24/08/2026
TALATA, 25 GA AGUSTA
NASSI: WAHAYIN YAHAYA 20:1-6
KAN MAGANA: MALAIKA ƊA MABUƊIN KULLE SHAIDAN
WAHAYIN YAHAYA 20:1-6
1: Sa'an nan na ga wani mala'ika yana saukowa daga Sama, yana a riƙe da mabuɗin mahallaka, da kuma wata babbar sarƙa a hannunsa.
2: Sai ya k**a macijin nan, wato, macijin nan na tun dā dā, wanda yake shi ne Ibilis, shi ne kuma Shaiɗan, ya ɗaure shi har shekara dubu,
3: ya jefa shi mahallakar, ya rufe, ya kuma yimƙe ta da hatimi, don kada ya ƙara yaudarar al'ummai, har dai shekarun nan dubu su ƙare. Bayan wannan lalle ne a sake shi zuwa ɗan lokaci kaɗan.
4: Sa'an nan na ga kursiyai, da waɗanda aka bai wa ikon hukunci, zaune a kai. Har wa yau, kuma na ga rayukan waɗanda aka fille wa kai saboda shaidar da s**a yi wa Yesu, da kuma Maganar Allah, ba su kuwa yi wa dabbar nan da siffarta sujada ba, ba su kuma yarda a yi musu alamarta a goshinsu ko a hannunsu ba, sun sāke rayuwa, sun yi mulki tare da Almasihu har shekara dubu.
5: Sauran matattu kuwa, ba su sāke rayuwa ba, sai bayan da shekaran nan dubu s**a cika. Wannan fa shi ne tashin matattu na farko.
6: Duk wanda yake da rabo a tashin nan na farko, mai albarka ne, tsattsarka ne. Mutuwa ta biyu ba ta da iko a kan irin waɗannan, amma za su zama firistocin Allah da na Almasihu, su kuma yi mulki tare da shi har shekara dubu.
MALAIKA ƊA MABUƊIN KULLE SHAIDAN
Abubuwan da s**a faru a nan sun biyo bayan nasarar da Almasihu ya yi a kan dukan makiyansa a yakin Armageddon.
Mala’ika mai iko ya sauko daga sama rike da mabudin da sarka a hannunsa domin ya daure Shaidan har shekara dubu, aya 1&2.
Mala’iku manzannin Allah ne don isar da sakonsa ga kowacce halitta, hukunci ko lada. Anan, saƙon shine a daure Shaidan kuma a jefa shi cikin rami marar matuka, a rufe shi, a sa hatimi a kansa. Ta haka zai rasa ikon rudin al’ummai na duniya na tsawon shekara dubu da Yesu zai yi sarauta a cikinsu.
Wannan shine lokacin da aka baiwa Masu Bi ikon yin hukunci da mulkin duniya tare da Almasihu, duba 1 Korintiyawa 6:2&3; Luka 19:17&19. Wadanda s**a fito daga cikin tsananin za a sāke ba su rai, kuma za su yi mulki tare da Almasihu, aya 4.
TAMBAYA:
Menene zai iya sa kowa ya rasa farin cikin nasarar da Almasihu yayi a kan Shaidan daga karshe?
ADDU’A:
Ubangiji Yesu, a tafiya ta ta mahajjaci, bari koyaushe in kiyaye a zuciyata gaskiyar cewa Yesu ne kadai ke da cikakken iko bisa Shaidan da aljanu, cikin sunan Yesu. Amin.
Abincin Yini - 2026