Yobe Islamic Center

Call Directions Contact the place of worship

Yobe Islamic Center THIS PAGE IS CRITICALLY ABOUT SUNNAH AND DAAWAH

Assalam alaikum.....Aigan studeos Embark On Architectural Desings In Other Meet With Numerous Client Needs For The Basis...
07/08/2016

Assalam alaikum.....Aigan studeos Embark On Architectural Desings In Other Meet With Numerous Client Needs For The Basis of CAD Symposium An Today's Virtual Technology. We Try to Lunch A Platform Were People Can Browse,Interact,Download Our Virtual Models.So Try to Have a Good and awesome Number Of Likes on Our Wonderful Page www.facebook.com/aiganstudeos

12/09/2014

Sayyida Fatima al-Zahra (a.s) - Matar Aure:

________________________
Fatima ta tare a dan karamin gidan mijinta Ali bin Abi Dalib (a.s.) alhali tana mai farin ciki da amincewa da shi. Ta rayu tare da mijinta cikin kwanciyar hankali da farin ciki, ko da yaushe tana cikin sakin fuska, tsananin rayuwa ma taba raba gidanta da farin cikinsa ba. Ita ce matar Ali gwarzon Musulunci, ma'abucin sadaukar da kai kuma mai dauke da tutar jihadi da nasara.

Fatima (a.s.) ta kasance ita ma daidai da haka. Ta kasance tare da Ali k**ar yadda mahaifiyarta Khadija ta kasance tare da Manzo (s.a.w.a), tana gamayya da shi ciki jihadinsa, tana kuma hakurewa wahalhalun rayuwa, don haka sai ta aiwatar da aikinta daidai da yadda Allah Madaukaki Ya zabe ta don shi.

Ali da Fatima (a.s) sun rayu a inuwar Manzo (s.a.w.a) kuma karkashin kulawarsa. Manzo ya ba Fatima abin da bai ba kowa ba bayan aurenta, ta yadda tsananin lurarsa da ta'allakar zuciyarsa da ita har ya kai in zai yi tafiya ko zai je yaki Fatima ce karshen wadda ke sallama da shi. Kuma idan ya dawo daga tafiyarsa ko yakinsa Fatima ce farkon wadda ya ke fara haduwa da su daga mutane.

Fatima (a.s.) ta rayu a gidanta a matsayin uwar-gida; tana lura da al'amuran gidanta kuma tana aiwatar da bukatun gidan bisa dogaro da kokarinta. Bata kasance tana da masu hidima ko bayi ko 'yan aiki ba. Duk rayuwarta ta kasnce jihadi ne da kokari.

Fatima ta kasance tana nika sha'iri, ta yi amfani da dutsen nika da hannunta, tana yin Alkubus da kanta, tana share gida kuma tana aiwatar lizimce-lizimcen iyali. Hakika kuma Manzo (s.a.w.a) da Ali (a.s.) sun kasance suna ganin haka daga Fatima, kuma suna tarayya da ita a cikin wahalhalun, suna kaskanta wahalhalun rayuwa a idonta. Ali (a.s.) ya kasance yana taimakonta a aikace-aikacen gida da gudanar da al'amuransa.

An ruwaito cewa Manzo (s.a.w.a) ya taba shiga wajen Fatima, sai ya same ta tana kuka a lokacin tana nika alhali tana sanye da wani mayafi na fatar rakumi. Yayin da ya ganta sai ya yi kuka ya ce: "Ya Fatima, jure dacin rayuwar duniya a yau da ni'imar gobe lahira. Sai Fatima ta ce: "Ya Manzon Allah, godiya ta tabata ga Allah a kan ni'imominSa"(1)

Haka Manzon Allah (s.a.w.a) da Ahlulbaiti (a.s.) ke ba mu darussan rayuwa da tsarkakken misali na shugabanci a Musulunci. Ina Musulunci da irin rayuwar holewa da jin dadi na fajirci da muke gani a yau? Ina tarihin yanayin rayuwar al-Mustafa (s.a.w.a) da tsarkakan iyalansa da irin girman kan mawadata da almubazzarancin masu hannu-da-shuni alhali a gab da su akwai dubban mayunwata da matalata?

12/09/2014

Zab'ar Mace Ko Namijin Aure
Ina godiya ga Allah da ya ba ni damar rubuta wannnan littafi mai suna "Zab'ar Mace Ko Namijin Aure" wanda yake nuni da wane namiji ko wace mace ce za a zab'a don zama tare. Mun rubuta wannan littafi ne daidai yadda zai dace da al'adun mutanenmu da kuma bayaninsa bisa ra'ayoyi mabanbanta, wannan ya taso ne musamman bayan mun ga ya dace mu rubuta wani abu wanda zai zama mai amfani ga al'ummarmu.
Littafin ya k'unshi tak'aitaccen bayani ne game da yadda ya k**ata gida ya kasance, da siffofin ma'aurata, da kuma yadda ya k**ata su kalli rayuwa, da abin da ya shafi kula da hak'k'in juna k**ar yadda musulunci ya gindaya ba tare da k'etare iyaka ba.
Muna fatan littafin ya zama mai amfani ga d'an Adam a yanayin zamantakewar gida, ta yadda zai zama sanadi na gina al'umma saliha da cigaban duniyar musulmi baki d'aya.
Ina rok'on Allah ya bayar da ladan rubuta wannan littafi ga malamaina da dukkan wanda ya sanar da ni wani abu da amfaninsa ya shafi duniya da lahira.

A musulunci an yi umarni ne da a yi aure ba domin biyan buk'ata ta duniya ko ta sha'awa ba kawai, akwai buk'ata ta gina al'umma saliha da zata ci gaba da d'aukar nauyin isar da sak'on Allah a duk fad'in Duniya, wanda wannan yana buk'atar taimakekeniya tsakanin ma'aurata, sa'annan akwai samun nutsuwa ta ruhi da d'an Adam yana buk'atarsa wanda an sanya shi ne ya zamanto ta hanyar zamantakewa tsakanin miji da mata.
Misali mace koda ta yi ilimi kuma ta samu komai na wannan duniya, da dukkan ni'ima, haka nan ma namiji, idan ba su da mai d'ebe musu kewa ta fuskacin zaman auratayya to akwai wani gib'i babba da ba su cike shi ba, wanda ba ya samuwa sai ta hanyar auratayya, wacce kur'ani mai girma ya yi nuni da ita , k**ar yadda a zamantakewar tare tsakanin ma'aurata idan aka mayar da k'auna da so s**a koma k'iyayya da gaba, abin yakan fi zama ba tare da mai d'ebe kewa ba muni. Kamar yadda haka nan ana son yin aure da wuri ga wanda ya balaga matuk'ar ya samu yalwa, domin a cikin rashin yin hakan akwai fitina a bayan k'asa da fasadi mai girma k**ar yadda ya zo daga Ahlul Baiti (a.s) . Mu sani akwai k**alar da ba ta yiwuwa a san ta ko a kai zuwa gareta sai ta hanyar aure, kuma ba ta samuwa ta hanyar zaman banza da fasik'anci. Irin wad'annan abubuwan sun had'a da: sanin ma'anar ciyarwa, yafewa, soyayya, hak'uri, juriya, d'aukar nauyin mutane, reno, tarbiyyar 'ya'ya, fahimtar k'imar iyaye, tunanin gida da sauransu.
Ayatul-Lahi makarim shirazi yana cewa: saudayawa daga cikin abubuwa k**ar ma'anar soyayya, da k'auna, da yafewa, da kyauta, da baiwa da tausayi, da fansar rai, ma'anarsu ba ta ganuwa da fahimtuwa sai da aure, wanda zaman banza ba tare da aure ba da matar haram ko zaman gwauranci da rashin aure ba za a iya fahimtar hak'ik'aninsu ba, kuma riskarsu tana yiwuwa ta hanyar zamantakewar aure ne kawai .

