04/09/2024
Ya maji roƙon gazajje,
Rabbana tashe ni in je,
Daibah in ga mafi mazaje,
Kwarjini ga kyau da sāje,
Da wushirya ba ta famfara ba.
In gabatar da gaisuwata,
Gun mafificin halitta,
In gaya masa tau buƙata,
Ke gare ni da tatssananta,
Shi bai taɓa ƙyale mai kira ba.
In kirashi kira garibai,
Ya fitilar haske duffai,
Sabulun wankan zunubbai,
Ya tafarkin iske rabbai..
- Marigayi Alhaji (Dr.) Aliyu Namangi