14/09/2020
SUWAYE 'YAN DARIQAR TIJJANIYYA???
'Yan Dariqar Tijjaniyya Wasu Mutane Ne Da:
(1). Suke suna cikin Ahlus Sunnah wal jama'a na sahun gaba.
(2). Mafi yawancin su suna biyar mazhabar malikiyyah ne, amma daga cikin su akwai masu biyar sauran mazhabobin fiqhu, kamar shafi'iyyah, da hanabila.
(3). Sun imani da Allah da manzon sa, da mala'ikun sa, da littattafan sa, da manzannin sa, da qadra ta alkhairi ko ta sharri, sun Kuma Yi imani da ranar qarshe.
(4). Sun shaida babu abun bautawa na gaskiya sai Allah, Kuma Annabi Muhammad manzon sa ne, suna yin sallah, suna bayar da zakka, suna yin azumin watan Ramadan, suna zuwa aikin hajji.
(5). Suna Kusantar Allah da abubuwan da ya wajabta musu, sannan suna yin qari da nafiloli domin samun qarin kusancin Allah.
(6). Suna kyautata zato ga dukkan musulmai, basa yiwa Allah da manzon sa shisshigi.
( 7). Basa kafirta musulmai, basa Kuma shiga tsakanin su da Allah, duk mai fadin la'ilaha illallahu musulmi ne a wajen su.
(8). Sun Yi imani da cewa duk Wanda ya Yi da'awar ya fi wani Annabi to wannan maqaryaci ne kafiri.
(9). Sun tabbatar da cewa salatul fatihi bata kai Alqur'ani ba b***e ta fi shi.
(10). Sun Yi imani da cewa Alqur'ani shine fiyayyen zance, Kuma harafi daya daga cikin sa baya zuwa dai dai da wani Abu ko menene.
(11). Sun Yi imani da cewa duk Wanda ya Yi iqirarin cewa manzon Allah boye wani Abu da Allah ya umurce shi ya Isar to wannan maqaryaci ne kafiri.
(12). Sun amince da cewa duk Wanda ya ce ana Yi masa wahayi ta kowace fuska to wannan maqaryaci ne kafiri.
(13). Sun Yi imani da cewa duk Wanda ya ce wani wuridi ya fi Alqur'ani to wannan maqaryaci ne kafiri.
(14). Sun tabbatar da cewa duk Wanda ya ce wani mutum ya fi sahabban manzon Allah to wannan batacce ne.
(15). Sun imani da cewa duk Wanda ya zagi sahabban manzon Allah ko ya tauye matsayin su to wannan kafiri ne.
(16). Suna son iyalan gidan manzon Allah da sahabban sa, basa banbance tsakanin su.
(17). Sun ambayon Allah a kowane hali, Kuma suna yin umurni da yin zikirin
(18). Sun tabbatar da cewa sahabban manzon Allah adilai duk, Kuma basa shiga cikin abun da ke faruwa a tsakanin su na rikici
(19). Basa Kiran sunan kowane sahabi har sai in Alkhairi zasu fadi a game da shi
(20). Kuma masadirut tashree'e wadanda aka Yi ittifaqi a kan su sune Alqur'ani da hadisi da ijma'in malamai, sune qaluluwar hujja a wajen su, sun yarda duk hujjar da ba wannan ba batatta ce
(21) Suna karanta Alqur'ani Suna hukunci da shi.
idan bakasan suwaye 'yan darika tijjaniya to yau kasani idan wani yatambayeka to ga amsa dazaka bachi
idan kaji dadin karanta wannan post to katurawa sauran groups din musulmai Suma su karanta su karu da kai
Allah duk wanda yatura wannan post zuwa cikin wani groups kabiyachi da kyautar gida Achikin Aljanna Alfarman Annabi ((muhammadu s,a,w))
idan baka cikin wannan page kayi like 👍 and following ✔