Islamic Youth Organization Akko

Islamic Youth Organization Akko Da'awa

Ina Mai Farin Cikin Gayyatar Yan'uwa Da Abokan Arziki Zuwa Daurin Auren Chairman Islamic Youth Organization Akko  Abdull...
29/09/2024

Ina Mai Farin Cikin Gayyatar Yan'uwa Da Abokan Arziki Zuwa Daurin Auren Chairman Islamic Youth Organization Akko Abdullahi J Kumo Wanda Za'ayi Ranar Asabar Mai Zuwa

Rana: Asabar 5/10/2024
Lokaci: 10:00am Na Safe
Wuri: Masallacin Juma'a na Izala Na. 1 Dake Hanyar Kalshingi Kumo.

Wanda Baza Su Samu Daman Halarta Ba Da Wanda Suke Nesa Muna Bukatar Addu'ar Ku.

Insha Allahu Gobe Za'a Fita Rokon Ruwa A Cikin Garin Kumo Idan Ba'asamu Ruwa ba Yau Da dareIdin Tike Karfe 8:00 Am Nasaf...
16/09/2024

Insha Allahu Gobe Za'a Fita Rokon Ruwa A Cikin Garin Kumo Idan Ba'asamu Ruwa ba Yau Da dare

Idin Tike Karfe 8:00 Am Nasafe

Dr Lawan 8:00 Am

Ya Allah Kabamu Ruwa mai yawa mai Albarka.

Islamic Youth Organization Akko Amadadin Chairman Nata Abullahi J Kumo  Na Akko Local Government muna mika sakon Godiya ...
01/11/2023

Islamic Youth Organization Akko

Amadadin Chairman Nata Abullahi J Kumo Na Akko Local Government muna mika sakon Godiya Ga S A protocal Na Mai Girma Gwamnan Alh Yakubu (Sarkin Kasuwa) Bisa daukan nauyin gyaran borehole na cikin makabartan Kumo da sayan itace na tsawon shekara daya (1) tabbas wannan abun ayabane a daidai wannan lokacin da ruwa yake wahala a cikin makabartan Kumo .

Muna Addu'ar Allah Ubangiji Yasaka da Alherisa.Allah yakara irinsa dayawa.

13/02/2023

SANARWA!!!

Wannan Kungiya Ta Islamic Youth Organization Akko Chapter, Ta Rushe Dukkan Mukamai, Daga Kan Amir Har Zuwa Kasa.
An Zabi Mal. Huzaifa Ahmad Kumo A Matsayin Acting Chairman Na Shura Committee.

Muna Rokon Allah Ya Sa Hakan Ya Zamo Alkhairi Da Sanadiyyar Cigaban Kungiyar.

INNA LILLAHI WA INNA ILAIHIN RAJIUN. Amadadin Islamic Youth Organization Akko muna mika taziyyarmu ga jama'ar Garin Kemb...
19/08/2022

INNA LILLAHI WA INNA ILAIHIN RAJIUN.
Amadadin Islamic Youth Organization Akko muna mika taziyyarmu ga jama'ar Garin Kembu dake kumo Gabar a karaman hukumar Akko bisa rasuwan Imam nasu malam Yaya Kembu lokacin da Muka kaiziyara garin Kembu wannan bawan Allah yabada gudumawa sosai wa addinin musullunci da wannan kugiyar ta Islamic Youth organization Akko .
Allah kajikan da rahama.

Alhamdullahi ana cigaban da kai Itace fisabilillahi magabartan cikin garin kumo. Allah ubangiji ya sakawa duk wadda yaka...
19/08/2022

Alhamdullahi ana cigaban da kai Itace fisabilillahi magabartan cikin garin kumo.

