JIBWIS Mararaba Gurku

JIBWIS Mararaba Gurku The Islamic Organization For Eradicating Innovations and Establishing Sunnah. Ibrahim Na Alh. Hudu Chikaji.
(2)

Jama’atu Izatil Bid’ah Wa Iqamatus Sunnah (Jibwis)

Kungiyar kawar da Bidi’ah da tsayar da sunna

Wannan qungiya ta al’ummar musulmi an kafa ta ne tun a shekarar 1978 a Najeriya, kuma shugabanta na farko shi ne Alhai Musa Gandu Muhammad, a qarqashin kulawar Malam Abubakar Mahmud Gumi, tare da Sheikh Isma’il Idris bn Zakariyya, a matsayin shugaban majalisar malamai na farko na kungiyar. Qungiyar it

a ce irinta ta farko a tarihin yada addinin musulunci a Najeriya, hadi da harkar ilmantarwa, tare da daukaka darajar harkokin addinin Musulunci ba tare da wani tsoro ba. Don haka ne sai kungiyar ta sanya wasu ginshiqan manufofi da take so ta cimma domin kai wa ga gaci. Daga cikin muhimman manufofin wannan kungiya sun hada da:

- Kawar da duhun jahilci daga cikin al’umma, wanda ya yi wa al’umma katutu.

- Hada kan al’ummar musulmi a bisa koyarwar Alqur’ani da Sunnar Manzon Allah (SAW),

- Wayar da kan al’ummar musulmi game da al’amuran addini, domin a gudu tare a tsira tare.

- Fadakar da al’ummar musulmi domin a yi watsi da wasu miyagun littattafai da suke tura mutane cikin halaka.

- Tabbatarwa da cewa Annabi (SAW) ya kammala isar da sakon Allah (SWT).

- Duk wanda ya yi da’awar annabta, ko kuma yake riya cewa Annabi (SAW) yana ziyartarsa da wani sako, to wannan zunzurutun makaryaci ne.

- Yada Musulunci a Najeriya da wajen Najeriya.

- Yin da’awa a kan fadin Manzon Allah (SAW) cewa: “duk wanda ya ga abin qi, to ya sauya shi da hannunsa, idan ba zai iya ba, to da harshensa, in ba zai iya ba, to da zuciyarsa, amma wannan shi ne mafi raunin imani.”

- Kar a boye hujja in dai har ta tabbata daga littafin Allah Madaukakin Sarki, ko sunnar Manzon Allah (SAW). Wasu daga cikin ayyukan kungiyar sun hada da:

Kasancewar wannan kungiya ta shahara sosai a kasashe daban-daban na duniya, wannan ya sa aka samar da kwamitoci daban-daban domin gabatar da ayyuka da yawa. Wasu daga cikin kwamitocin kungiyar sun hada da:

- Kwamitin Da’awah.

- Kwamitin Tarurrukan Wa’azi.

- Kwamitin Kula da Marayu

- Kwamitin Ilimi.

- Kwamitin Mutane Goma.

- Kwamitin Taimakon Gaggawa. KWAMITIN ZARTASWA

Shugabanta na kasa a wannan lokaci shi ne Sheikh Abdullahi Bala Lau, khalifa na farko a sashin shugabancin wannan kungiya tun bayan kafa kungiyar, wanda tsohon mataimakin shugaban kungiyar ne a zamanin shugabancin marigayi Alh. Musa maigandu Muhammad, kuma ya gaje shugabancin kungiyar ne bayan rasuwarsa.

- Alh. Azare: Mataimakin Shugaban Kungiya Na Kasa.