Masu ilimi sun kawo wasu abubuwa k**ar haka da s**an kawo jinkirin aure:
1- Tsawon muddar lokacin karatu: ta yadda saurayi ko budurwa kafin ya kai ga kammala jami'a ya kai shekara talatin zuwa talatin da biyar a mafi yawan lokuta, saudayawa wannan yakan jefa wasu cikin halin da s**a katse karatu idan ba zasu iya had'a biyun ba, don haka yana kan al'umma da gwamnatocinsu su yi tunanin maganin wannan koda ta hanyar tallafi ne a kan 'yan makaranta. Misali a nan a k'asar farisa s**an yi k'ok'arin yi wa dubunnan d'aliban jami'a aure a kyauta kowace shekara da kuma ba su tallafi.
2- Samun damar yin alak'ar haram: Yawaitar gidajen karuwai da wajajen fasik'anci saudayawa yakan sanya wasu samari su ga ya fi musu sauk'i su je su yi mummunar mu'amala ta haram da matan banza na wani d'an lokaci tsawon rayuwar samartakarsu. Wannan ma wani abu ne da musulunci ya sanya mafita gareshi ta hanyoyi da dama k**ar haka:
a- Tallafin aure da wuri daga baitul mali ga dukkan wanda ba zai iya aure ba kuma da buk'atar hakan domin ya balaga.
b- Tarbiyyantarwa ta hannun malamai, da kafafen watsa labaru da jaridu da makarantu.
c- Hana gida ehehhehdjen fasadi da kulle duk wani waje da ahar.

26/03/2014

Barka da yamma pans

28/12/2013

DUNIYAR MA'AURATA
karin aure: Amsoshin tambayoyin masu karatu (2)
Assalamu alaikum Makarantanmu, barkanmu da
sake haduwa cikin wannan fili. Da fatan Allah Ya
amfanar da mu dukkan bayanan da za su zo
cikinsa, amin. Ga karashen amsoshin wasu daga
cikin tambayoyin da kuka aiko game da matsalolin
da ke tattare da karin aure, da fatan Allah Ya sa
wannan bayani ya isa ga duk masu bukatarsa
musamman wadanda s**a aiko da tambayoyi, amin.
Ya halatta uwargida ta hana karin aure?
Ni dai na yi rarrashin duniyar nan, amma
uwargidana ta ki bari in kara aure, ta ce wai sai dai
in rabu da ita kafin na kara aure, ni kuma wallahi ina
sonta, karin auren ne ya k**a ni dole, amma ita ta
ki fahimta; shin ko matar mutum na da wannan ikon
ta hana mijinta karin aure a kan sai dai ya rabu da
ita? Daga Mai son uwargidansa.
Kamar yadda bayani ya gabata, bai halatta ba
uwargida ta hana maigidanta karin aure a kan bisa
ko ma wane dalili ba; babu wanda yake da ikon
haramta wa mutum abin da Allah Ya halatta masa
komai matsayin mutumin nan kuwa; kai ko kai
kanka ba daidai ba ne ka haramta wa kanka abin da
Allah Ya haramta maka shi. Domin Annabin Rahma
SAW ma, Allah Ya yi hani gare shi a kan haramta
wa kansa abin da Allah Ya halatta Masa SAW:
“Ya Kai Annabi! Don me Kake haramta (wa Kanka)
abin da Allah Ya halatta maka don neman yardar
Matanka? Kuma Allah Mai Gafara ne, Mai Jinkai.”
Surah 66; Aya 1. Don haka shawarar Duniyar
Ma’aurata gare ka shi ne: Ka ci gaba da rarrashinta,
da alama barazana ce kawai take yi maka, don ta
san kana da wannan raunin na ba za ka iya rabuwa
da ita ba, inda ta san akwai yiwuwar ka iya din, da
kila ba za ta yi maka wannan barazanar ba. Ka
kuma dage da yi mata addu’a da Allah Ya sa ta
gane ta hakura ta dauki kaddara; a cikin haka kuma
ka ci gaba da shirye-shiryen karin aurenka kana
mai ci gaba da rokon Allah Ya sa alheri a cikinsa,
kuma ya zama alheri gare ku duka duniya da lahira,
amin. Da fatan Allah Ya ganar da uwargidanka da
duk mata Musulmi masu irin wannan karkataccen
ra’ayin, amin.
Na kasa yin adalci!
Na kasa daidaita sha’awa da mu’amular aure kan
matana biyu masu shekaru sama da sittin da ta uku
mai shekaru 29. Na yi kokarin na daidaita su na
kasa, saboda bambancin shekaru. Ina tsoron kada
Allah SWT Ya k**a ni da rashin adalci, ya ya zan
yi? Daga Ali N.
To Malam Ali tun da har kana tsoron kada Allah Ya
k**a ka da rashin adalci, to ka bari tsoron Allah ya
yi maka jagora zuwa ga aikata daidai don ka tserar
da kanka daga irin wannan tuhuma. Kamar yadda
bayani ya gabata, sha’awa da ibadar aure ba lallai
ba ne sai an daidaita su tsakanin mata, duk ma
wanda ya yi kokarin yi, to da wuya ya yi nasara;
iyaka dai kowacce a tabbatar ana ba ta hakkinta na
ibadar aure daidai gwargwadon hali. Amma sauran
al’amuran mu’amular aure irinsu ci da sha, tufafi,
muhalli da kyakkyawar zamatakewa, to wannan
dole ne sai an daidai su tsakanin mata. Da fatan
Allah Ya kara maka da dukkan magidanta karfin
gwiwa wajen dagewa ga zantar da adalci tsakanin
mata, amin.
Ya halatta hada ‘Yan uwa biyu kishi?
Anti Nabila ni dai ba na kyamar kishiya kuma ina
murna da a kawo min abokiyar zama, ko ba komai
na samu abokiyar hira ba sai na bi makwabta ba;
kuma in ba ni lafiya ta taya ni kula da ‘ya’ya; amma
sai dai kash, duk da haka ina jin zafin kishiyar da za
a kawo min yanzu domin ‘yar uwa ta ce;
mahaifiyata da tata abokan wasa ne, shin irin haka
ya halatta, kuma yaya zan yi in daina jin kyamar
abin? Zakiyya.
‘Yan uwan da s**a fito tsatso daya ne yake
haramun a hada su kishi a lokaci daya; amma duk
wata dangantaka bayan wannan to ya halatta a
musulunce, kuma ba wani abin kyama ba ne ko abin
tir ga mijin da ya yi haka ko ga iyayen da s**a
bayar da diyarsu ga irin wannan auren.
Sai dai k**ar yadda Hausawa kan ce ‘wai ana
barin halal don kunya’ domin zafin zuwan kishiya
yana da zafi da kuna sosai ga mafi yawan mata,
don haka gara a ce wani bare zai yi sanadin jin
wannan zafin ba dan uwa na jini ba.
Yadda za ki yi ki daina kyamar irin wannan auren
shi ne, sai ki tuna da cewa duk wani abu da
Addininmu ya halatta mana shi, to ba daidai ba ne
mu kyamace shi, don ba yadda za a yi Allah Ya
halatta abin kyama a gare mu; ki kuma dage da yin
addu’a na Allah Ya wanke maki wannan kyama
daga cikin zuciyarki, sannan ki tuna cewa in dai har
zamanku ya yi dadi da abokiyar zamanki, to zai
kara dadada kasancewarta ‘yar uwarki ce; ko ba ku
auren miji daya, ke dolen ta ce ga kyautatawa kuma
‘ya’yanki ai ‘ya’yanta ne ko ba don aure ba. Da
fatan Allah Ya ba ku zaman lafiya ya sa alheri a
cikin rayuwar aurenku, amin.
Zan dakata a nan, sai mako na gaba InshaAllah, da
fatan Allah Ya sa mu kasance cikin kulawarSa a
koda yaushe, amin.