Allah ubangiji ya sakawa duk wadda yakai da wadda aka sani da wadda ma ba'asansa ba

Alhamdullahi Anfara kai Taimako Itace magabarta.A halin Yanzu tareda Chairman(Amir) Na Islamic Youth Organization Akko A...
16/08/2022

Alhamdullahi Anfara kai Taimako Itace magabarta.
A halin Yanzu tareda Chairman(Amir) Na Islamic Youth Organization Akko Abdullahi J kumo muka kai Ziyaran gani da Ido magabartan cikin garin kumo Ida muka taras da wani bawan Allah mai Suna Usman Ahmed yakai mota daya na Itace Allah Yasaka da Alheri Bugu da Kari ana bukatar maganin fishi ciyawa donmin fishe Inda ake bune gawawaki a halin yanzu yakai Dan 'Uwa Kayi iya kokarinka wajen wannan aikina Alheri.
Sin by.
Islamic Youth Organization Akko

08/07/2022

Insha Allah Za'a Tsada Sallah Idin Layyan Bana kamar haka A cikin garin kumo
Idin Tudun Hatsi 8:30 am
Idin Dr Lawan 8:30 am
Idin Akkoyel 9:00 am
Idin Kwata 9:00 am
Idan Allah Yakaimu

03/06/2022

Insha Allah Gobe Akwai Sallah Rokon Ruwa a cikin garin kumo

Masallacin idi na Tike 8:00am

Masallacin idi na kwata

Masallacin Idi na Akkoyel 9:00am

Masallacin Idi na kofar Dr Lawan Hayar Jauro tukur 8:00am

Yaa Allah ubangiji yabamu ruwa mai yawa mai albarka

Akin feshi Islamic youth organization akko kenan a magabartan cikin garin kumo. Allah bada lada
27/09/2021

Akin feshi Islamic youth organization akko kenan a magabartan cikin garin kumo.

Allah bada lada

06/05/2021



Duk da babu wani dalili na shari'ah da yace in daren Jumma'a ya dace da witiri a goman karshen ramadhana zai zama daren lailatul qadri, sai dai kasan cewar daren Jumma'a da wunin ta, sune mafi Alheri a cikin sata, wassu daga cikin Malamai s**a ce, anfi sammanin daren a irin wannan lokaci da falala s**a hadu, kamar yadda ibn Rajab Al-hanbali ya ruwaito, daga ibn hubairah, acikin littafin ibn rajab: Laďaiful Maarif shafi na: (203)

Shawari:
Kamar yadda muka faďa hikimin boyewa mutane asalin ranar shine don su kara dagewa, don kusan tan Allah ta'ala da raya wadan nan kwanakin gaba daya, irin wannar hikimar ne ta sa aka boye lokacin karbar addu'a ranar jumma'ah, haka ba'a faďi hakikanin sunaye 99 na Allah wanda in ka haddace su kasan ma'anan su kayi aiki dasu zaka shiga Aljannah, ruwayar Tirmithy da aka ambace su bata inganta ba, ba'a faďe su ba, sai dai in ka duba Alqur'ani da sunnah zaka samu sama da sunaye 99.
A takaice wannan damace garemu da mu kara dagewa.
Allah ya mana jagora baki daya ya datar damu.

04/05/2021



Daren ashirin da uku yana daya daga cikin dararen da ake tsammani mai karfi na lailatul qadri, yazo a hadithi ingantacce daga Abdullahi bn Unais R.A yace: Manzo S.A.W yace: (An sanar dani daren lailatul qadri, Sai aka kuma mantar dani yaushe ne, amma kuma an nuna mini a cikin bacci, cewa nayi sujjada cikin ruwa da tabo a asubahin washe garin daren, sai aka mana ruwan sama cikin daren 23 ga wata, bayan munyi sallar asuba sai muka ga ruwa da tabo suna diga daga goshi da hancin Manzo S.A.W).
Duba Muslim: (1168). da Ahmada: (16088), da Baihaqee: (8799).

Karin bayani:
Kamar yadda aka sani mafarkin Annabawa gaskiya ne, kuma gashi kamar yadda muka gani a hadithin nan, daman kuma rufin Masallacin a lokacin sa S.A.W anyi shine da kaba da kuma ganyen dibino, sabida haka in anyi ruwa yakan isa kasa, don haka mu dage a wannan dare, kamar yadda mukayi bayani daren na iya zuwa 21, ko 23, ko 25, ko 27 ko ma 29.

Kada a manta da yawan maimaita Allahumma innaka afuwun tuhibbul afwa fa'fu annaa.

Allah ya datar damu ya karba mana.

Address

Kumo

Telephone

+2348108567172

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Islamic Youth Organization Akko posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Place Of Worship

Send a message to Islamic Youth Organization Akko:

Share