zuwa Ya Samu Wannan Raka'a Kafin Ka Tashi Tsaye:

✍️Tawa Fahimta Za'a Iya Jira Amma Kada Ya Wuce Mutum Daya Domin Shima Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam Iya Mutum Daya Ya Tsawaita Dalilinsa Haka Kuma Dalilin Mutum Daya Ya Takaita Allahu A'alam

Domin Karin Bayan Zaku Iya Duba Littafen.
مختصر اختلاف العلماء

✅Zaku Iya Copying Da Sharing Domin Yan Uwa Su Amfana

(Cire Tan-Tama 08)Tambaya: Miye Hukuncin Bin Masbuqi Sallah? Amsa:Masbuqi: Shine Wanda Ya Samu Raka'a Daya Ko Biyi Tared...
28/01/2026

(Cire Tan-Tama 08)
Tambaya:
Miye Hukuncin Bin Masbuqi Sallah?

Amsa:
Masbuqi: Shine Wanda Ya Samu Raka'a Daya Ko Biyi Tareda Liman Kokuma A Takaice Bai Samu Cikakkar Sallah Tareda Liman Ba.
✍️ Malamai Sunyi Sabani Akan Wannan Mas'alar Har Gida Biyu:

1. S**ace Baza'a Bi Masbuqi Sallah Ba Musamman A Mazhabar Malikiyya.
Dalili: Gaskiya Ban Taba Ganin Wani Dalili Na Shara'a Daya Nuna Hakan Ba A Iya Bincike Na.
Bayanai Cikakku Akan Hakan Zaku Samesu Acikin Littafen Fikhul Islam.

2. Sukuma Malamai Na Biyu Suna Fatawa Akan Za'a Iya Bin Masbuqi Sallah.
✍️S**ace Shi Masbuqi K**ar Wanda Yake Sallah Shi Kadai Ne, Saboda Haka K**ar Yanda Sallarsa Take Karbuwa Haka Idan Kayi Sallah A Bayansa Sallarka Take Karbuwa.

Wannan Shine Fahimtar Uthaimin Kuma Nima Nafi Karkata Akan Wannan Fatawar Domin Babu Hujjah Akan Karhancin Hakan A Hadisi Ingantacce A Iya Sanina Saboda Haka Duk Wanda Sallarsa Shikadai Take Inganta To Idan Ka Bisa Sallarka Ta Inganta In Sha Allahu.

Allahu A'alam.

✅Zaku Iya Copying Da Sharing Domin Yan Uwa Su Amfana

(Cire Tan-Tama 07)Tambaya:Mace Ce Tana Cikkin Iddar Saki Sa Mijinta Wanda Ya Saketa Ya Rasu, Shin Zata Cigaba Da Iddar S...
27/01/2026

(Cire Tan-Tama 07)
Tambaya:
Mace Ce Tana Cikkin Iddar Saki Sa Mijinta Wanda Ya Saketa Ya Rasu,
Shin Zata Cigaba Da Iddar Saki Ne Kokuma Takaba Zata Koma Ma'ana Iddar Mutuwa?

Amsa:👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇
✍️Irin Wadannan Matan Kala Biyu Ne:
1. Wacce Akayiwa Saki Uku Wanda Ba Kome
2. Wacce Aka Yiwa Saki Daya Ko Biyu Wacce Za'a Iya Dawo Da Ita.

1. Ta Daya:
✍️Wacce Akayiwa Saki Uku Wanda Ba Damar Dawowa Da Ita To Idan Mijinta Ya Rasu Batada Gado Koda Bata Gama Iddah Ba Kuma Bazata Daina Iddar Saki Ba Domin Batada Alaka Da Mijin A Yanzu.

2. Ta Biyu:
✍️Wacce Aka Yiwa Saki 1 Ko 2 Wacce Za'a Iya Dawo Da Ita,
To Ita Irin Wannan Idan Mijinta Ya Rasu Tana Cikin Iddah Bata Kammala Ba To Lallai Ana Bata Gado Domin Tanada Alaka Da Mijinta,
Sannan Kuma Zata Saki Iddar Saki Ta Koma Takaba Ma'ana Iddar Mutuwa Zata Koma Sai Tayi Wata Hudu Da Kwana 10 Shekenan Daga Nan Tana Iya Yin Wani Sabon Aure.

Ku Duba Littafen Minhajul Muslim Na Abubakar Jabir Al-Jaza'iry.

Kitabul Mu'amalat Baben Aure Inda Yake Magana Akan Kalolin Iddah.

Allahu A'alam.

✅Zaku Iya Copying Da Sharing Domin Yan Uwa Su Amfana.

(Cire Tan-Tama 06)Tambaya:Dan Allah Mlm Munaso Takaitaccen Bayani Akan Kabli Da Ba'adi?Amsa:✍️Ma'anarta: Shujudar Rabkan...
27/01/2026

(Cire Tan-Tama 06)
Tambaya:
Dan Allah Mlm Munaso Takaitaccen Bayani Akan Kabli Da Ba'adi?