28/12/2013

DORA WA ’YA’YA
TALLA: IYAYE
MATA A JI TSORON
ALLAH
Assalamu alaikum. Ina fara wa da sunan Allah
Madaukakin Sarki. Gaisuwa mai tarin yawa a gare
ku iyaye; maza da mata, Allah Ya kara mana
kwanaki, Ya sa mu gama da duniya lafiya. A yau
wannan rubutu zai karkata ne ga iyaye musamman
mata, kasancewar akwai wani babban kuskure da
kuke tafkawa a matsayinku na iyaye. Wannan
kuskure yana da illoli masu muni wadanda daga
karshe za ku fada tarkon da na sani, a lokacin da
bakin alkalami ya riga ya bushe.
Wannan kuskure da ku ke yi kuwa ba wani kuskure
ba ne a yawancin idanun mutane marasa tunani da
hangen nesa da kuma son ci gaban al’ummar
Musulmi, su dai sun dauki wannan kuskure a
matsayin ba wata matsala ba ce, tun da bukatunsu
suna biya.
A zamanin yanzu muna fuskantar barazana a kan
wata dabi’a da iyaye mata s**a dauka na dora wa
‘ya’yansu talla, wanda kowa ya san duk yarinyar da
aka kira ta da sunan mai talla, ba a ganinta da wani
mutunci.
Iyaye mata da suke dora wa ‘ya’yansu talla sun
manta da amanar da Allah Ya danka musu, suna ta
cin amanar Allah da mazajensu wajen dora wa
‘ya’yansu talla.
A yanzu akwai wani sabon salon talla da ya fito,
wannan sabon salon talla kuwa shi ne, yara suna
zuwa su kai riba gida ba tare da sun dauki kayan
talla daga gida ba. A yanzu ana cewa daukar kayan
talla daga gida kauyanci ne, a maimakon haka ,sai
yara su tafi tasha wajen masu shaguna su dauki
tallan jus da fiya-wata (pure water), duk abin da
s**a sayar ribar tasu ce.
Abin tambaya a nan ga irin wadannan iyaye da suke
tura ‘ya’yansu suna irin wannan talla, sun tabbatar
cewa ‘ya’yan nasu tallan s**a je, s**a yi ko kuwa
wata hanya daban s**a bi s**a kawo riba gida? Ke
kuma uwa babu bincike kin karbi riba, jiki yana
rawa kina murna.
Ya k**ata iyaye masu irin wannan hali, su lura su
daina sanya ‘ya’yansu mata a hanyar hallaka ta
hanyar ba da gudunmawarsu. Kowa ya san ‘yan
mata a yanzu suna fakewa da talla suna aikata
abubuwa marasa kyau.
Talla hanya ce da ‘yan mata suke amfani da ita
suna abin da ransu yake so. Ballantana a ce yarinya
ta samu ‘yanci, ba sai ta dauki kaya daga gida tun
da riba kawai ake bukata.
Don haka, wallahi ina ganin idan ba a yi taka tsan-
tsan ba, wata rana riba biyu za a samu wato ribar
kudi da ribar karuwa.
Ina rokon iyaye a lura da halin da ‘ya’ya suke ciki a
gida da kuma wuraren da suke zuwa talla. Tun da
wasu babu yadda za su yi, dole sai sun dora wa
‘ya’yansu talla, domin ta wannan hanya ce suke
samun abinci.
‘Yan mata masu talla a ji tsoran Allah, komai kuka yi
Allah Yana gani, kuma akwai ranar hisabi.
Daga karshe, ina rokon iyaye su karfafa sanya
‘ya’yansu a makarantu, domin karatu ya fi daukar
talla. Ina fatan za a dauki wannan shawara da na
kawo, a matsayin gyara kayanka. Allah Ya gafarta
mana, amin.

