Dan Jatau

Dan Jatau Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Dan Jatau, Religious organisation, Sharada Phase II Kano, Kano.

02/08/2024

🚨| Yana da kyau idan da hannun ka a kona Digital Industrial Park (DIP) Nigerian Communication Commission (NCC) ka san wannan.

DIP NCC daya ce daga cikin centres guda shida da aka gina a NIGERIA. Kowane zone da ke kasar nan an kai musu guda daya. A northern states, Kano ce kadai ta samu.

An samar da center din ne don promoting digital economy and entrepreneurship for northern youths. Anan ne ake sa ran kaddamar da Data Centre ta farko a northern Nigeria. Wanda zata iya kawo wa Kano Haraji da kudin shida sama da million dari uku duk wata.

Aikin da akai a gurin, da systems da aka zuba, da servers, da devices da configurations din CISCO ne s**a zo daga America s**a yi. Na tabbata idan ba babban rabo ba da kuma ikon Allah, wannan gurin bazai tashi ba. Shikenan an rufe babin sa. Sabida billion dollar project ne.

A yadda plan din yake DIP centre zata samarwa da Kano ma'aikata akalla dubu goma sha. Wannan wuri zai zama wuri na farko a arewa da yan arewa zasu amfana da shi wajen koyan advanced networking, cloud computing, data science da Business Analytics.

📍 Idan zuga ku akai, to an cuce ku, idan kuma kwakwalanku ne, kun cuci kawunan ku. Domin kuwa salary din mutum daya a wajen zai iya kula da yan gidan ku mutum goma. A karshe aikin assha da ku kayi yayi costing ma Kano wannan opportunity din da Jobs da kuma revenue.

Ina tunani anan?

Don Girman Allah kuyi sharing don su gani. Su kuma san me su kayi.

Muhammad Ubale Kiru

02/08/2024

Kuyi hankali da masu tunzura ku wadanda ba'a cikin ku suke ba!

21/06/2024

Wasu lokutan fa kana da bukatar bayyanar da ɓoyayyen karatu kafin mai Koma ya fahimci cewa lallai Kifi yana kallon sa!

Dan Jatau

13/06/2024

SAƘO MAƘOƘO!

Ayi amfani da hankali wajen karantawa don Allah!

INA NEMAN ALFARMA!
Don Allah ina neman alfarma, kar wanda ya ƙara yi min "sharing" ko "tagging" duk wani abu da ya shafi rikicin masarautar Kano! Bani da sauran wata sha'awa game da cigaba da tattaunawa akan wannan batun!

SAƘO ZUWA GA KWANKWASO DA GANDUJE!
Duk waɗanda suke da kusanci da Kwankwaso ko Ganduje, don Allah ga saƙo ku gaya musu: Ku sanar dasu cewa; don Allah kar su fasa ko ja da baya akan ƙudirin su akan Masarautar Kano domin cikar burin su ne da kuma na iyayen su ganin lallai sai sun ga bayan Masarauta! Wannan shine abinda kowane ɗa na gari ya kamata ya kasance, ya tabbatar ya cika burin magabatan sa kuma bai bari duk wani abu da iyayen sa s**a kafa bai rushe ba. TABBAS SUN CIKA 'YA'YA!


SAƘO ZUWA GA AMINU, SANUSI DA ABBA!
Sannan duk wanda yake da kusanci da Aminu ko Sanusi ko Abba, ga saƙo, don Allah, ku gaya musu cewa; Don Allah kar su hankalta, kar su gyara, kar suyi abinda ya dace. Su ci gaba da cin dunduniyar junan su, har sai maƙiyansu sun samu nasarar yin amfani da su wajen rushe tare da lalata duk wani buri da wahalar da iyayen su s**a ɗauki shekaru suna yi don ganin tabbatuwar masarautar! Wannan shine irin sakamakon tarbiyyar da magabatan su s**a basu. Za su kafa tarihin da ba'a taɓa kafawa ba! 'YAN BANZA SUN YI NASARA AKAN 'YAN KWARAI!

Sai anjima!

SHAWARA:!
Idan baka ji daɗin rubutun nan ba, kayi hakuri da karanta ka wuce domin duk abinda za ka faɗa ba zai chanja rubutun ba!

Address

Sharada Phase II Kano
Kano

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Dan Jatau posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share