Markazu Khaleed Bn Waleed Litta'awun Wannasharul Islam Sheme.

Markazu Khaleed Bn Waleed Litta'awun Wannasharul Islam Sheme. Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Markazu Khaleed Bn Waleed Litta'awun Wannasharul Islam Sheme., No49 Sheme faskari local govm, Katsina.

GAYYATA GAYYATA GAYYATA
06/11/2024

GAYYATA GAYYATA GAYYATA

02/11/2024

Duk fa wanda ka ji yace wai malamai s**a tallata mana su kawai son zuciyansa ne yake fada
Da gaskene wasu daga cikin malamai sun tallatasu amma kaima abun yayi daidai da son zuciyarka ya sa ka zabesu idan ba hakaba ai akwai malaman da s**a nuna maku illolin zabensu a lokacin zaginsu kuke.
Son zuciya kawai ku daina zagin malamai idan zaku hankalta ku hankalta

Assalamu Alaikum warahmatullah yan'uwa masu Albarka don Allah wanda yake da pdf din wannan ya taimaka mani Ass,Prof Kabi...
24/10/2024

Assalamu Alaikum warahmatullah yan'uwa masu Albarka don Allah wanda yake da pdf din wannan ya taimaka mani
Ass,Prof Kabir Abubakar Kabir Asgar
Malam Abdurrahman Muhd Sani Umar
Sheikh Dr Muhammad Rabi'u Rijiyar Lemo
Sheikh Ibrahim Musa Faskari
Sheikh Umar Shehu Zaria

08035756874
A taimaka mani

Assalamu Alaikum ana sanar da daliban ilimi cewa sak**akon rashin tsaro da ke a hanyar gusau zuwa funtua  an dage karatu...
12/09/2024

Assalamu Alaikum
ana sanar da daliban ilimi cewa sak**akon rashin tsaro da ke a hanyar gusau zuwa funtua an dage karatun sahihu ibni kuzaima da za a yi a kano gobe juma'a,sai an sake saka wata rana nan gaba.

Ya Allah ka kawo mana karshen wannan masifa

Alhamdulillahi masha Allahu Malam Kabir Asgar Kabir Abubakar now officially Reader (Associate Professor) a harshen Larab...
29/08/2024

Alhamdulillahi masha Allahu Malam Kabir Asgar Kabir Abubakar now officially
Reader (Associate Professor) a harshen Larabci a Jami'ar Ahmadu Bello, Zariya.

Allaah Ya sa albarka, Ya ƙara ɗaukaka

‏‎لله بُحتُ بما في الروحِ من أَلَمٍما أجمل البَوْحَ للمولى وأحلاهُسيرفَعُ الحُزنَ عن قلبي ويمنَحُهُمِن البشائرِ ما يُنسي...
05/08/2024

‏‎لله بُحتُ بما في الروحِ من أَلَمٍ
ما أجمل البَوْحَ للمولى وأحلاهُ

سيرفَعُ الحُزنَ عن قلبي ويمنَحُهُ
مِن البشائرِ ما يُنسيهِ بلواهُ

وإن تأخّرَ ما أرجُوهُ من أمَلٍ
فلُطفُ ربي تجلّى حين أخفاهُ

سحائبُ اللُّطفِ في الحالَيْنِ تُمطِرُني
ما قدّرَ اللهُ مِن أمرٍ سأرضاهُ...

Gobene in sha Allahu Dr Ahmad musa filin samji katsina.
23/07/2024

Gobene in sha Allahu
Dr Ahmad musa filin samji katsina.

23/07/2024

قال قتادة :
من يتق الله يكن معه ومن يكن الله معه
فمعه الفئة التي لا تُغلب والحارس الذي لا ينام
والهادي الذي لايضل

Ga wanda bai san tushen rikicin ba to wannan shine tushen rikicin.Amma ko shedan ya haifi mutum zuciyarsa ba zata taba y...
22/07/2024

Ga wanda bai san tushen rikicin ba to wannan shine tushen rikicin.

Amma ko shedan ya haifi mutum zuciyarsa ba zata taba yarda a ce wai shehinmu ba yason Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare.

10/07/2024

ZANGA-ZANGA A MAHANGAR MUSULUNCI:

Tsohuwar ajiya

Rubutawa: Sheikh Dr. Ibrahim Jalo Jalingo (H)
Date: 09/09/ 2017

Zanga-zangar talakawa saboda neman tabbataccen wani hakki nasu, ko saboda neman tunkude wata barna da ke gudana a cikin kasa tabbas wani al'amari ne da ake gani yana faruwa daga lokaci zuwa lokaci cikin al'ummai daban-daban.

1. Babu sabani a tsakanin Malumanmu cewa: zanga-zangar hayaniya da kone-kone, da kuma zanga-zangar da za yi domin tabbatar da wani zalunci lalle irin wannan nau'i na zanga-zanga ba ya halatta a mahangar Musulunci.

