Dr. Aminu Usman Abu Ammar Ph.D katsina

Dr. Aminu Usman Abu Ammar Ph.D katsina Domin yaɗa karatukan Sheikh Dr. Aminu Usman Abu Ammar

19/08/2026
14/08/2026

Khudbar SALLAR Juma'a tare da Sheikh Dr Aminu Usman (Abu Ammar) daga Markazus Salafy Barhim Estate Katsina

12/08/2026

Jawabin Godiya a wajen rufe Ramadan Tafseer na Shekarar 1447/ 2026.

Allah shi Kara ma Sheikh Abu Ammar lafiya da Taufeeqee ya kare mana shi daga dukkan Sharri.

20/07/2026

الناس للناس مادام الوفاء بهم # والعسر واليسر أوقات وساعات

وأكرم الناس مابين الورى رجل # تُقضي على يده للناس حاجات

18/07/2026

WAKILCIN MATA A MUSULUNCI TSAKANIN NASSI DA IJTIHADI

Kamar yadda Dr Aminu Usman Abu Ammar ya yi bayani a taƙaice, ni kuma na ɗan faɗaɗa bayanin NE SABODA ƳAN ƘWARAM, domin ya amfanin masu neman ƙarin fahimta da kuma masu son ganin hujjojin malamai dalla dalla.....

A duk lokacin da aka taso da wata mas'ala ta addini, ya kamata mu fara da AlQur'ani da Sunnah, sannan fahimtar magabatan wannan al'umma. Domin ALLAH ya ce

فإن تنازعتم في شيء فردوه إلى الله والرسول

"Idan kuka yi saɓani a kan wani abu, ku mayar da shi zuwa ga ALLAH da Manzonsa." (Nisa'i: 59)

Game da wakilcin mata a majalisa, babu aya ko hadisi sahihi da ya ambaci wannan tsarin siyasa da sunansa...

Dalili kuwa shi ne, tsarin majalisar dokoki na zamani bai kasance a zamanin Annabi ﷺ ba...

Hadisin da malamai s**a fi tattaunawa shi ne:

«لن يفلح قوم ولوا أمرهم امرأة»

"Mutanen da s**a ba mace shugabancin al'amuransu ba za su yi nasara ba.

Sai dai tambayar da malamai s**a yi ita ce:

Shin wannan hadisi yana magana ne kan dukkan mukaman gwamnati, ko kuwa yana magana ne kan babban shugabanci kawai?

(الولاية العامة)

A nan ne aka sami sabanin ijtihadi.

Wasu malamai, kamar su.
Shaikh Binbaz
Shaikh Ibn Uthaymin
Shaikh Salih Al-Fawzan
sun fahimci cewa wannan hadisi ya haɗa da irin waɗannan mukamai, saboda haka s**a hana.

A gefe guda kuma, malamai irin su
Shaikh Yusuf Alƙaradawi Shaikh Wahbah AlZuhayli Shaikh Mustafa Al_Zarqa
sun bambanta tsakaninsu.

- الولاية العامة — babban shugabanci.

- الوكالة أو النيابة — wakiltar jama'a da isar da muradunsu.

A ganinsu, ɗan majalisa ba shugaban ƙasa ba ne, ba gwamna ba ne, kuma ba shi kaɗai ke yanke hukunci ba. Wakili ne na jama'a, kuma aikinsa yana gudana tare da sauran wakilai a cikin tsarin gwamnati.

Malaman Usulul Fiqh sun kafa ƙa'ida mai girman gaske.
(الأصل في الأشياء الإباحة حتى يدل الدليل على التحريم)

"Asali a al'amura shi ne halaccinsu har sai hujja ta tabbatar da haramcinsu."

Haka kuma, Imam AlQarafi ya bayyana cewa bambance bambancen zamani da sababbin al'amura na iya buƙatar sabon ijtihadi, muddin ba a saɓa wa nassi ba.

Imam shawkani ma ya yi nuni da cewa idan babu nassi bayyananne a kan wata sabuwar mas'ala, ƙofar ijtihadi tana nan a buɗe ga masana saboda haka wannan ijtihadi ba Abu Ammar ya fara shi ba shima kwaikwayo yayi daga wasu malamai magabata...

Saboda haka, wannan ba mas'alar da za a ce an yi ijma'i a kanta ba ce. Mas'ala ce ta ijtihadi, kuma a irin waɗannan mas'aloli, ba zaka auna gaskiya da yawan masu magana.

Don haka, idan wani malami ya ce wakilcin mata ya bambanta da babban shugabanci, wannan ba sabon addini yake ƙirƙira ba ne. Yana bayyana ɗaya daga cikin ra'ayoyin ijtihadi da wasu manyan malaman Musulunci na zamani s**a ɗauka.

Mu bambanta tsakanin abin da nassi ya yanke hukunci a kansa da kuma abin da malamai s**a yi ijtihadi a kansa. Wannan shi ne adalcin ilimi, kuma shi ne abin da ya fi kare mutuncin addini da mutuncin malamai....

والله المستعان، وعليه التكلان، ولا حول ولا قوة إلا بالله.

CEO Tea Palace Comrade Usman Hussaini Rafukka Ina rokon Allah da sunayensa kyawawa yasama wannan Company Albarka... Cong...
05/07/2026

CEO Tea Palace Comrade Usman Hussaini Rafukka Ina rokon Allah da sunayensa kyawawa yasama wannan Company Albarka... Congratulations.

Address

Katsina

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Dr. Aminu Usman Abu Ammar Ph.D katsina posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

Share