Sheikh Yakubu Musa Hassan Katsina

  • Home
  • Sheikh Yakubu Musa Hassan Katsina

Sheikh Yakubu Musa Hassan Katsina Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Sheikh Yakubu Musa Hassan Katsina, Religious Center, .

Wannan shafi ne na Shugaban Kwamitin Amintattu na Kungiyar Jama'atu Izalatil Bidi'a Wa Ikamatis Sunnah ta tarayyar Najeriya kuma Daraktan Da'awah, Shugaban Kwamitin Tafsir na Kasa kuma Shugaban Kungiyar a Jihar Katsina Sheikh Yakubu Musa Hassan katsina

SAKO ZUWA GA ALHAZAI DA SAURAN AL’UMMAR MUSULMI BAKI DAYA “Ina taya dukkan Alhazai murnar samun damar tsayuwa a filin Ar...
26/05/2026

SAKO ZUWA GA ALHAZAI DA SAURAN AL’UMMAR MUSULMI BAKI DAYA

“Ina taya dukkan Alhazai murnar samun damar tsayuwa a filin Arfa, wuri mafi girma a cikin ibadun Hajji. Ina roƙon Allah maɗaukakin sarki ya karɓi ibadunsu, ya yafe zunubansu, ya dawo da su gida lafiya cikin rahama da gafara.

Ranar Arfa rana ce mai girma da falala. Rana ce ta yawaita azumi, addu’a, istigfari da ambaton Allah. Don haka ina kira ga sauran al’ummar musulmi da su ribaci wannan rana ta hanyar:

i. Yawaita istigfari da salati ga Annabi ﷺ

ii. Yin azumin ranar Arfa ga wanda ba Alhaji ba

iii. Yin addu’a domin samun zaman lafiya da ci gaban al’umma

iv. Nisantar sabo da ayyukan da ba su dace ba

Ina kuma kira ga al’ummar musulmi da su sanya ƙasarmu Nigeria cikin addu’a, domin Allah ya kawo mana zaman lafiya, ya kawo ƙarshen matsalolin tsaro da wahalhalun rayuwa, ya sanya albarka a cikin ƙasarmu da al’ummarmu baki ɗaya.

Mu ci gaba da kasancewa masu son juna, taimakon juna da kiyaye dokokin Allah domin samun rahama da nasara a duniya da lahira.

Allah ya sa mu dace da falalar wannan rana mai albarka, ya karɓi ibadunmu baki ɗaya.

Barka da Ranar Arfa.” - Sheikh (Dr.) Yakubu Musa Hassan Katsina (Sautus-Sunnah)

Address


Telephone

08036487324

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Sheikh Yakubu Musa Hassan Katsina posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

  • Want your place of worship to be the top-listed Place Of Worship?

Share