23/12/2013

KARE KANKA/KI DAGA ZINA A cikin littafin Nahajul-balaga:
Hikima ta 27- ya zo cewa: An
tambaye shi game da imani sai ya
ce yana kan ginshikai hudu ne: akan
juriya, da yakini, da adalci, da jihadi:
A- Hakuri yana kan rassa hudu:
akan shauki, da tsoro, da zuhudu, da
taka-tsantsan: wanda ya so aljanna
zai fidiye (ya fita) daga sha’awaice-
sha’awaice, wanda ya ji tsoron wuta
zai nisanci haram, wanda ya yi
gudun duniya zai ga saukin musibu,
wanda ya yi sauraron mutuwa zai
gaggauta zuwa aikata alherai…”.
Sannnan a cikin littafin sakon
hakkoki na Imam Zainul-abidin (a.s)
yana cewa: "Amma kuma hakkin
farjinka shi ne ka kare shi daga zina,
ka kiyaye shi daga abin da bai
halatta ba, ka taimaka a kansa da
rufe idanuwa, domin shi ne mafi
taimakon abu, da kuma ba shi kariya
da yunwa da kishirwa idan ya yi nufi,
da yawaita ambaton mutuwa, da
kuma gargadi ga kanka saboda
Allah, da tsoratar da ita da shi,
kariya da taimako suna ga Allah ne,
kuma babu dubara ko karfi sai da
shi".
Farji wani bangare ne na gabar
da ake yin amfani da ita domin
samun haihuwa ta hanyar amfani da
shi ga namiji ne ko mace, sai dai
galibi ana kiran na mace da wannan
kalma, amfaninsa shi ne kare
samuwar nau'in mutum daga
karewa.
Wannan bangaren shi ne ya fi
kowanne hadari wurin halakarwa,
kuma a sanadiyyarsa ne aka saba
wa Allah dare da rana, da dan Adam
ba shi da wannan bangaren da
ma'anar ba a ma yi masa sha'awa
ba, to da bai sha wahalar wannan
gida na duniya ba, k**ar yadda da
ba a yi masa shi ba, da babu wani
amfanin saukowarsa duniya domin
yada zuriya.
Da farkon Imam Sajjad (a.s) ya
yi nuni da cewa kare farji daga zina
yana daga cikin hakkokin farji,
sannan shari'a ta sanya hanyoyin
kare shi daga zina, sai ta sanya
kariya ga farji da aure da'imi da
kuma auren mutu'a, domin kada dan
Adam ya fada cikin hadarin zina, sai
tarbiyyar ruhinsa ta lalace, sannan a
samar da 'ya'yan shego, sai aikata
zunubi ya yi sauki, bala'o'I su faru a
duniya barkatai.
Domin dan zina ya fi samun
saukin aikata sabo a kan dan halal,
don haka tarbiyyarsa tana bukatar
himma matuka. Akwai wani wanda
ya taba kashe wani babban wansu a
watan azumi 1428, kuma lokacin da
ya kashe shi da dutse da ya dauka
mai nauyi ya kwankwatsa masa kai
da shi, sai na ga ya yi daidai da
lokacin da aka sari Imam Ali (a.s) da
takobi wato sallar asuba 19 ga
watan ramadhan.
A lokacin babu wani abu da ya
zo mini sai cewa wannan anya kuwa
ba dan shege ba ne. Ilai kuwa sai
nan wani yake gaya mini cewa ai
bayan babarsu ta fita daga gidan da
ta haifi wan nasu da shi kanin ya
kashe wanda a sanadiyar tabin
hankali ne babansa ya sake ta. Sai
aka rasa inda take domin wasu 'yan
iska ne s**a dauke ta ba su bar ta
ba sai da ta yi cikin shegen da aka
samu cikin wannan wanda ya yi
kisan da shi da dan'uwansa 'yan
tagwai.
Da yawa zamu ga wani rashin
imani da babu k**arsa, idan mun
bincika sai mu samu ba dan halala
ba ne ya yi shi. Da sharrin zina ya
tsaya kan haka ne kawai da ya isa
sharri, domin yana hana k**alar
dan Adam, hada da kazanta da take
yawaita da yada cututtuka marasa
iyaka a cikin al'umma, ga kuma
hana ruwan sama da arziki da zai
iya mamaye al'umma sak**akon
zina.
Don haka ne sai musulunci ya
zo da hanayr aure domin ya
tarbiyyantar da al'umma, ya samo
mata hanyar mafita domin kada a yi
zina, mu sani sau da yawa samari
da 'yan mata s**a lalace saboda
rashin aure. Don haka ne Allah mai
hikima domin kada maza su fada
cikin bala'in zina sai ya sanya ikon
dukan matan da suke kin su a
kwanciya a hannunsu, bai kuma
sanya ikon dukan mace ba sai a
wannan kawai.
Sannan Allah mai hikima bai
bar wannan lamarin ba sai da ya
sanya auren mutu'a domin ya
sawwake alakar cakudar maza da
mata, wannan auren yana iya
kasancewa mafita daga zina, kuma
tun da Allah ne ya sanya shi a
matsayin doka babu wani wanda zai
iya hana shi ya hanu.
Sai dai abin takaici a
kasashenmu an yi mummunar
fahimta ga wannan auren, domin ma
ba a san shi ba, sai zinace-zinace
s**a yawaita, yana da kyau mu sani
auren mutu'a halal ne daga Allah
k**ar auren da'imi, kuma a
littafinmu na auren mutu'a mun yi
bayani a ciki dalla-dalla bisa
sharuddansa da dokokinsa.
Sarkin muminai Imam Ali (a.s)
ya kawo hana auren mutu'a da halifa
na biyu ya yi a matsayin dalilin da ya
sanya yawaitar zina a cikin duniyar
musulmi, domin da manzon Allah
(s.a.w) ya zo da shari'a ya shimfida
duk abin da zai hana mutum sabo a
cikinta, idan kuwa ba haka ba, idan
wani ya yi zina aka yi masa haddi
zai kasance zalunci ne.
Don haka duk wanda ba shi da
ikon yin auren da'imi, ya samu mace
wacce sharuddan yin auren mutu'a
da ita s**a cika, k**ar
kasancewarta ba matar aure ba, ba
kuma budurwa ba, da sauransu,
sannan sai ya yi zina, lallai wannan
ya cancanci dukkan ukubar Allah.
Amma idan da babu irin wannan
doka, sai aka k**a shi da sunan
shari'a aka yi masa ukuba, to ya
zama zalunci, domin ba yadda Allah
zai halicci mutum, sannan sai ya
hana shi hanyar mafita kan halittar
sha'awa da ya yi masa.
Ibn Abbas yana cewa: "Mutu'a
rahama ce da Allah ya tausaya wa
wannan al'umma da ita, ba domin
Umar ya hana ta ba, da babu wanda
zai bukaci yin zina sai tababbe".
Jabir dan Abdullah yana cewa:
"Mun yi auren mutu'a lokacin
manzon Allah (s.a.w) da lokacin
Abubakar, da wani bangare na
lokacin Umar, sai Umar ya ce:
Kur'ani dai shi ne Kur'ani, Manzon
Allah dai shi ne manzon Allah, kuma
dai wadannan mutu'o'in guda biyu
ne da suke lokacin manzon Allah
