Tauhid Hausa Media

Tauhid Hausa Media Spreading Islamic information (knowledge), incuding Books, lectures, and preaches of our Islamic Scholars! These and others are the great challenges upon us.

IN THE NAME OF ALLAH MOST MERCIFUL, MOST BENEFICIENT IN MERCY
All praises are due to Allah, and may peace and blessing of Allah be upon our leader, the Messenger of Allah, And upon all his family and his Companions. To proceed:
KNOW MY MUSLIM BROTHERS AND SISTERS, May Allah be merciful upon you, that the purpose of creating US is to WORSHIP ALLAH; AS He says in the Holy Qur’an: “I HAVE ONLY CREATE

D JINNS AND MEN, THAT THEY MAY SERVE ME” [QUR 51:56]. HENCE, it is COMPULSORY UPON US to know four (4) basic things;-
THE FIRST IS KNOWLEDGE: Which is knowing about Allah (SWT), His prophet (SAW), and religion of Islam. THE SECOND IS ACTION: Which is acting according to knowledge. THE THIRD IS CALLING AND PROPAGATING THE KNOWLEDGE AND PRACTICE OF IT. THE FOURTH IS TO HAVE PATIENCE AND PERSEVERANCE WITH ANY MISFORTUNU FACED IN THEM (learning, practicing, teaching and calling others to it). The people that past before us has suffered a lot in seeking for knowledge, but nowadays the things becomes so easy for us due to the tireless effort of the Scholars in gathering all information (knowledge) in books. So also, majority of those books that were written in ARABIC language, have been TRANSLATED and EXPLAINED by our native scholars in our common languages of communication such as; HAUSA, YORUBA, ENGLISH, and so on. In order to participate in this noble action of spreading knowledge and easing the way for us to get that knowledge obligatory upon us at our doorstep, WE BROUGHT THE FOLLOWING;-
ISLAMIC TEXT-BOOKS: Of Arabic, Hausa, and English versions for the higher and very basics of Islamic knowledge needed by all, such as; Saheehul Bukhaary (By: Imamu Bukhaary), Saheehu Muslim (By: Imamu Muslim), Muwadda Malik (By: Imamu Malik), Kitaabut-Tauheed (By: Sheik Muhammad ibn Abdulwahab), Sifatu Salatin Nabiyyi S.A.W (By: Sheikh Muhammad Naasir-ud-Deen Al-baani), Hisnul-Muslim (By: Sheikh Sa’id bn Ali bn Wahaf Al-Qahtani), Arba’unan-Nawawy (By: Imamu Yahya bn Zakariya’ Annawawi), Al-Akhadari (By: Imamu Abdurrahman Al-akhdari), E.T.C, including; The Holy Qur’an (of various Qira’at, versions, models, and sizes). ISLAMIC DOWNLOADS AND MEMORY CARDS: Of Audio and Video lectures and preaches of our Islamic Scholars, such as; Sheik Ja’afar M.Adam Kano, Sheik Albani Zaria, Sheik Abubakar Gero, Sheik Muhammad bn Uthman, Sheik Aminu Ibrahim Daurawa, Dr. Isah Ali Fantami, Dr. Sani Umar R/lemo, Dr. Umar Sani Fage, Sheikh Haruna Kabiru

