10/07/2026
KOWACE RAI TANA TARE DA WANDA TAKE SO. ❤️
Cikin ikon Allah, a yau na samu damar halartar majalisar Fadilatu Sheikh Kabir Bashir Abdulhamid Hafizahullahu Ta'ala ta karatun Al-Adabul Mufrad da ake gabatarwa a Rijiyar Zaki.
Bayan kusan shekara biyu ban samu damar halartar wannan majalisa ba, Allah Ya ƙaddara a yau na halarta. Alhamdulillah, na amfana matuƙa, kuma ina roƙon Allah Ya sanya mana albarka a cikin ilimin.
Wallahi, farin cikina ba ya misaltuwa. Na sake ganin masoyina, Sheikhana Abin da ya fi faranta mini rai shi ne lokacin da ya ce da ni "Masha Allah, sannu da zuwa, ka dawo." Wannan kalma ta faranta mini rai ƙwarai
Ya Allah, Ka ƙara wa Sheikh ɗinmu lafiya, ƙarfi imani da ikhlasi, Ka saka masa da mafificin alheri a duniya da lahira, Ka albarkaci iliminsa, Ka ci gaba da amfanar da al'umma ta hanyarsa.
Allahumma Amen. 🤲❤️