(s.a.w), wato hajjin tamattu'i, da
kuma auren mutu'a" (Masnad
Ahmad bn Hambal: 1 / 52). Sai dai a
nan Ahmad bn Hambal ya cire
karshen maganar ne, domin Umar
yana cewa: Ni na hana ne kuma ina
yin ukuba a kan duk wanda ya yi su.
(Masnad Ahmad bn Hambal:398).
Suyudi yana cewa: "Farkon
wanda ya hana auren mutu'a shi ne
Umar" (TarikhulHulafa: 137).
Jabir dan Abdullah yana cewa:
"Mun yi auren mutu'a lokacin
manzon Allah (s.a.w) da lokacin
Abubakar, da wani bangare na
lokacin Umar, sai Umar ya
hana" (Bidayatul Mujtahid, na
Hambalawa: 2 / 63).
Mash'huriyar maganar Imam
Ali (a.s) ta shahara cikin musulmi
cewa: "Ba don Umar ya hana auren
mutu'a ba, da babu wanda zai yi
zina sai ya tabe". Wasu suna
fassara shi da cewa: "Ba don Umar
ya hana auren mutu'a ba, da babu
wanda zai yi zina sai
tababbe" (Tafsirul Fahrurrazi: 10 /
51).
Wannan lamarin a fili yake
yana nuna cewa zina ta yawaita
cikin al'ummar musulmi ta yadda ta
shiga kowane lungu da surkukiya,
domin wannan hanin da Umar ya yi
wa auren mutu'a. Wannan magana
ce da malaman Sunna da Shi'a s**a
yi ittifaki a kanta.
Sannan fadin Imam Ali Sajjad
cewa "ka kiyaye shi daga abin da
bai halatta ba", yana karfafa mana
hanyar nan ta nisantar sha'awar da
zata kai ga fadawa cikin haram da
wannan amanar da Allah ya yi mana
ita. Wasu mutane sau da yawa suna
son su hole k**ar yadda suke so ba
tare da la'akari da haramcin Allah ko
kiyaye huruminsa ba, don haka ne
Imam (a.s) ya nuna musu cewa
hakki ne da shi kansa farji yake da
shi a kan mutum ya kiyaye shi daga
fadawa cikin halaka.
Sannan Imam Sajjad (a.s) ya yi
nuni da wasu hanyoyin taimaka wa
farji samun kariya daga sabon Allah
da fadawa cikin halaka, sai ya yi
nuni da kawar da duk wani abu da
yake share fage ne zuwa ga kaiwa
ga sabawa, yana mai cewa: "ka
taimaka a kansa da rufe idanuwa,
domin shi ne mafi taimakon abu",
wannan magana ce da ta tattaro
dukkan hikima. Domin masu hikima
suna cewa: Kallo, sai magana, sai
haduwa, sai auka wa juna.
Wato wanda ya hadu da wata
mace farkon abin da yake faruwa
tsakaninsu shi ne kallon juna, sai
kuma su yi wa juna magana, sai su
sanya inda zasu hadu, sai kuma su
hadu kan sabon Allah. Wannan su ne
matakai da suke kai wa ga saba wa
Allah da keta huruminsa, da cin
amanar farji da rashin kiyaye
hakkinsa, sai Imam (a.s) ya yi
umarni da yanke asasin farko shi ne
kallon sha'awa da kawar da kai daga
kallon juna.
Sai kuma ya gindaya wasu
hanyoyi masu muhimmanci da zasu
iya zama hanyar ladabtar da farji ya
shiga taitayinsa, domin kawar da shi
daga saba wa Allah da kutsawa cikin
haram, yana mai cewa: "da kuma ba
shi kariya da yunwa da kishirwa idan
ya yi nufi, da yawaita ambaton
mutuwa, da kuma gargadi ga kanka
saboda Allah, da tsoratar da ita da
shi, kariya da taimako suna ga Allah
ne, kuma babu dubara ko karfi sai
da shi".
Sai ya ginda ya masa
wadannan hanyoyi masu kima da
daraja da maganin taurin kan
sha'awa wacce ba ta jin maganar
hankali ba ta bin umarninsa, kuma
ba ta jin gargadinsa. Sai ya fara da
hanyar jiyar da ciki yunwa makoshi
kuwa a shayar da shi magagin nan
na kishirwa domin sha'awa kada ta
tashi, domin idan ciki ya samu koshi
ya cika, makoshi ya jike ya samu
gamsuwa, to a lokacin ne ita kuma
sha'awa zata motsa. Don haka ne
hadisi madaukaki daga manzon
rahama (s.a.w) kakansa (a.s) ya yi
umarni da yin azumi domin rage
kaifin sha'awa da maganin taurin
kanta da tak**arta, domin kada ta
jefa samari cikin bala'in sabo.
Sannan ya yi nasiha da
yawaita ambaton Allah domin zukata
su samu nutsuwar biyayya ga Allah
fiye da yadda suke samun nutsuwa
da cin abin ci da shan abin sha, ko
yin jima'i. Wanda duk ya dadani
dadin ambaton Allah (s.w.t), to
tabbas babu wani abu da zai nema a
matsayin makwafinsa, domin dadin
da rai take samu da nutsuwa da
ubangijinta babu wani dadi da ya fi
shi. Don haka ne ake iya sallamawa
a bar duk wani dadi idan dai ya ci
karo da kisa, amma sau da yawa ba
a sallama wa dadin ambaton Allah
koda kuwa za a fuskanci kisa.
Sai kuma mai aminci ya bi da
ambaton sauran hanyoyi da s**a
hada da gargadin kai da yi mata fada
don kada ta keta hurumin Allah, da
tsoratar da ita wutar Allah da zafinta
mai radadi idan ba ta ji ba, da kuma
yin addu'o'in cewa Allah ya taimaka
mana kan kare kawukanmu da
iyalanmu daga wannan hari na
sha'awa, kuma wannan ita ce mafi
muhimmancin hanya da tafi sauran
hanyoyi, domin babu wanda ya fi
wanda Allah ya ba shi kariya karfi da
tsayawa gaban harin sha'awarsa.
Babu wani abu da ya fi
sha’awa karfi a cikin mariskai, idan
ta kwashi mutum kai ka ce babu
wani abu sai ita kadai, a lokacin
jima’i dukkan wata gaba hatta da
hankalin mutum yana koma wa
zuwa ga wancan bangare na
sha’awa ne, ta yadda dukkan wani
abu na rayuwa zai kasance an
manta da shi sai wannan bangaren
kawai.
Sai dukkan gabobi su kasance
sun tashi a wannan lokacin fiye da
kowane lokaci, sai jinni ya rika
gudana cikin sauri, fatar jiki ta tashi,
lumfashi ya rika daukewa, kwayoyin
halittar fushi su tashi, jin shafa ya
kai kololuwarsa, sannan dukkan
gabobin kasa su yankwane, jijiyoyi
su motsa suna masu girgidi.
Sha'awa tana da hadari
matuka a cikin ci gaban dan Adam,
don haka ne addini ya yi nuni da
hadarinta kuma ya tanadi maganinta,
sai ya sanya hanyar aure har kala
biyu: maras lokaci (da’imi har
mutuwa) da na kayyadadden lokaci
(mutu’a), kuma ya yi umarni da
tsarkake farjin namiji da na mace
bayan fitar abubuwa daga garesu
k**ar mani da bawanli da bayan