17/04/2023

Yazo a cikin littafin Kiyamu Ramadan na Sheikh Muhammad Nasiruddeen Albani, yana cewa: Daren Lailatul Kadri shine daren ashirin da bakwai ga Watan Ramadana, wannan itace magana mafi karfi daga dukkanin naganganun da malamai sukayi, kuma mafi yawancin hadisan da sukazo akan wannan haka suke nunawa, daga cikin wadannan hadisai akwai hadisin da aka rawaito daga Zurru bn Hubaish yace: An baiwa Ubaiyu dan Ka'ab (RA) labari, Abdullahi dan Masa'ud (RA) yana cewa: "Wanda duk ya mike a kowane dare cikin shekara yayi ibada, tabbas zai dace da Lailatul Kadri". Sai Ubaiyu (RA) ya ce: "Allah Ya jikan Abdullahi dan Masa'ud (RA) yana nufin ne kada yasa mutane suyi sakaci su kwanta suki fitowa s**e sai a ranar kaza zasu tashi suyi ibada, don haka ya bar musu wannan mas'ala a rufe, domin suyi ta ibada kawai. Yace na rantse da Allah wanda babu abin bautawa da gaskiya sai shi, Lailatul Kadri tabbas a cikin Watan azumin Ramadana take (mai ruwaya yace Ubaiyu bn Ka'ab rantsuwa yake baya yin ko togaciya), kuma yace na rantse da Allah, Ni nasan kowanne darene daren Lailatul Kadri, shine daren da Manzon Allah (SAW) Ya umarcemu damu tashi muyi ibada a cikinsa, shine daren da safiyar zata waye a ashirin da bakwai.

Falalar wannan daren mai girma ne, Saboda cikinsa aka saukar da Al-kur'ani wanda shine jagoran wanda yayi riko da shi zuwa ga hanyoyin daraja da karamci, kuma ya daga shi zuwa ga tsororuwan girma da dauwama.

Ya isa matsayi ga daren "Lailatul Kadir" cewa ya fi wata dubu alheri, da fadin Allah Ta'ala: "Hakika mu ne muka saukar da shi cikin lailatul kadari, menene ya sanar da kai abin da ake kira lailatul kadari, lailatul kadari yafi Alkhairi sama da watanni dubu. Mala'iku suna sauka da Ruhu (Jibrilu) cikinsa da izinin Ubangijisu da ko wane Umarni, Aminci ne shi har fitowar Alfijir". [Alkadr:1-5].

Kuma cikin lailatul kadir ake rarrabe Al'amura bayyanannu na hikima, da fadin Allah Ta'ala: "Lalle ne Mu muka saukar da shi a wani dare mai albarka. Lalle Mu mun kasance masu yin gargadi. A cikinsa (shi daren) ake rarrabe kowane al'amari da ake hukuntawa. Umarni ne daga wurinmu. Lalle mune muka kasance masu aikawa. Rahama daga Ubangijinka, hakika shine Mai ji Masani". [Addukhan: 3-6].
🔊TA YAYA MUSULMI ZAI NEMI LAILATUL KADRI:

Lalle wannan dare mai albarka wanda duk aka haramtawa an haramta masa alkhairi dukansa, kuma babu wanda za'a haramta masa alherin wannan dare sai ma shakiyi mara arziki. Saboda haka ake son Musulmi ya dage wajen biyayyar Ubangiji, ya raya dararen yana mai imani da kwadayin lada mai girma, idan ya aikata haka Allah zai gafarta masa abin da ya gabata na zunubansa. Da fadin Annabi (SAW) cewa: "Wanda ya sallaci daren Lailatul Kadri yana mai imani da neman lada za a gafarta masa abin da ya gabata na zunubansa." [Bukhari (4/217) Muslim (759)].

Kuma ana so a yawaita addu'a cikin daren, domin ya zo daga Nana A'isha (RA) tana cewa, "Na ce wa Manzon Allah (SAW) yaya kake gani idan na gane Lailatul Kadri me zan fada a ciki? Sai yace: ki fadi:

"ALLAHUMMA INNAKA AFUWWUN, TUHIBBUL-AFWA, FA'AFU ANNI"

Ma'ana: "Ya Ubangiji kai ne mai yawan Afuwa, Kana son Afuwa, Ka yi min Afuwa." [Tirmizi (3760) Ibn Majah (3850)].

🔊DAGA ALAMOMINTA:

Ka sani ya kai dan uwa cewa an wassafa safiyar daren Lailatul Kadri saboda musulmi su san wane dare ne ita, k**ar haka:

Daga Ubayyu (RA) yace: "Manzon Allah (SAW) ya ce: "Safiyar Lailatul Kadri rana 🌕 tana fitowa babu haske sosai, k**ar wata langar tasa ce har ta d**o sama." [Muslim (762)].