2. Zanga-zangar lumana wacce aka tsara saboda neman wani tabbataccen hakki, ko neman tunkude wani tabbataccen zalunci daga shugabanni, ko daga wasunsu, lalle malamanmu na Musulunci a wannan zamani sun kasu kashi biyu game da hukuncin irin wannan zanga-zangar.

Kashi na farko s**a ce: Zanga-zangar talakawa ba ta halatta saboda abubuwa uku:-
1. Akwai k**anta kai da Kafirai cikin yin ta; saboda Kafirai ne aka san cewa suna daukar yin zanga-zanga a matsayin wata hanya ta neman kauda wani munkari; duk kuwa abin da Kafirai za su kebanta da shi, to ba halal ba ne Musulmai su rika yin shi.
2. Ita Zanga-zanga tana daga cikin fararrun al'amura a cikin Addini; duk kuwa abin da yake fararren lamari ne a cikin addini to lalle ba daidai ba ne a yi shi.
3. Dogara da Qa'idar "sadduz Zari'ah"; domin sau da dama yin zanga-zanga saboda neman kauda wani munkari ya kan sabbaba fadawa cikin munkarin da ya fi shi girma, wannan kuwa zai wajabta nisantar yin ta tun farkon fari.

Kashi na biyu kuwa s**a ce: Zanga-zangar lumana halal ce "babu wani laifi a yi amfani da ita saboda neman kauda wani munkari, ko tabbatar da wata ayyanannar maslaha; saboda hujjoji k**ar haka:-

1. S**a ce: zanga-zangar lumana wani abu ne da Salaf s**a yi amfani da shi domin kauda munkari; saboda Imam Abubakar Bin Al-Khallal ya ce cikin littafinsa mai suna Al-Amru Bil Ma'arufi Wan Nahyu anil Munkari shafi na 50:-
((عن محمد بن أبي حرب قال: سالت أبا عبد الله عن الرجل يسمع المنكر في دار بعض جيرانه. قال: يأمره. قلت: فان لم يقبل؟ قال: تجمع عليه الجيران وتهول عليه)).
Ma'ana ((Daga Muhammad Dan Abi Harb, ya ce: na tambayi Abu Abdullahi (watau Imam Ahmad Dan Hanbal) game da mutumin da yake jin munkari cikin gidan sashin makwabtansa. Sai ya ce: Zai umurce shi (da ya bari). Sai na ce: To in bai karba ba fa? Sai ya ce: sai a tara masa makwabta a tsoratar da shi)).

2. Har yanzu Imam Abubakar Bin Al-Khallal ya riwaito cikin cikin lattafin nasa a shafi na 50-51 ya ce:-
((عن جعفر بن محمد النسائي قال: سمعت أبا عبد الله سئل عن الرجل يمر بالقوم يغنون؟ قال: اذا ظهر له هم داخل. قلت: لكن يسمع الصوت يسمع في الطريق. قال: هذا ظهر عليه ان ينهاهم. ورأى ان ينكر الطبل يعني اذا سمع حسه. قيل: مررنا بقوم وقد اشرفوا من علية لهم وهم يغنون فجئنا الى صاحب الخبر فاخبرناه. فقال: لم تكلموا في الموضع الذي سمعتم؟ فقيل: لا. قال: كان يعجبني ان تكلموا لعل الناس كانوا يجتمعون وكانوا يشهرون)).
Ma'ana: ((Daga Ja'afar Dan Muhammad An-Nasaaii ya ce: Na ji Abu Abdillah an tambaye shi game da mutumin da ya wuce wasu mutane suna wake-wake? Sai ya ce: idan ya bayyana gare shi cewa suna cikin gida. Sai na ce: sai dai ana jin sauti ana ji a cikin hanya. Ya ce: wannan ya zama wajibi a kan shi ya hana su. Kuma ina ganin ya yi inkarin babbar ganga, watau idan s**a ji motsin shi. Sai aka ce: mun wuce wasu mutane suna kan wani bene nasu suna ta wake-wake, sai muka je wa jami'in hukuma wanda ake kai masa labarai aka ba shi labari. Sai ya ce: ba su yi magana cikin maudhu'in da kuka ji ba? Sai aka ce: a'a. Sai ya ce: ya kasance yana kayatar da ni su yi magana, watakila mutane za su kasance suna taruwa suna yayata lamarinsu)).
Kamar yadda kuke gani karara a cikin wadannan atharai biyu Imam Ahmad ya yi fatawar mutane su taru saboda inkarin munkari saboda a tsoratar da mai munkarin da kuma yayata lamarinsa.