gida, sabanin jiki k**ar gumi da ba a
sanya komai ba sak**akon fitarsa.
Sannan kuma ita wannan sha'awa
an sanya hukuncin haddi ga wanda
ya biya mata bukata ba ta hanyar
halal ba, sai aka sanya ukuba dukan
dukkan jiki har sau dari ga wanda ya
yi hakan, k**ar yadda ya ji dadi da
dukkan jikinsa ya yi sabawa.
Idan sha'awa mai karfi ta
k**a mutum takan sanya duk
jijiyoyin jikinsa su tashi, jikinsa ya yi
makyarkyata, hankalinsa ya
makanci, zuciyarsa ta kurumci, don
haka ne aka so toshe hanyoyin da
zasu kai ga marhalar biyan bukatar
haram da wannan sha'awar da wasu
daga matakan da s**a gabata.
Bayan fitar mani sai jiki ya koma
yadda yake a da, sai dukkan gabobin
jiki su yi rauni, hankali ya kwanta,
idanuwa su nemi yin bacci, sai
jijiyoyi su nemi komawa yadda suke
a da, don haka ne sai gajiya ta
mamaye dukkan jiki.
A cikin maganar Imam Sajjad
(a.s) zamu iya fahimtar samun wata
alaka tsakinin gani da ciki da farji,
domin su masu taimaka wa juna ne,
idan aka rasa daya daga cikinsu, to
bala'in sabo da yake faruwa
sak**akon sha'awa yakan yi rauni
ko ya mutu. Idan mun duba muna iya
ganin cewa, sai an gani ake so, sai
an koshi ake nema, sai da sha'awa
ne ake aukawa. Don haka aka nemi
kawar da gani, da neman taimako da
rashin koshi, da kuma ambaton Allah
da tuna mutuwa mai yanke jin dadi,
domin a samu karayar sha'awa.
Zina ita ce samar da alaka
kusaci da juna da jima'i tsakanin
namiji da mace ba tare da aure ba,
musulunci ya hana wannan alaka
saboda muninta da samar da alaka
maras karfi tsakanin namiji da mace,
da haifar da yara da ba na shari'a ba
da halacci wanda cutar hakan takan
koma wa dukkan al'umma ne.
Al'ummu da yawa ne suke
gaba da wannan lamari saboda
muninsa, suke karfafar samar da
alakar aure domin samun arzuta da
rabautar al'ummarsu, da samar da
aminci da zaman lafiya, da kawar da
dukkan cututtukan da s**an iya
haifuwa sak**akon alaka barkatai.
Har ila yau an hana zina domin
mutane su fahimci kimar daukar
nauyin iyali da yi musu hidima,
domin idan da mutum namiji zai biya
bukatarsa kawai sai ya kyale mace
da daukar ciki da sauran wahalhalu
da al'umma ta lalace, da an samu
dora nauyi kan al'ummar mata
wacce take ita ce mafi raunin
rayuwa.
Musulunci ya dauki dukkan
matakai da zasu kai ga zina, sai ya
nemi gyaran kai da cika rai da
tsoron Allah da ambatonsa, sannan
ya nemi mata su rufe kyawawansu
tun daga gashi har kafa, kuma ya
nemi karanta cakuda tsakanin maza
da mata ba tare da wani dalili ba.
Babban abin da yake hana
sha'awa da yin maganinta shi ne
cikar hankali da amfani da shi kan
dukkan abin da muke fuskanta.
Hadisai masu yawa sun yi nuni da
wannan lamari mai girma da aka yi
nuni da shi a cikin littafin Mizanul
Hikima na Raishahari, j 3, shafi:
2052, k**ar haka: "Idan hakali ya
cika sai sha'awa ta ragu". "Wanda
hankalinsa ya cika zai wulakanta
sha'awowi".
Mazon Allah (s.a.w) ya ce:
"Wanda ya yi zina da wata mata
musulma ko bayahudiya, ko kirista,
ko bamajusiya, 'ya ce ko baiwa,
sannan bai tuba ba, kuma ya ci gaba
da hakan, to Allah zai bude masa
kofofi dari uku a cikin kabarinsa da
macizai da kunamun wuta zasu rika
fitowa suna saran sa da cizon sa,
yana konewa har a tashi kiyama,
idan kuwa aka taso shi daga kabari
to mutane zasu cutu daga warinsa,
sai a gane shi da wannan a kuma
gane me yake yi a duniya, har sai a
yi umarni da shi zuwa wuta.
(Ma'arijun yakin fi Usuluddin: Sheikh
Sabzawari, s; 408).
An karbo daga sayyidi Ali (a.s)
ya ce: Mai tsira da aminci yana
cewa: "Na hana ku zina, domin a
cikinsa akwai abubuwa shida, uku a
duniya, uku a lahira: Amma na
duniya su ne: Tana tafiyar da
kwarjini, Tana yanke arziki daga
sama, Kuma tana gaggauta karewa.
Amma na lahira su ne: Mummunan
hisabi, Da fushin Allah, Da kuma
dawwama a wuta. (Ma'arijun yakin fi
Usuluddin: Sheikh Sabzawari, s;
408).
Jikin Mutum
Bayanan da muka kawo na
maganganu masu daraja na Imam
Sajjad (a.s) sun bayar da
muhimmanci an gabobin da aka
kawo a baya da s**a hada da:
harshe, ji, gani, hannu, kafa, ciki,
farji. Wadannan gabobi masu hadari
kuma masu kima da daraja suna
matsayin hanyoyin da rai take
amfani da su domin samun daraja da
daukaka, ko kuma samun kaskanci
da wulakanci, don haka ne bahasi
kansu yake da matukar muhimmaci.
Sai dai a nan zamu kawo bayanai
game da su ta fuskancin jiki gaba
daya ne.
Muna ganin muhimmancin
gabobin jikin dan Adam ta yadda
s**a kasance kofar da za a bi domin
tarbiyyar ransa, imam Zainul-abidin
(a.s) ya nuna mana wannan domin fu
fadaka game da wadanna bangarori
na jiki, mu san kirmarsu da
muhimmancinsu, da kasancewar
gyaran kawuka ya doru a kan kiyaye
su.
Jikin mutum yana da
abubuwan da yake bukata na
rayuwa domin ci gaba da samuwa,
wadannan abubuwan idan babu su to
karshensa ya zo ke nan. Yana
bukatar abubuwa biyu na ciki da na
waje, da kuma wani abu na uku da
ya shafi rayuwarsa a matsayinsa na
dan Adam.
Na ciki sun hada da ci, da sha,
da magani domin waraka daga
cututtuka, sai kuma abin da jiki yake
furzarwa wadanda suke fita daga
gareshi domin samun sauki k**ar
kashi, da bawali, da amai, da mani,
ko wadi da mazi, da gumi ko zufa, da
hawaye, da majina, da daudar kunne,
da yawun baki.
Na waje kuwa sun hada da
wanke dauda, da sanya tufafi k**ar
riga da wando, da takalmi da hula, da
sanya abu mai kanshi k**ar turare,
da kayan ado k**ar sarka da dan
kunne, da awarwaro, da mai domin
shafawa, da mai domin gyaran
gashi, da jan farce. Kamar yadda
yake bukatar wurin zama da inda zai
samu rayuwa mai kyau da
