20/07/2026
SAƘON TAYA MURNA
Sheikh Dr. Abdullahi Bala Lau a madadin kungiyar JIBWIS, na miƙa saƙon taya murna ga shugaban ƙungiyar Izala na Jihar Neja, Alhaji Hassan Nuhu Mayanan Minna, bisa samun nasarar kammala karatun Digirin Digirgir (PhD) da ya samu a wannan mako.
Wannan gagarumar nasara abin alfahari ne ga al'umma baki ɗaya, kuma shaida ce ta jajircewa, himma, da sadaukarwa wajen neman ilimi da ci gaban al'umma.
Muna roƙon Allah Maɗaukakin Sarki Ya sanya wannan ilimi ya zama mai amfani gare shi, Ya ƙara masa hikima, lafiya, da tsawon rai, Ya ci gaba da amfani da shi wajen hidimtawa addinin Musulunci da ci gaban ƙasa baki ɗaya.
Muna taya ka murna, Dr. Alhaji Hassan Nuhu Mayanan Minna. Amin
Allah Ya ƙara ɗaukaka da albarka.
Jibwis Nigeria