Daga Abu Huraira (RA) yace: "Mun yi Muzakarar Lailatul Kadri wajen Annabi (SAW) sai yace: "Waye daga cikinku zai tuna lokacin da wata 🌙 ya fito, yana k**ar yankin akushi?" [Muslim (1170)].

Daga Ibn Abbas (RA) yace: "Manzon Allah (SAW) yace: "Daren Lailatul Kadri dare ne mai walwala 🏡 a sake babu zafi babu sanyi, rana tana fitowa a safiyarsa mai rauni ja-ja ja-ja 🌇.

👉TAMBIHI:

Daga wadannan hadisai ne zamu gane cewa abubuwan da ake fada na cewa idan daren ya yi, ana ganin bishiyoyi 🌴🌴 sun kwanta, ko ana iya hango ka'aba, ko gidaje 🏠🏠 suna kwanciya da dai sauran abubuwan da ake fada wadanda basu da asali a addini, duk abubuwa ne da ya k**ata mu watsar, mu k**a wanda ya zo daga fiyayyen halitta (SAW) wanda ba ya fadar abinda yake son zuciya, duk abinda ya furta wahayi ne daga Ubangijin kowa da komai.

ALLAH (SWT) YA SA MU DACE, AMIN.

14/04/2023

An rawaito daga Ibn Umar ya ce : Manzon Allah (SAW) ya ce: "Ku nemi Lailatul Kadri a goman karshe, idan kuma dayanku ya yi rauni ko ya gaza to kada ya bari ayi galaba kansa a kwana bakwai na karshe" [Bukhari (4/221) Muslim (1165)].

07/08/2022

Ashura!

Mutane sun kasu gida uku dangane da ranar Ashura.

1. Masu bakin ciki da kuka da dukan jiki, da fitar wa kai jini saboda juyayin kashe jikokin Manzon Allah S.A.W da a ka yi a wannan rana, a shekara ta 61 bayan hijirar Manzon Allah S.A.W.

Wannan kaso sun sabawa koyarwar Manzon Allah S.A.W da ya hana aikata wadannan abubuwa idan musifa ta samu mutum, hakanan kuma bai yi umarni da ware ranar da wani ya mutu a mayar da ita ranar kuka da juyayi ba.

2. Kaso na biyu : Masu farin ciki, da cika ciki a wannan rana, don murna da kashe Jikokin Manzon Allah S.A.W da kishiyantar masu bakin ciki da juyayi a wannan rana.

Wadannan ma ba sa kan Sunnar Manzon Allah S.A.W, domin ba ya halatta Musulmi ya yi murna da kashe dan uwansa Musulmi, ballantana Iyalan gidan Manzon Allah S.A.W.

3. Masu azumtar wannan rana don koyi da Manzon Allah S.A.W da bin umarninsa, da neman lada a wurin Allah. A gefe guda kuma ba sa murna da kashe Jikokin Manzon Allah S.A.W da a ka yi a irin wannan rana a shekara ta 61 A.H. Sun yi bakin ciki da abin da ya faru, amma kuma ba su maida ranar ta zama ranar kuka da dukan jiki, da zaman makoki, saboda babu inda Manzon Allah S.A.W ya koyar da hakan a Sunnarsa ingantacciya.

Ya kai dan uwa ka sani koyi da Manzon Allah S.A.W shi ne tsira duniya da lahira.

Allah ka samu cikin bayinka nagartattu duniya da lahira. Ameen.

