13/06/2024
Tabbas jawaban Sanata Shehu sani a Ranar Demokradiyya ga Shugaba Tinubu sun share hawayen ƴan Najeriya tare da isar da asalin abinda ke faruwa a Najeriya.
Tabbas sauran kwamarawa manyansu da ƙananunsu ya kamata suyi koyi da Sanata Shehu Sani domin ya tabbatarwa ƴan Najeriya cewa shi mai isar da koken ƴan kasa ne.inji Barrah Almadany.
Shugaban kungiyar yan Jaridu masu yada manufofinsu a yanar gizo Malam Barrah Almadany ya bayyana haka ne yayin taron manema labarai da ya gabatar a safiyar ranar Alhamis a babban birnin Tarayya Abuja, don jinjinawa Sanata Shehu sani bisa yadda ya shafawa idonsa bula ya sanar da Shugaban kasa abinda yake damun Najeriya ba tare da tsoro ko neman mukami ba.
Almadany ya bayyana gwagwarmayar Sanata Shehu sani a matsayin babban abin koyi ga yan Najeriya domin Iranta ake buƙata a halin da Najeriya ke ciki a yau.