13/04/2025
YAN'MATA KUYI HATTARA!!!
SOYAYYA BA HAUKA BACE!!!
Budurwa takan bada kanta saboda tana son namiji, Amma Shi Namiji Yakan Keɓe da Mace Ne Kawai saboda biyan bukata.
Zina Soyayya ce ga budurwa amma Shauqi ne ga Saurayi.
Idan Budurwa tayi tsananin kamuwar Soyayya da Shauqi musamman ga Namijin da ya haɗa komai da mata suke bukata, to tana iya amince masa ko wani irin bukata.
Yana wuya kaga mace ta amince namiji ya taɓa koda hannunta ne b***e har akai ga saduwa.
Amma shi Namiji zai iya biyan buƙatan shi ga ƴa'mace koda baya Sonta, harma ya mata hidimomin rayuwa dan kawai ya Biya Bukatarsa da ita ba soyayya ba!
MATAKIN FARKO KE YAR'UWA!
Kada ki taɓa koda kuskure ne ya matso jikin ki,
Ko ya taɓa hannun ki,
Ko tufafin ki,
Ko hira a inda ba'a ganin ku,
Ko cire hijabi don yaga design na kayan ki koda shine ya ɗinka,
Ko buɗe hannu da kafafu don yaga design na nallen ki,
B***e har ki tube masa wando!
Wallahi idan kika kiyaye matakin farko, Bi'IznillAh zaki tantance samarin Kirki da na Shaho.
Samarin Shaho zai kirkiro hanyar da zaku rabu amma idan har samarin Kirki Ne - hakan ne zai kara samun natsuwa a gareki harma ya gaggauta yin auren ku don zai kasa jira ko tsoron kar wani yazo ya ƙasa shi!
Ya Rabbil'Alameen Ka Tsaremu Mu Dukka ...