✍️ Sheikh Muhammad Rabiu R/lemo

02/05/2021

🔊TA YAYA MUSULMI ZAI NEMI LAILATUL KADRI:
Lalle wannan dare mai albarka wanda duk aka haramtawa an haramta masa alkhairi dukansa, kuma babu wanda za'a haramta masa alherin wannan dare sai ma shakiyi mara arziki. Saboda haka ake son Musulmi ya dage wajen biyayyar Ubangiji, ya raya dararen yana mai imani da kwadayin lada mai girma, idan ya aikata haka Allah zai gafarta masa abin da ya gabata na zunubansa. Da fadin Annabi (SAW) cewa: "Wanda ya sallaci daren Lailatul Kadri yana mai imani da neman lada za a gafarta masa abin da ya gabata na zunubansa." [Bukhari (4/217) Muslim (759)].
Kuma ana so a yawaita addu'a cikin daren, domin ya zo daga Nana A'isha (RA) tana cewa, "Na ce wa Manzon Allah (SAW) yaya kake gani idan na gane Lailatul Kadri me zan fada a ciki? Sai yace: ki fadi:
"ALLAHUMMA INNAKA AFUWWUN, TUHIBBUL-AFWA, FA'AFU ANNI"
Ma'ana: "Ya Ubangiji kai ne mai yawan Afuwa, Kana son Afuwa, Ka yi min Afuwa." [Tirmizi (3760) Ibn Majah (3850)].
🔊DAGA ALAMOMINTA:
Ka sani ya kai dan uwa cewa an wassafa safiyar daren Lailatul Kadri saboda musulmi su san wane dare ne ita, k**ar haka:
Daga Ubayyu (RA) yace: "Manzon Allah (SAW) ya ce: "Safiyar Lailatul Kadri rana 🌕 tana fitowa babu haske sosai, k**ar wata langar tasa ce har ta d**o sama." [Muslim (762)].
Daga Abu Huraira (RA) yace: "Mun yi Muzakarar Lailatul Kadri wajen Annabi (SAW) sai yace: "Waye daga cikinku zai tuna lokacin da wata 🌙 ya fito, yana k**ar yankin akushi?" [Muslim (1170)].
Daga Ibn Abbas (RA) yace: "Manzon Allah (SAW) yace: "Daren Lailatul Kadri dare ne mai walwala 🏡 a sake babu zafi babu sanyi, rana tana fitowa a safiyarsa mai rauni ja-ja ja-ja 🌇.
👉TAMBIHI:
Daga wadannan hadisai ne zamu gane cewa abubuwan da ake fada na cewa idan daren ya yi, ana ganin bishiyoyi 🌴🌴 sun kwanta, ko ana iya hango ka'aba, ko gidaje 🏠🏠 suna kwanciya da dai sauran abubuwan da ake fada wadanda basu da asali a addini, duk abubuwa ne da ya k**ata mu watsar, mu k**a wanda ya zo daga fiyayyen halitta (SAW) wanda ba ya fadar abinda yake son zuciya, duk abinda ya furta wahayi ne daga Ubangijin kowa da komai.
ALLAH (SWT) YA SA MU DACE, AMIN.
BY NAGABAS ISLAMIC CENTER.
CLICK THE LINKS BLOW TO JOIN; OUR FACEBOOK PAGE: https://mobile.facebook.com/Na-Gabas-Islamic-Center-1854818891486104 WHATSAPP GROUP:https://chat.whatsapp.com/JmjmnLvaB3YEXXABXrDxaY
TELEGRAM GROUP: https://t.me/nagabasislamiccenter