shakatawa, sannan ya samu wani
abu da zai rage masa wahalar cirata
daga wuri zuwa wani wurin k**ar
mota ko babur.
Amma a bangare na uku yana
bukatar wasu abubuwa da s**a
shafi zaman tare na al’umma, da
hukumar da yake karkashinta, idan
mun duba irin wadannan abubuwan
zamu ga suna cikin bayanai k**ar
haka:
Mutum yana bukatar wasu
abubuwan saukaka rayuwa da
yalwarta k**ar wutar lantarki da
ruwan famfo, da t**i mai kyau, da
amincin gari ta yadda babu wani
wanda zai zo domin satar kayansa,
ko dukansa ko kisansa, kuma yana
bukatar kare duk wani abu da ya
shafi jininsa, ko mutuncinsa, ko
dukiyarsa. Amma sama da hakan
akwai ‘yancin fadin ra’ayi da kare
hakkinsa domin kada wani ya takura
masa a wannan fage mai
muhimmanci. Fadin ra’ayi yana
k**a da amai ko atisshawa ne da
idan ba su fito ba to suna kumewa a
cikin jiki, haka nan ra’ayi yakan
zama ya kume a cikin tunani sai ya
kasance wani bakin ciki da yake
taruwa a cikin zuciya.
Akwai wani abu da yake
bukatarsa wanda ya fi kowanne
muhimmanci wanda shi ne akidarsa,
kowane mutum yana bukatar inda
zai rayu da imani da akidarsa, yana
kare akidarsa da hujjojinsa na
shari’a ko na hankali.
Idan mun duba sai mu ga
kowane bangare sai da shari’a ta ba
shi matsayi na musamman domin
k**alar mutum. Don haka ne a nan
zamu yi nuni da wasu daga ciki a
dunkule, mai son duba bayanai
masu fadi sai ya koma wa littattafan
shari’a.
Idan mun duba bukatun jiki na
ciki sai mu ga shari’a ta
muhimmantar da su ta yadda ta hana
ci ko shan wani abu da yake
cutarwa ko lahantawa, da yawa
ayoyin da s**a yi bayani kan haka a
cikin littafi mai tsarki na Kur’ani,
wasu ayoyin sun yi nuni da cewa: “…
kuma ba a sanya muku kunci a cikin
addini ba...” [1] , wasu kuwa sun yi
nuni da cewa: “... kuma yana
haramta musu mai muni -
cutarwa- ...” [2] . A nan muna iya
cewa hatta da abu mai sanya maye
da aka haramta a shari’a yana
komawa ga cutuwar mutum a
hankalinsa ko jikinsa ne.
Sai shari’a ta haramta dukkan
mai sanya maye da mai cutarwa
domin ta kare tarbiyyar mutum ta jiki
da ta rayinsa, da gujewa sanya
masa kunci a cikin rayuwarsa, da
kaucewa ransa ko jikinsa daga
fadawa cikin wahala da halaka.
Dogaro da wannan maslahar
ne shari’a ta sanya wajabcin yin
magani ga wanda ba shi da lafiya
domin ba ta halatta masa cutar da
kansa ko wata gaba ta jikinsa ba,
don haka ne ta hana sayar da wani
bangare na jikinsa wanda zai kai shi
ga cutar da ransa ko jikin, sai dai
idan babu cutuwa a ciki k**ar sayar
da wani bangare na jininsa.
Sannan hikimar Allah ta sanya
masa wasu dokokin da zai samu
sauki a cikin jikinsa k**ar furzar da
majina ko miyau, ko amai, ko kuma
fitar da dauda da dattin da ya taru a
cikin jikinsa ta hanyar bawali da
bayan gida, ko kuma fitar da maikon
da yana iya daskarewa ta hanyar
gumi da zufa. Da ba a sanya masa
hanyoyin da zai samu sauki ba da
ya halaka, da rayuwarsa ta kare,
amma sai ya kasance an ba shi
hanyoyin sararawa.
Sannan aka sanya masa
hanyar sanyaya ransa da zuciyarsa
ta hanyar yin kuka abin da yake
ni’ima ce babba ga bayi da Allah ya
yi musu. Kuma iyakacin bala’in da
ya fada wa mutum da nauyinsa a
kan zuciya ne ransa take bukatar
fesar da shi ta hanyar yin kuka
domin samun lumfasawa.
Ruwaya ta zo cewa: “Masu
kuka mutum biyar ne...” [3] . Kuka
wani abu ne da ake son yin sa
domin wasu abubuwa da s**a hada
da tsoron Allah ga wanda ya tuna
zunubansa, ko yayin wata musiba
k**ar mutuwa. Wasu mutane sun
so hana kuka yayin mutuwa, sai dai
wannan ya taso daga rashin fahimtar
maganar manzon Allah ne da wani
sahabi ya yi, sai Ai’sha matar Annabi
(s.a.w) ta gyara masa cewa ba haka
ake nufi ba, sai dai abin da aka hana
a kukan mutuwa shi ne fadin abin da
ya saba wa shari’a.
Wata hanyar samun lafiya da
Allah ya sanya wa bayinsa ita ce
hanyar fitar wasu abubuwa da
shari’a ta sanya wanka saboda
fitarsu, wadannan abubuwan sun
hada da mani, da jinin haila da na
haihuwa, da na istihala idan yana da
yawa sosai. Akwai kuma wasu ruwa
masu fita daga mutum da ba a
sanya komai a kansa ba don sun
fita, wadannan su ne mazi da wadi,
kuma shari’a a bisa mahangar
Ahlul-baiti (a.s) ta yi musu hukunci
da tsarki.
Wasu kuwa an sanya yin tsarki
ne saboda fitarsu wadannan
abubuwan sun hada da bawali da
gayadi, wadannan idan sun fita sai
mutum ya yi tsarkinsu. Akwai kuma
wasu halaye su ma da ake son
wanda ya yi su ya yi alwala,
wadannan abubuwan sun hada da
yin bacci ko suma.
Amma abubuwan da suke daga
wajen jiki sun hada da tsarkin
daudar jiki, shari’a ta sanya
tsarkake jiki daga dauda domin kada
ya yi wari ya cutar da kansa da
mutane. Wata ruwaya tana cewa da
mu: “An gina addini a kan tsafta
ne” [4] , wata kuwa tana cewa:
“Tsafta tana daga imani ce” [5] .
Kazamin mutum ba ya samun kima
da daraja a cikin mutane, mutane
suna wulakanta wanda s**a gani
cikin kazanta komai kimarsa.
Akwai kuma kayan sawa da
s**a hada da riga da wando, da
takalmi, da hula, da turare, da gashin
mata, da sauran kayan ado k**ar
sarka da awarwaro da dan kunne, ko
jan farce da sauransu. Shari’a
dukkaninsu ba ta hana su ba, sai dai
a tufafin mace ta wajabta mata rufe
dukkan jikinta in banda fuska da
tafuka.
Wadannan tufafin kowace
al’umma tana da nata yanayin shiga,
kuma dukkan shigar al’umma ba ta
da wata matsala a shari’a matukar
dai ba ta saba wa waccen doka da
aka sanya wa mace ba. Al’adun
Hausa mace tana iya sanya atamfa
da dan kwali da zane, da mayafi, sai
ta rufe duk jikinta da wannan, tana
