Farin Cikin Ma'aurata.

Farin Cikin Ma'aurata. Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Farin Cikin Ma'aurata., Religious Center, Dandume local government, Katsina.

MAYE MATSAYIN LEHE (LEFE) A CIKIN SHARI'AR MUSLUNCI?!SHIN WAJIBI NE YIN LEHE (LEFE)?!
02/02/2023

MAYE MATSAYIN LEHE (LEFE) A CIKIN SHARI'AR MUSLUNCI?!

SHIN WAJIBI NE YIN LEHE (LEFE)?!

02/02/2023

HALIN ZAMANTAKEWAR MALAM BAHAUSE

SHIN MAI KE KAWO SAƁANI BAYAN AN SHA SOYAYYA MARAS MISALI KAFIN AURE?!

MATASA A K**A SANA'A    Matashin idan kana son ka gina rayuwarka wacce kake yi yanzu da wacce za ka yi a nan gaba to kay...
07/09/2022

MATASA A K**A SANA'A

Matashin idan kana son ka gina rayuwarka wacce kake yi yanzu da wacce za ka yi a nan gaba to kayi ƙoƙarin k**a sana'a domin kuwa wannan zamanin babu abin da zai yiwu face sai da kuɗi.
Ka sani ci da shanka da suturarka da ta mahaifanka da karatunka, kai harma gudunmawar addini suna buƙatar kuɗi ne a wannan zamanin, don haka kada ka ɓata kanka da gayu na ƙarya, kada ka zo ka yi biyu babu, saboda haka gayu bai samu wurin zama ba a tare da kai, sai ka zage rantse ka cire kunya da ganin gari ka nemi kuɗi.

LOKACI MAFI HATSARI:      Haƙiƙa matakin matasantaka a kowacce al'ummar duniya, ana la'akari da shi a matsayin matakin f...
07/09/2022

LOKACI MAFI HATSARI:

Haƙiƙa matakin matasantaka a kowacce al'ummar duniya, ana la'akari da shi a matsayin matakin farko mafi muhimmanci wajen samar da ɗan'adantaka da al'umma baki ɗaya, kuma matasantaka ita ce tushen ginin zamanin da zai zo nan gaba

YADDA MATASHI ZAI GANE MACEN DA TAKE SON SHI:    Ya kai matashi! Idan kana so ka gane matashiyar da take sonka so na gas...
07/09/2022

YADDA MATASHI ZAI GANE MACEN DA TAKE SON SHI:

Ya kai matashi! Idan kana so ka gane matashiyar da take sonka so na gaskiya, to ka yi mata busharar yin rayuwa cikin wuya da rashin yalwar abin duniya bayan aurenku, idan ta amince zata aureka duk da wannan busharar, cewa za ta shiga matsakaiciyar rayuwa, to ka sani tabbas tana matuƙar sonka tunda za ta iya shiga ƙunci saboda ta rayu da kai.

Ya kai matashi! Kar kai wasa ka yi ma matashiya albishirin shiga wata sabuwar rayuwa wacce ba ta rigaya ta zo hannunka b...
07/09/2022

Ya kai matashi! Kar kai wasa ka yi ma matashiya albishirin shiga wata sabuwar rayuwa wacce ba ta rigaya ta zo hannunka ba, sannan kada ka yi ma matashiya albishir din wata rayuwa wacce kake hangowa ba tare da ka dade kana jin dadin wannan rayuwar ba.ka sani duk ranar da ta gano cewa babu wannan abu to kuwa zaku rabu, idan kuma ya kasance kun riga kun yi aure to ka sani za ku rabu da ita.

HALIN ƳAN MATAN WANNAN ZAMANI:          Da yawan yanmatan wannan zamanin ƙarya suke buƙatar a yi masu a lokacin neman au...
07/09/2022

HALIN ƳAN MATAN WANNAN ZAMANI:

Da yawan yanmatan wannan zamanin ƙarya suke buƙatar a yi masu a lokacin neman aurensu, hakan ya sa za ka ga basu sauraron waɗanda s**a zo masu da haƙikanin rayuwarsu ta gaskiya.
Ku sani duk wanda ya yi maku ƙarya a wajen neman aurenku cewa zai sanya ku a cikin wata sabuwar rayuwa, to ku sani za ku shiga ƙunci mai tarin yawa bayan aurenku.

Yake yar'uwata mai girma da daraja!A duk lokacin kika ga baki samun soyayya da muhimmantarwa da kulawar da s**a cancanci...
07/09/2022

Yake yar'uwata mai girma da daraja!
A duk lokacin kika ga baki samun soyayya da muhimmantarwa da kulawar da s**a cancanci ki samesu daga wurin mijinki, to ki tausaya ma shi tare da sauƙaƙamashi yanayin rayuwarshi na wani ɗan lokaci. ki ja hankalinshi sannu-sannu, tare da rarrashi, zaki ga ya dawo cikin rayuwarki tare da cikar da soyayya da tausasawa fiye da yadda yake maki a baya.

ZARGI DA GAJIYAWA A CIKIN ZAMANTAKEWA      Ya ke yar'uwata ki sani gundura mai ɗorawa da zargi maras yankewa suna kashe ...
07/09/2022

ZARGI DA GAJIYAWA A CIKIN ZAMANTAKEWA

Ya ke yar'uwata ki sani gundura mai ɗorawa da zargi maras yankewa suna kashe jin daɗin komai, ko da kuwa mutum bai aikata waɗannan abubuwan ba domin ya kashe jin daɗin zamantakewar aurensu ba.
Saboda haka ku yabi kyawawan ayyukan junanku, sannan ku yawaita yafe kurakuren junanku, domin kuwa kyakykawar magana tamkar mabuɗi ce, kyawawan zantuka suna buɗe zukatan waɗanda suke gefenka.

Yake "yar'uwata mai daraja!Ki tambayi mijinki tambayar da yake da ikon baki amsa, kuma tambayar da yake da kwaɗayin yin ...
07/09/2022

Yake "yar'uwata mai daraja!
Ki tambayi mijinki tambayar da yake da ikon baki amsa, kuma tambayar da yake da kwaɗayin yin magana dangane da ita, domin kuwa shi mutum koda yaushe yana son yin magana a kan abin da ya shagaltar da shi, saboda haka kiyi nazari mai zurfi kafin ki yi mashi tambaya.
Sannan ki sani aikinshi da samunshi su ne haƙiƙarshi, haƙiƙarshi shi ne iyalinshi, sannan yanayin rashin kuɗi shi ne matsalarshi, saboda haka ki taya shi tunani wajen neman mafita, domin kuwa samu mafita shi ne mafarkinshi.

Uwar gida ki sani kin kasance kyakykyawa a kwanakin da kika kasance kina jin kwanciyar hankali tare da mijinki, shin ko ...
07/09/2022

Uwar gida ki sani kin kasance kyakykyawa a kwanakin da kika kasance kina jin kwanciyar hankali tare da mijinki, shin ko kin mance cewa mijin nan naki shi ne sababin wannan jin daɗin naki?
To don mai yasa k**e mance waɗannan kwanakin? Sak**akon wasu ƙananan sabani da s**a bijiri maku a cikin wasu ƴan kwanaki?

07/09/2022

Address

Dandume Local Government
Katsina

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Farin Cikin Ma'aurata. posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share