Amsa:
✍️Ma'anarta: Shujudar Rabkanuwa Wasu Sujudai Ne Guda Biyu Da Ake Bukata Mai Sallah Yayi Domin Gyara Wani Gibi Da Aka Samu Acikin Sallarsa Ta Hanyar Ragi Ko Kari.

✍️ Kashe-kashensa: Sun Kasu Gida Biyu Wasu Kafin A Sallama Akeyinsu (Kabli) Kenan Wasu Kuma Bayan Anyi Sallama(Ba'adi) Kenan.

✍️Na Farko (Kabli) Kenan
Ana Yin Sujuda Ne Kafin Ayi Sallama Aduk Sanda Akayi Ragin Sunnah Daya Ko Fiyeda Haka A Sallah Amma Wasu Malamai S**ance Sai Sunnah 2 Zuwa Sama.

Misali: Wanda Yayi Raka'a Biyu Sai Ya Manta Baiyi Zaman Tahiya Ba To Zai Wuce Ya Cika Sallarsa Sai Yayi Kabli Domin Yayi Ragin Sunnah 2 Zaman Tahiya Dakuma Tahiya.

✍️Ta Biyu (Ba'adi) Kenan
Sukuma Anayinsu Ne Bayan Anyi Sallama Saboda Wani Kari Da Akayi A Sallah.

Misali: Idan Mutum Ya Zauna A Raka'ar Farko To Yayi Kari Domin Ba Zama Wajen, Kokuma Ya Kara Raka'a Daya Ko Biyu, Kokuma Ya Kara Tsayuwa Ko Abunda Yayi K**a Da Haka To Zaiyi Ba'adiyya.

✍️Yanda Akensu:
Kowacce Anayin Iya Sujuda 2 Ne A Sallame Shine Mafi Inganci Domin Babu Hadisi Ingantacce Akan Yin Tahiya Bayan Yin Sujudar Rabkanuwa Amma Idan Mutum Yayi Ba Laifi Domin An Samu Hadisai Masu Rauni Akan Hakan Wanda Idan Aka Tattara Su Sai Su Zama (Hasan).

Domin Karin Bayani Ku Duba Littafen Alwajeez Fee Fiqhissunnati Wal Kitabil Azeez

Zaku Iya Duk Tamyarda Kuke Da Ita A Comment Section.

✅Zaku Iya Copying Da Sharing Domin Yan Uwa Su Amfana.

(Cire Tan-Tama 05)Tambaya:Wanda Ya Samu Raka'a Biyu Tereda Liman  A Sallar Magrib Ko Isha, Yaya Zaiyi Ya Rama Sauran, Sh...
23/01/2026

(Cire Tan-Tama 05)
Tambaya:
Wanda Ya Samu Raka'a Biyu Tereda Liman A Sallar Magrib Ko Isha, Yaya Zaiyi Ya Rama Sauran, Shin A Bayyane Ko A Boye Zaiyi Karatu?

Amsa:
✍️ Malamai Sunyi Sabani Akan Wannan Mas'alar Kuma Dukkaninsu Hujjarsu Hadisi Dayane.
Sabanin Akan Sabanin Riwayat Da Aka Samu Ne ,
✍️Wasu Hadisai Sunzo Da فاقضوا Wato Ku Rama.
Shine Hujjar Wanda Suke Cewa Ayi Karatu A Bayyane.
✍️Wasu Kuma Riwayoyin Sunzo Da Kalmar فأتموا Ma'ana Ku Cika
Wanda Shine Hujjar Wanda Suke Cewa Ayi Karatu A Asirce.

✍️Saboda Post Din Bazai Dauka Ba Zamuyi Bayani A Takaice Ne K**ar Haka:

✅Cewar Ayi Karatu A Asirce Shime Mafi Inganci Saboda Dalilai K**ar Haka:
1. Hadisan Da S**azo Da Kalmar فأتموا sunfi Yawa Akan Wadancan Hadisan Masu فاقضوا.
2. Kalmar فاقضوا Takan Daukar Ma'anar Cikawa Amma Kalmar فأتموا Bata Taba Daukar Ma'anar Ramawa.
K**ar Yanda Allah Yace ثم ليقضوا تفثهم
A Suratul Hajji Kaga Yana Nufin A Cika Ayyukan Hajji Bawai A Rama Na Baya Ba.

Saboda Haka Idan Mutum Ya Bayyana Baiyi Laifi Ba Amma Mafi Dacewa Shine A Boye Karatu Kuma A Karanta Iya Fatiha Kawai.

Domin Kai Raka'o'inda Ka Samu Tareda Imam Sune Na Farko A Wajenka Saboda Haka Yanda Kake Yin Raka'o'in Karshe Idan Kana Sallah Kaikadai Haka Zaka Rama Su Idan S**a Rage Maka Tareda Liman.

Allahu A'alam.