iya sanya wando ko ta hada zane da
wando.
Muna iya ganin a wasu
al’ummun namiji ne yake daura zane
mace kuma wando, wannan yana
nuna mana kowace al’umma tana da
nata yanayin shiga, kuma babu wata
shiga da musulunci ya hana sai dai
kawai ga mace idan zai kai ga
bayyanar da jikinta da ya hana.
Wasu jama’un namiji yakan iya
sanya gajeren wando da ‘yar riga,
mace kuwa ta sanya siket da riga.
Musulunci bai hana su wannan shiga
ba, sai dai mace idan zata yi siket
ya ja har kasa ta yadda zai rufe
dukkan kaurinta har kafarta babu
wani haramci a kan hakan, kanta
kuwa da jikinta ta sanya riga zuwa
karshen hannunta, ta sanya kuma
abin da zai rufe kanta.
Muhimmi a cikin tufafi shi ne
kiyaye wancan ma’anuni da
musulunci ya sanya, idan aka kiyaye
wannan babu wani tufafin wata
al’umma da ya fi na wata. Babu
bambanci, babban tufafi da karami
duka daya suke, babu bambanci
tsakanin babbar riga da kot da
wando a wurin shari’a wannan duk
yana komawa ga tunanin al’adun
mutane ne.
Muna iya ganin yadda hula
take da muhimmanci a wata
al’umma, a wasu al’ummu girman
mutum yana kan hularsa ne, da zai
je taro babu hula to da kimarsa ta
fadi ke nan. Amma a wasu al’ummu
hula ba ta da wata kima ta a zo a
gani, wasu suna ganin cewa sanya
hula da dare yana haifar da matsala
a ganin mutum, wasu sun tabbatar
da matsalar yawan rufe gashi
kodayaushe.
Amma wasu al’ummu idan ba
su sanya hula ba suna ganin k**ar
ba su kammala ba, kana iya ganin
mutum yana rufe kansa da zafin
rana, kansa yana ta yi masa kaikayi
amma ba zai cire hular ba, mafi muni
shi ne likita yana iya hana shi sanya
hula amma don kada al’umma ta gan
shi karamin mutum sai ya sanya,
haka nan al’adu suke cutar da
al’ummu daban-daban.
Musulunci yana son tufafi ne
na takawa, don haka kowace irin
shiga al’umma take da shi ba shi da
muhimmanci a wurinsa, abu
muhimmi a nazarinsa shi ne takawar
mutum, mutumin da yake sanya
gajeren wando da karamar riga yana
mai jin tsoron Allah da kiyaye
dokokinsa shi ne abin so wurin Allah,
amma mutumin da ya sanya rawani
da alkyabba, ga babbar riga da mota
mai tsada ba shi da wata kima wurin
Allah sai idan shi ma yana da
takawa.
Wannan ne ya sanya ma’aunin
Allah da yake kallon bayinsa da shi
ya saba da ma’aunin da mutane
suke kallo da shi. Ma'aunin Allah ya
doru bisa ganin dukkan halittarsa a
daidai a cikin al'adunsu matukar ba
su saba wa dokokinsa, amma
ts**akken tunanin mutane yana
girmama dan Adam ta cikin al'adu
da abin duniya ne.
Idan muka waiwayi kayan
adon mata haka nan babu wani ado
da musulunci ya hana mace kowane
iri ne, sai dai bai halatta ta bayyanar
da adonta ga wasu mazaje ba sai
dai ga mata ko mutane da suke
muharramai k**ar 'yan'uwanta,
babu wani dan kunne ko sarka, ko
man shafawa, ko karin gashi, ko rina
gashi, ko jagira, ko jan farce, da
sauran kayan ado da addini ya hana
mace.
Sai dai namiji yana da
dabaibayi da shari'a ta yi masa na
cewa bai halatta ya sanya zenare ko
azurfa ba, ko alhariri, don haka
mace tana iya sanya zinare amma
namiji bai halatta ya sanya shi ba.
Zai iya yiwu wata al'ummar ya
kasance namiji yana yin kitso ko ya
sanya dan kunne da sarka ko
awarwaro don adon namiji, shi ma a
nan musulunci ya hana namiji sanya
sarkar zinare, wannan haramcin na
zinare ga namiji ba shi da bambanci
a cikin al'ummu.
Game da wurin zaman rayuwa
k**ar gida, ko kuma wani abin
hawa k**ar mota, babu wani wanda
Allah ya yi wa haramcinsa k**ar
namiji ko mace, a irin wannan
abubuwan shari'a ba ta hana komai
ba sai idan na haram ne. Idan gida
ya kasance na kwace, ko filin
kwace, to sai shari'a ta haramta
zama da yin salla a cikinsa, k**ar
yadda ta haramta hawa motar sata
ko ta kwace.
Wasu masu daskararren
tunani game da musulunci sai s**a
hana mace tuka mota bisa jahilci,
irin wannan jahilci ana yin sa a wasu
kasase abin takaici da sunan
musulunci. Kamar yadda zamu ga
wasu kasashen ko kungiyoyi, ko ma
wasu masu bayar da fatawa bisa
ts**akken tunaninsu sun takaita
kaya da irin na al'adarsu suna masu
daukar cewa shi kadai ne na
musulunci.
Amma a bangare na uku
mutum yana bukatar wasu
abubuwan saukaka rayuwa da
yalwarta da ya hau kan hukumar da
yake rayuwa karkashinta ta samar
masa da su, irin wadannan
abubuwan sun hada da wutar
lantarki da ruwan famfo, da t**i mai
kyau, da amincin gari ta yadda babu
wani wanda zai zo domin satar
kayansa, ko dukansa ko kisansa.
Aminci wani abu ne mai
matukar muhimmanci a rayuwar dan
Adam, idan babu shi to al’umma ba
ta samun sukunin ci gaba. Don haka
yana bukatar mai kare masa jininsa,
da mutuncinsa, ko dukiyarsa. Kamar
yadda yake matukar bukatar wanda
zai kare masa ‘yancin fadin
ra’ayinsa, da kare hakkinsa domin
kada wani ya takura masa a wannan
fage mai muhimmanci.
Sannan akwai wani abu da
yake bukatarsa wanda ya fi
kowanne muhimmanci wato ‘yancin
akida, kowane mutum yana bukatar
inda zai rayu da imani da akidarsa,
yana kare akidarsa da hujjojinsa na
shari’a ko na hankali. Kuma wannan
akida wani abu ne da ya kafu a
ransa, ya yi rassa a gabobinsa, don
haka ne ba a tilasta mutum ya bar
akidarsa, idan ana son gamsar da
shi cewa akidarsa batacciya ce, to
ya zama ta hanyar hankali ko hujjar
shari'a.
[email protected]

Address

MAIDUGURI Road P. O BOX 257
Satabawa

Telephone

07065358595

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Yobe Islamic Center posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Place Of Worship

Send a message to Yobe Islamic Center:

Shortcuts

Share

Category