26/11/2025
MASUSSUKA MAI WAYO
Tun da farko ya bayyana ne a matsayin mai rushe duk abinda ba Alkur'ani ba, tunda daga kan Hadisai, littatafan Fiqhu, Tauhidi da sauran su. Kuma dama duk yan akidar zallar Alkur'ani na gaske ba su yarda da komai ba sai Alkur'ani zallah. Wannan dalilin ya sa za ka ga ko ibadar su ta sha bamban da ta ma su aiki da Hadisai. Misali :
1- Su na yin sallah, amma ba da sigar irin sallar ma su hadisi ba. Wasu ma a cikin ba sa sallar.
2- Ba sa cin kifi har sai an yanka shi kamar yadda a ke yanka akuya ko kaza. Da sauran su. Don ba su yarda mataccen naman ruwa halal tunda babu ayar a cikin Alkur'ani.
MASUSSUKA KAN SA YA FARA YIWA RITAYA:
Bayan Masuss**a ya fahimci ba wanda zai fahimce shi a kan akidar aiki da Alkur'ani zallah. Sai ya fara neman wacce dabara zai yi don ya ribaci mutane. Ya sani serai cewa Ahlus-sunnah dai ba za su bar littatafan Tauhidi, Hadisi da sauran su ba. Su ma 'Yan darika ba za su bar Hadisi, Fiqhu, Diwani, Ishriniya, Maulidi da Wazifa ba.
To a nan ne ya lura da cewa ai 'yan darika su na da sa6ani da Ahlus-sunnah a kan wasu abubuwa musamman fassarar Nassi ko tabbatar da wasu hadisai.
Sai Masuss**a ya fara kusantar yan darika da kalamai na hikima da wayo. Misali :
1) Ai nima a baya dan cikin darika ne, ni dan gida ne.
2) Yanzu na yarda da Hadisai, amma ban da wanda su ka karyata aya, ko su ka taba Janibin Annabi ko su ka yi umarni da ta'addanci.
3) 'Yan Izala ba sa kyautawa wajen kafirta yan darika da su ke yi, bayan addinin Musulunci na Allah ne, ba na su ba.
To a nan, duk wani Dan darika wanda ba shi da zurfin tunani zai ga cewa Masuss**a ya na kokarin ba shi kariya ne daga yan izala/salafiyya/wahabiyya, kuma ya na caccakar su.
Nan take sai su ka manta da cewa a baya Masuss**a ya ci mutunci shehunan su, a baya Masuss**a ya ce "Inyass" mushe ne, Shehu Tijjani ma mushe ne, Allah ma bai ambace su cikin Alkur'ani ba. Sannan ya yi raddi na cin mutunci ga littatafan su kamar Jawahirul-Ma'ani da sauran su. Kuma har yanzu bidi