16/04/2025
Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un.
Babban Limamin Masallacin Shaikh Aliyu Harazimi Zambiya, kuma Muqaddam na Darikar Sufi Tijjaniyya, Shaikh Tidiane O. Oghejjem, ya amsa kiran Allah a yau, a titin Nelson ivïde, a wani hatsarin mota a jamhuriyar Lusaka Jahar Zambia. kafin rasuwarsa, yana karantar da dalibansa a cikin gidansa a cikin Zawiya, da kuma cikin masallaci kafin sallar Asuba.
A da ba Musulmi ba ne, ya Musulunta a Amurka kimanin shekaru 15 da s**a gabata a hannun jikan Shaikh Ibrahim Niass R.T.A domin sun yi karatu tare, abokin karatunsa ne, kuma ya koyi ilimi da yawa a wajen Shaikha Maryam Niass R.T.A makarantar Sénégal kuma ya tafi kasar Morocco, ya koyi karatun addini da yawa Sannan Da litattafan Dariqa, kuma ya yi karatun boko da Qa’ahir, sannan ya yi karatun digiri na uku a jami'ar Ilorin.
Allah ya jikansa da rahama Ameen