- Sheikh Muhammad Kabir Haruna Gombe: Babban Magatakardan kungiya

- Sheik Sani Yaya Jingir: Shugaban Majalisar Malamai na kasa

- Sheik Yusuf Sambo Rigachuku: Mataimakin Majalisar Malamai na Kasa

- Alh. Isa Waziri: Shugaban Yan Agaji na Kasa

- Engr Mustapha Imam Sifti: Mataimakin Shugaban Rundunar Yan Aagaji na kasa

kungiyar ta samu karbuwa a sassa daban-daban na duniya. A Najeriya tana da rassa a dukkanin jihohin Najeriya 36 da birnin tarayya. Haka kuma saboda irin yadda kungiyar take kokarin ilmantar da al’umma, wannan ya sa har ta sami kutsawa zuwa ga wasu kasashe, kamar su; Nijar da Mali da Sinigal da Togo da Kamaru da Cadi da Burkina da Gini, Saudi Arabia da sauransu. Wasu daga cikin abubuwan da kungiyar ta mayar da hankali wajen yin su, sun hada da:

- Koyarwa a bisa tafarkin Manzon Allah (SAW) ba tare da bin son zuciya ko kuma yin makauniyar biyayya ga wani ba.

- Tsantsar karantar da hakikanin ilimin addinin Musulunci.

- Gabatar da wa’azin kasa a duk makwanni biyu ko uku ko hudu don tunatar da mutane abin da suka manta ko kuma lokutan da suka dace.

- Kafa makarantu domin koyar da ilimin addini da na boko, da sauran fannonin ilimi.

- Kai ziyarori gidajen marayu da gidajen yari da asibitoci, domin tallafar musulmai marasa galihu.

- Samar da taimakon gaggawa a duk lokacin da bukatar hakan ta taso. kungiyar ta samar da hamshaqan malamai a sassa wadanda suka sami daukaka ta ilimi a fadin duniya baki daya, saboda jajircewa da kokarin bin tafarkin Manzon tsira, Annabi Muhammad (SAW), sau da kafa. Haka kuma ta ko wacce fuska tarihin izala zaizo , dogo ko gajere, ba za a taba mantawa da irin gudummar da marigayi Sheikh Isma'ila Idris Bin Zakariyya ya bada ba, da irinsu Marigayi Ibrahim Bawa Maishinkafa da Mal. Koda ba manufarmu zayyana sunan kowa ba, amma muna addu'a ga dukkan wadanda suka sadaukar da dukiyoyin su da kuma rayukansu akan wannan harka taci gaban addini, Allah ya saka musu da gidan Aljanna ya hada mu dasu a babban matsayi a lahira. Wannan kadan ne daga cikin irin manufofin da kungiyar Izala ta kafu a kayi, kuma a haka za'a tafi da ikon Allah. Daga Karshe Muna Addu'an Allah ya nuna mana gaskiya gaskiya ce ya bamu ikon binta, ya nuna mana karya karya ce ya bamu ikon guje mata.

As salamu alaykum Warahmatul lahi Wabarakatuhu.*SA'KON GAISUWAR SALLAH*Kungiyar Jama'atu Izalatil Bidi'a, Wa Iqamatis Su...
29/05/2026

As salamu alaykum Warahmatul lahi Wabarakatuhu.

*SA'KON GAISUWAR SALLAH*

Kungiyar Jama'atu Izalatil Bidi'a, Wa Iqamatis Sunnah Garin Mararabar Gurku Karamar Hukumar Karu Jahar Nasarawa.

Karkashin Jagorancin Sheikh Abdul Aziz Usman Gusau.

Tana Taya Membobin ta Da Dukkan Sauran Al Ummar Musulmi Murna Tare da Yi Masu Gaisuwar Barka Da Sallah.

Muna Rokon Allah Ta'ala Ya Karbi Ibadunmu Baki Daya Ya Gafarta Mana Kurakuran mu.

Ameen Ya Hayyu Ya Qayyum.

Usman Ibrahim Nadabo Kankara
Chairman Social Media Jibwis Mararabar Gurku. Amadadin Jibwis Mararabar Gurku.

Assalamu Alaikum,JAMAA'ATU IZALATIL BID'AH WA'IQAMATIS-SUNNAH MARARRABA BRANCH, KARU L.G.A.Ga Jadawalin Wa'azi Sati Biyu...
07/04/2026

Assalamu Alaikum,
JAMAA'ATU IZALATIL BID'AH WA'IQAMATIS-SUNNAH MARARRABA BRANCH, KARU L.G.A.