3. Abul F***j Abdurrahman Ibnul Jauzii wanda ya rasu shekarar hijira 527 ya ba labarin wata zanga-zangar da Malaman Musulunci na Ahlus Sunnah s**a shirya saboda neman Mahukunta su kauda wani munkari da yake gudana; ya ce a cikin littafin tarihinsa mai suna: Al-Mutazim Fi Tarikhil Muluuki Wal Umam 8/240:-
((واجتمع في يوم الخميس رابع عشر المحرم خلق كثير من الحربية والنصرية وشارع دار الرقيق وباب البصرة والقلائين ونهر طابق بعد ان أغلقوا دكاكينهم وقصدوا دار الخلافة وبين ايديهم الدعاة والقراء وهم يلعنون اهل الكرخ، وازدحموا على باب الغربة وتكلموا من غير تحفظ في القول، فراسلهم الخليفة ببعض الخدم: اننا قد انكرنا ما انكرتم، وتقدمنا بان لا يقع معاودة، ونحن نغفل في هذا ما لا يقع به المراد. فانصرفوا وقبض على ابن الفاخر العلوي في آخرين، ووكل بهم في الديوان. وهرب صاحب الشرطة؛ لانه كان أجاز لأهل الكرخ ما فعلوا)).
Ma'ana: ((Mutane da yawa s**a hadu ranar alhamis sha hudu ga Muharram, daga Harbiyyah, da Nasriyyah, da Shari'u Darir Raqiq, da Babul Basrah, da Qalaawiin, da Nahru Tabiq bayan sun kukkulle kantuna sun nufi Fadar Khalifah, a gaba gare su akwai Masu wa'azi da Makaranta Alkur'ani suna ta tsine wa jama'ar Karkh, s**a yi cinkoso a kofar gurbah, s**a yi ta magana ba tare da wani rufa-rufa ba. Khalifah sai ya aiko wasu yaran Sarki zuwa gare su (da sakon): Lalle mu mun yi inkarin abin da kuka yi inkarin shi, kuma muna gabatar da (akawalin cewa) haka ba zai sake faruwa ba, kuma mu za mu tushe aukuwar dukkan abin da ba shi ne manufa ba. Sai s**a watse, kuma aka k**a Ibnul Faakhir Ba'alawe da ma wasu daban. Kuma aka jingina su cikin Diwani, sannan shugaban yan sanda ya gudu, saboda shi ne ya ba wa jama'ar Karkh izinin yin abin da s**a yi)).
Wannan zanga-zangar ta faru ne a shekarar hijira 458 watau yau shekaru 975 ke nan da s**a wuce. Idan kun dubi maganar Imam Ahmad sannan kuka dubi wannan kissa za ku fahimci cewa zanga-zanga saboda inkarin wani munkari lamari mai asali a cikin Musulunci, ba yi da alaka da abin da za a kira shi da cewa: Shi Kwaikwayon kafirai ne.

4. Da za a kaddara cewa: zanga-zanga wata sabuwar wasilar inkarin munkari ne ba wai tsohuwa ba ce a cikin Musulunci, to da ma hakan ba zai maida ita haramun ba, ko kuwa hakan ba zai sanya ta cikin jerin bidi'o'i a cikin Addini ba, saboda su Wasaa'il matukar dai ba su kasance haramun ba ne saboda zatinsu, ko kuwa matukar dai ba su kasance wani shi'ari ba ne kebabbe ga kafurai to babu wani laifi Musulmi su fa'idantu da su a cikin Maqaasidush Shari'ah, k**ar yadda dai Shaikhul Islam Ibnu Taimiyyah yake cewa cikin Majmu'ul Fatawa 30/206 watau k**ar fa'idantuwa da kayayyakin gini, da saka, da sauran sana'o'i. Kuma a wannan zamani namu sai mu ce k**ar su lasfikar da za a kira salla da ita saboda Kara sauti. Kai k**ar rike tasbaha saboda kidayar lafuzan zikiri, kun san cewa babban Shaikhinmu Sheik Ibnu Uthaimiin yana ganin halaccin amfani da shi, k**ar yadda ya zo cikin littafin: Jalasaatu Wa Fataawa Ibni Uthaimeen 8/32 saboda ita tasbaha tana daga cikin babi ne na Wasaa'il.

WANI TSOKACI:
1. Idan kuna cikin Kasar da ta haramta yin zanga-zanga to lalle wajibi ne ku bi dokar Kasar saboda tabbatar da maslahar zaman lafiya cikin Kasa.
2. Idan kuna cikin Kasar da take halatta yin zanga-zanga amma bayan samun izini na musamman to dole kafin yin zanga-zangar ku sami izini na musamman daga mahukunta tukun.
3. Idan kuna cikin Kasar da take halatta sakakkiyar zanga-zanga to halal ne ku shiriya zanga-zangar lumuna a duk lokacin da kuke ganin akwai maslaha cikin yin hakan. Allah Ya taimake mu.

An daga karatun daurar sahihu ibn khuzaimah saboda rashin lafiyar malam za'a sanar da lokaci na gabaMuna rokon Allah ya ...
09/07/2024

An daga karatun daurar sahihu ibn khuzaimah saboda rashin lafiyar malam za'a sanar da lokaci na gaba

Muna rokon Allah ya bawa Dr Kabir maru lafiya.
Yan'uwa ka sa malam cikin Addu'o'inku

Allah ya bada ikon halarta ya kuma anfanar damu
07/07/2024

Allah ya bada ikon halarta ya kuma anfanar damu

Address

No49 Sheme Faskari Local Govm
Katsina

Telephone

08035756874

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Markazu Khaleed Bn Waleed Litta'awun Wannasharul Islam Sheme. posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share