02/05/2021

🔊DAREN LAILATUL KADIRI:
Falalar wannan daren mai girma ne, Saboda cikinsa aka saukar da Al-kur'ani wanda shine jagoran wanda yayi riko da shi zuwa ga hanyoyin daraja da karamci, kuma ya daga shi zuwa ga tsororuwan girma da dauwama.
Ya isa matsayi ga daren "Lailatul Kadir" cewa ya fi wata dubu alheri, da fadin Allah Ta'ala: "Hakika mu ne muka saukar da shi cikin lailatul kadari, menene ya sanar da kai abin da ake kira lailatul kadari, lailatul kadari yafi Alkhairi sama da watanni dubu. Mala'iku suna sauka da Ruhu (Jibrilu) cikinsa da izinin Ubangijisu da ko wane Umarni, Aminci ne shi har fitowar Alfijir". [Alkadr:1-5].
Kuma cikin lailatul kadir ake rarrabe Al'amura bayyanannu na hikima, da fadin Allah Ta'ala: "Lalle ne Mu muka saukar da shi a wani dare mai albarka. Lalle Mu mun kasance masu yin gargadi. A cikinsa (shi daren) ake rarrabe kowane al'amari da ake hukuntawa. Umarni ne daga wurinmu. Lalle mune muka kasance masu aikawa. Rahama daga Ubangijinka, hakika shine Mai ji Masani". [Addukhan: 3-6].
🕑LOKACIN DAREN:
An rawaito daga Nana A'isha (RA) ta ce: "Manzon Allah (SAW) ya kasance yana dagewa a goman karshe na Ramadan, yana cewa: "Ku nemi Lailatul kadri cikin kwanakin mara a goman karshe cikin Ramadan". [Bukhari (4/225) Muslim (1169)].
Kuma an rawaito daga Ibn Umar ya ce : Manzon Allah (SAW) ya ce: "Ku nemi Lailatul Kadri a goman karshe, idan kuma dayanku ya yi rauni ko ya gaza to kada ya bari ayi galaba kansa a kwana bakwai na karshe" [Bukhari (4/221) Muslim (1165)].
Saidai yazo a cikin littafin Kiyamu Ramadan na Sheikh Muhammad Nasiruddeen Albani, yana cewa: Daren Lailatul Kadri shine daren ashirin da bakwai ga Watan Ramadana, wannan itace magana mafi karfi daga dukkanin naganganun da malamai sukayi, kuma mafi yawancin hadisan da sukazo akan wannan haka suke nunawa, daga cikin wadannan hadisai akwai hadisin da aka rawaito daga Zurru bn Hubaish yace: An baiwa Ubaiyu dan Ka'ab (RA) labari, Abdullahi dan Masa'ud (RA) yana cewa: "Wanda duk ya mike a kowane dare cikin shekara yayi ibada, tabbas zai dace da Lailatul Kadri". Sai Ubaiyu (RA) ya ce: "Allah Ya jikan Abdullahi dan Masa'ud (RA) yana nufin ne kada yasa mutane suyi sakaci su kwanta suki fitowa s**e sai a ranar kaza zasu tashi suyi ibada, don haka ya bar musu wannan mas'ala a rufe, domin suyi ta ibada kawai. Yace na rantse da Allah wanda babu abin bautawa da gaskiya sai shi, Lailatul Kadri tabbas a cikin Watan azumin Ramadana take (mai ruwaya yace Ubaiyu bn Ka'ab rantsuwa yake baya yin ko togaciya), kuma yace na rantse da Allah, Ni nasan kowanne darene daren Lailatul Kadri, shine daren da Manzon Allah (SAW) Ya umarcemu damu tashi muyi ibada a cikinsa, shine daren da safiyar zata waye a ashirin da bakwai.
👉TAMBIHI:
Hadisai sun zo suna nuni kan cewa Lailatul Kadri na cikin goman karshe, wasu hadisan kuma na cewa a kwanakin wutiri (mara) na goman karshe ne, Saboda haka babu cin karo tsakaninsu, Sannan wasu hadisan sun zo kan cewa tana cikin kwanaki bakwai na karshe, amma an kayyade su da wanda yayi rauni Saboda haka babu Ishkali (rikitarwa).
Dan uwa Allah ya yi maka albarka ya datar da kai ga yi masa da'a, ka sani a kowane dare Lailatul Kadri ya K**a, kai dai abin da za ka yi shine dagewa da ibada a goman karshe, a raya dararenta a kauracewa shimfida, kuma ka umarci iyalinka da hakan ka yawaita da'a ga Ubangiji.
Nana A'isha (RA) tana cewa: "Manzon Allah (SAW) Ya kasance idan goman karshe ta shigo yana nisantar iyali, ya raya dararenta, kuma ya tashi iyalansa." [Bukhari (4/233) Muslim (1174)].
Kuma tana cewa: "Ya kasance yana dagewa sosai a goman karshe irin dagewar da ba ya yi a kwanakin da basu ba." [Muslim (1174)].
ALLAH (SWT) YA SA MU DACE, AMIN.
BY NAGABAS ISLAMIC CENTER.
CLICK THE LINKS BLOW TO JOIN; OUR FACEBOOK PAGE: https://mobile.facebook.com/Na-Gabas-Islamic-Center-1854818891486104 WHATSAPP GROUP:https://chat.whatsapp.com/JmjmnLvaB3YEXXABXrDxaY
TELEGRAM GROUP: https://t.me/nagabasislamiccenter

