26/03/2026
Yadda Mabiya Dariqar Qadiriyyah a Jahar Zamfara S**a S**a Gabatar da Taron Yinin Zikiri Wanda ake kira da (IKHWANUS SAFAH)
Taron Wanda Ya Gudana a Karkashin Jagorancin Babbar Cibiyar Dariqar Qadiriyyah ta Jahar Zamfara Dake Darul Qadiriyyah Kaura Namoda Bisa Jagorancin Shugaban Dariqar Qadiriyyah Na Jahar Zamfara Khalifa Sheikh Muhammadu Sani Sheikh Muhammadul Mahi Kambarawa
Dandazon Mabiya Dariqar Da Jagororinsu Muqaddamai, Malamai da Muridansu Tareda Matansu Ya'yansu Maza Da Mata Manya da Kanana Duka Sun Bar Gidajen Su Sun Tare a Daji Sunata Ambaton Allah da Manzonsa Cikin kowane Hali
Taron Wanda Suke Shafe Yini Bakidaya Tun Daga Karfe 10: 00 Na Safe Har Zuwa Karfe 6:00 Na Yamma Babu Abunda Sukeyi Ambaton Allah Da Manzonsa da Bayin Allah Salihai
Wannan Taron Yinin Zikiri Wanda Ake Kira da Taron IKHWANUS SAFAH Wata Sunnah ce Daga Cikin Ayyukkan Annabawa da Manyan Bayin Allah kamar su Annabi Dawuda Alaihi Salam da Babban Malamin nan Na Duniya Shehu Junaidul Baghdadi, Sarkin Waliyan Allah Bakidaya Shehu Abdulkadir Jelani (Q.S) Wanda Shine Ya Assasa Dariqar Qadiriyyah, Haka kuma Akwai Shehun Dariqar Qadiriyyah Na Afrika Maulana Amirul jaishi Sheikh Muhammad Nasiru Kabara (R.t.a) Duka Wadannan Jagororin Addini Sun Gabatar da Wannan Ibada
Wannan Suna Daga Cikin Dalilan Da S**a Sa Suma Mabiya Dariqar Qadiriyyah a Nan Jahar Zamfara Suke Cigaba da Raya Wannan Kyakyawar Ibada Domin Neman Yardar Allah
Allah Ubangiji Yabamu ladar Dake Cikin Wannan Babbar Ibada Da Muka Gabatar Alfarmar Shugaba Annabi Muhammadu Sallallahu Alaihi Wasallam.
Rubutawa
Mujtaba ridwan Al-Qadiry
Memba Qadiriyyah Social Media Team
26/03/2025