✅Zaku Iya Copying Da Sharing Domin Yan Uwa Su Amfana..

22/01/2026

I'm on the weekly engagement list for Shafin Ibnul Islam Albuwady.

(Cire Tan-Tama 04)Tambaya:Wanda Yana Musulmi Kuma Ya Daina Sallah Sai Bayan Shekara 1 Ko 2 Saiya Tuba Shin Ya Zaiyi Zai ...
22/01/2026

(Cire Tan-Tama 04)
Tambaya:
Wanda Yana Musulmi Kuma Ya Daina Sallah Sai Bayan Shekara 1 Ko 2 Saiya Tuba Shin Ya Zaiyi Zai Rama Wannan Sallolin Ko Zaici Gaba Ne Kawai Daga Inda Ya Tuba?

Amsa✍️
Akwai Wani Babban Malami Mai Suna Ibn Hazmin Acikin Littafensa Al-Muhallah Volume Na 2 Shafi Na 235. (2/235)
Yake Cewa:
Hakika Allah Ya Sakawa Kowace Sallah Lokuta Guda 2, Tana Inganta Idan Aka Yita Cikin Dayan Lokutan Kuma Tana Lalacewa Idan Akayi Ta Cikin Dayan Lokutan .

✍️Ya Kara Da Cewa : Babu Banbanci Tsakanin Wanda Yayi Sallah Kafin Lokacinta Da Kuma Wanda Yayita A Bayan Lokacinta.

✍️Yaci Gaba Da Cewa: Rama Sallah Aiki Ne Na Shara'a Saboda Haka Yana Bukatar Allah Da Manzon Sa Sallallahu Alaihi Wasallam Suyi Magana Akan Hakan Kuma Basuyi Ba Kuma Tabbas Allah Baya Mantuwa .

✍️A Takaice Ya Nuna Cewa Wanda Yabar Sallah Da Ganganci Har Lokacin Ta Ya Fita To Babu Hujjah Ko Daya A Al-Qur'ani Ko Hadisi Da S**ace A Rama Sallar Saboda Haka Ramata Ma Kuskure Ne.

Mu Duba Littafen Alwajeez Fee Fiqhissunnati Wal Kitabil Azeez Shafi Na 86-87.

Kammalawa.
Wanda Yabar Sallah Da Ganganci Har Lokacin Ta Ya Fita Ba Wani Uzuri Na Shara'a To Baya Ramawa Kuma Koya Rama Baza'a Karba Ba K**ar Yanda Uthaimin Ya Fada A Littafensa Sifatu Salatinnabiyyi.

Hanya Dayace Maganin Hakan Shine Nadama Da Istigfari Sai Kuma A Tinkari Gaba.

Allahu A'alam.

✅Zaku Iya Copying Da Sharing Domin Yan Uwa Su Amfana.

(Cire Tan-Tama 03)Tambayar Yau Itace:Miyasa Naga Wani Liman Yana Sallah Wa Gawaye Dayawa A Tare Amma Daya Daga Cikin Gaw...
21/01/2026

(Cire Tan-Tama 03)
Tambayar Yau Itace:
Miyasa Naga Wani Liman Yana Sallah Wa Gawaye Dayawa A Tare Amma Daya Daga Cikin Gawayen Kansa A Bude Yake Ya Abun Yake?

Amsa:
✍️ Na Farko Dai Musani Ya Halasta A Hada Gawaye Dayawa Waje Daya Ayi Masu Sallah Kuma Za'a Iya Hade Gawayen Maza Da Mata Ayi Masu Sallah A Tare Koda Sunkai 100 Sama Da Haka.

✍️Abu Na Biyu Kuma Idan Za'ayi Sallar To Maza Za'a Kawo A Farko Daga Wajen Liman Kuma Koda Kananan Yara Ne Sannan Mata Su Biyo Baya Kuma Ana Duba wanda Yafi Iya Karatun Al-Qur'ani A Kowosa Wajen Liman.

✍️Abu Na Uku Kuma Ana Yiwa Gawa Sallah Ne Cikin Cikakkiyar K**ala Tareda Sitirce Jikinsa Sai Idan Wani Dalili Ne Yasa A Bude Kan Nata K**ar:

✅Idan Mutum Yana Cikin Aikin Hajji Ya Rasu To Ba'a Rufe Kansa A Haka Za'a Masa Sallah Kuma A Bixnesa Kansa A Bude.

Allahu A'alam.

✅Zaku Iya Copying Da Sharing Domin Yan Uwa Su Amfana.

21/01/2026
Tareda Daya Daga Cikin Admins Namu
21/01/2026

Tareda Daya Daga Cikin Admins Namu

Sallallahu Alaihi Wasallam
21/01/2026

Sallallahu Alaihi Wasallam

Address

Nigeria
Sokoto

Telephone

+2349160704044

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Al-Qur'ani Jirgin Tsira. posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Place Of Worship

Send a message to Al-Qur'ani Jirgin Tsira.:

Share