13/04/2021

MARABA DA RAMADAN 🌙
Ramadana wata mai albarka ne, mai tarin alheri, Allah ya cika shi fal da falaloli masu tarin yawa k**ar haka;
👉AN SAUKAR DA AL-KUR'ANI A CIKINSA:
Allah (SWT) Ya saukar da littafinsa mai daraja domin shiriya ga mutane, kuma waraka ga muminai, yana mai Shiryarwa ga hanyar tsira yana bayyana ta, a cikin daren lailatul kadari cikin watan Ramadan mai alheri,
Allah mai girma da daukaka yace: "Watan Ramadan wanda aka saukar da Alkur'ani a cikinsa shiriya ne ga mutane da hujjoji bayyanannu daga shiriya da rarrabewa. To wanda ya halarta daga gare ku a watan sai ya Azumceshi". [Bakara: 185].
👉ANA KULLE SHAIDANU, A KULLE KOKOFOFIN WUTA DA BUDE NA ALJANNA ACIKIN SA:
Manzon Allah (SAW) Ya ce: "Idan watan Ramadan ya zo, sai a bude kofofin Aljanna Sannan a rufe kofofin wuta kuma a kulle shaidanu". [Bukhari (4/97), Muslim (2/757)].
Dukkan wannan yana kammaluwa daga lokacin da daren farko na watan Ramadan ya shigo. Saboda fadin Manzon Allah (SAW) : "Idan daren farko na watan Ramadana ya kasance, sai a kulle shaidanu da kangararrun aljanu, a rufe kofofin wuta, babu wadda za'a bari daga cikinta, a bude kofofin Aljanna ba za'a bar ko daya a rufe ba. Sai wani mai Kira yayi Kira: ya mai neman alheri matso kusa, ya mai neman sharri yi nesa, kuma Allah yana da wasu 'yantattu daga wuta, wannan kuwa yana faruwa a kowane dare". [Tirmizi (682), Ibnu Majah (1642)].
👉DAREN LAILATUL KADARI A CIKINSA:
Hakika Allah (SWT) Ya zabi watan Ramadan Saboda a cikinsa ne aka saukar da Al-kur'ani Wanda shine jagoran wanda yayi riko da shi zuwa ga hanyoyin daraja da karamci, kuma ya dagashi zuwa ga tsororuwan girma da dauwama, k**ar yadda Allah (SWT) Take cewa: "Hakika mu ne muka saukar da shi cikin lailatul kadari, menene ya sanar da kai abin da ake kira lailatul kadari, lailatul kadari yafi Alkhairi sama da watanni dubu. Mala'iku suna sauka da Ruhu (Jibrilu) cikinsa da izinin Ubangijisu da ko wane Umarni, Aminci ne shi har fitowar Alfijir". [....].
Da fadinsa: "Lalle ne Mu muka saukar da shi a wani dare mai albarka. Lalle Mu mun kasance masu yin gargadi. A cikinsa (shi daren) ake rarrabe kowane al'amari da ake hukuntawa. Umarni ne daga wurinmu. Lalle mune muka kasance masu aikawa. Rahama daga Ubangijinka, hakika shine Mai hi Masani". [Addukhan: 3-6].
👉AMSA ADU'A DA 'YANTARWA DAGA WUTA A CIKINSA:
Manzon Allah (SAW) yace: "Hakika Allah yana da wasu 'yantattu daga wuta a kowane dare cikin Watan Ramadan, kuma ga kowane musulmi yana da wata addu'a da zai roka,
BY NAGABAS ISLAMIC CENTER.
CLICK THE LINKS BLOW TO JOIN; OUR FACEBOOK PAGE: https://mobile.facebook.com/Na-Gabas-Islamic-Center-1854818891486104 WHATSAPP GROUP:https://chat.whatsapp.com/JmjmnLvaB3YEXXABXrDxaY
TELEGRAM GROUP: https://t.me/nagabasislamiccenter