Ga Jadawalin Wa'azi Sati Biyu - Biyu DA Sauran Ayyukan Kwamitin Da'awa na shekaran 1447AH/1448AH (2026M/2027M) karkashin JIBWIS Mararaba Gurku, Karu LGA, Nasarawa State.

Sanarwa Daga Ofishin Sakataren Kwamitin Da'awa; Muhammad Nura Abu Fatima
Ta Hannun;
Sakataren Kwamitin Yaɗa Labarai(Social Media); Safwan Muhammad Musa

16/03/2026

LOKUTTA DA WURARAN SALLOLIN IDI, KARAMA A GARIN MARARABAR GURKU KARU LG NASARAWA STATE.

Shugaban Kungiyar Malam Abdul aziz Usman Gusau.

Shugaban Majalisar Malamai Malam Yusuf Idris Farin Ruwa.

Shugaban Agaji Na Riko Malam Harun Gombe.

Amadadin Kungiyar Izala Reshen Mararabar Gurku.

Ke Sanar Da Al Ummar Musulmai Lokuttan Sallar Idi Karama Kamar Haka.

1- Uthman Bin Affan (A) Unguwar Katsinawa

Lokaci 8:30am

Limami Malam Kabir Shuaibu Jaji.

2- Filin Idi Umar Bin Khaddab Rugar Juli.

Lokaci 8:30am

Limami Malam Husain Musa Abubakar

3- Awwaliyya Gidan Kaji Sabon Gari.

Lokaci 8:00am

Limami Malam Ilyasu Abubakar

4- Utman Bin Affan (B) Rugar Madaki.

Lokaci 8:00am

Limami Malam Mukhtar

5- Bayan Dutse

Lokaci 8:00

Limami Malam Auwal Ibeto.

6- Asma Filling Station Abacha Road

Lokaci 8:00am

Limami Malam Sanusi Ibrahim Daura

7- Abara Foundation (Royal Estate) Abacha Road

Lokaci 8:00

Limami Malam Aliyu Adam Bauchi

8- Masjid Istiqama

Lokaci 8:00

Limami Malam Musbahu Nasir P**i.

Allah Taala Ya Kaimu Ranar Ya Kuma Karbi Ibadun mu

Was salamu alaykum.

Sanarwa Daga Shugaban Komitin Social Media. Usman Ibrahim Nadabo Kankara Amadadin Shugaban Kungiya

01/03/2026

Innalillahi Wa Inna Ilaihir Rajiun.

Cikin Alhini da Jimami Shugaban Jibiwis Mararabar Gurku. Malam Abdul aziz Usman Gusau

Yake Umarta Na Da In Sanar daku Rasuwar Tsohon Shugaban Jibiws Mararabar Gurku Alhaji Musa Daura

Jana'iza Masallacin Ung Katsinawa 4:00pm

Was salamu alaykum.

Usman Ibrahim Nadabo Chairman Jibwis Social Media Mararabar Gurku

23/02/2026
22/01/2026

Assalamu Alaikum Wa Rahmatullah.

SAKON TA'AZIYYA

Daga Jiwis Mararabar Gurku.

Karkashin Jagorancin Sheikh Abdul aziz Usman Gusau

Amadadin yanuwa baki daya ina gabatar da taaziyyarmu ga dukkan yanuwa na rashin babban Malaminmu shaikh Habib Yahaya Kaura.
Allah ya gafarta masa kurakuransa, ya karba masa kyawawan ayyukansa Yasa Jannatul Firdausi itace makoma gareshi.

Was salamu alaykum. Usman Ibrahim Nadabo Kankara Chaiman Jibwis Social Media Mararaba Gurku.

Amadadin Shugaban Kungiya

Address

Jum'at Masjid, Unguwar Katsinawa, Maraba Karu LGA
Nasarawa

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when JIBWIS Mararaba Gurku posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Place Of Worship

Send a message to JIBWIS Mararaba Gurku:

Share