13/04/2021

🔊WELCOMING RAMADHAAN (THE MONTH OF FORGIVENESS):
👉O you who Believe! Fasting is Prescribed to you as it was Prescribed to those before you, That you may (learn) Self - Restraint, Righteousness, Piety, God Conciousness"
Al Qur'aan 2:183
👉The Messenger of Allaah (pbuh) said: 'The five daily prayers, from one Jumu'ah to the next, and from one Ramadhaan to the next, are an expiation for whatever (sins) come in between, so long as one avoids major sins."
Saheeh Muslim - Vol 1, Hadith 522
👉The Messenger of Allaah (pbuh) said:
"... Whoever observes saum (fasts) in the month of Ramadhaan with sincere faith and hoping for a reward from Allaah, all his previous sins will be forfgiven"
Saheeh Al Bukhaari - Vol 3, Hadith 1901
🔊IMPLEMENT THE DAY-TO-DAY SUNNAH OF THE PROPHET (PBUH) AS MUCH AS POSSIBLE
"... So take what the Messenger (pbuh) assigns to you, and deny yourselves that which he withholds from you ..."
Al Qur'aan 59:7
🔊FASTING EVERY DAY OF RAMADHAAN
The Messenger of Allaah (pbuh) said: "Whoever believes in Allaah and His Messenger, establishes regular prayer and fasts the month of Ramadhaan, then it is incumbent upon Allaah to admit him into Paradise ..."
Saheeh Al Bukhaari - Vol 9, Hadith 7423.
BY NAGABAS ISLAMIC CENTER.
CLICK THE LINKS BLOW TO JOIN; OUR FACEBOOK PAGE: https://mobile.facebook.com/Na-Gabas-Islamic-Center-1854818891486104 WHATSAPP GROUP:https://chat.whatsapp.com/JmjmnLvaB3YEXXABXrDxaY
TELEGRAM GROUP: https://t.me/nagabasislamiccenter

*SANARWA               SANARWA                SANARWA**Daga yau Jumma'a 1 ga watan Ramadan 1441Hijrah* Zamu fara kawo mu...
24/04/2020

*SANARWA SANARWA SANARWA*

*Daga yau Jumma'a 1 ga watan Ramadan 1441Hijrah*

Zamu fara kawo muku Tafsirin Alkur'ani da wasu daga cikin manyan Mulumanmu na Sunnah zasu gabatar a wannan shekara ta 1441/2020 Insha Allah.

*Malaman sun hada da;*
(1) Sheikh Dr. Muhammad Sani Umar R/Lemo,
(2) Sheikh Dr. Isah Ali Ibrahim Pantami, da
(3) Sheikh Dr. Abdallah Usman Umar G/Kaya

*Domin samun wadannan karatuttuka ku biyomu a shafikanmu k**ar haka;*

*WhatsApp:* https://chat.whatsapp.com/JmjmnLvaB3YEXXABXrDxaY

*Telegram:* https://t.me/nagabasislamiccenter

Address

KANO
Kano

Telephone

+2347036431435

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Tauhid Hausa Media posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share