11/07/2025
Abinda Lawan Triumph yace...
-akwai wani sahabi bashi da lafiya sai aka ɗakko shi a ambulance, aka kaishi wajen Annabi (s.a.w), sai Annabi yaga kan sahabin nan yana zubar da kwarkwata. Abinda yasa kan sahabin nan yake zubar da kwarkwata, sbd yayi kwana 2 be wanke kansa ba. Lawan Triumph yaci gaba da cewa- kwarkwata da faso na ƙafa ba ƙazanta bace awajen larabawa.
Note: abinda yasa Lawan Triumph ya bada wannan labarin shine- yana so ya tabbatarwa duniya Lallai Annabi yanada kwarkwata. Shiyasa ma ya fara kawo labarin sahabin cen, daga baya kuma yace Annabi yana zuwa gidan gwaggonsa Ummu-haram ta k**a masa kansa har tana cire masa kwarkwata (wal iyazu billah).
Ga tambayoyina zuwa ga mal. Lawan Triumph, ko yaransa masu kareshi.
1) ka ce Ummu-haram gwaggon Annabi ce, kuma baka faɗi nasabar data haɗata da Annabi ba, tarihi ya nuna ba Ummu-haram ba, ko mijinta ubadatu-bin-sabit Annabi ya bashi sama da shekara 19 da haihuwa (kenan tazarar da take tsakanin Annabi da Ummu-haram ba kaɗan bace), kayi mana bayanin ta yaya ta zama gwaggon Annabi s.a.w?
2) duk da ka ce kwarkwata ba ƙazanta bace awajen larabawa, amma kuma da kanka ka warware wannan mgnr taka, tunda acikin maganganun naka ka ce saida sahabin yayi kwana 2 be kula da kansa ba sannan kwarkwatar ta fito masa. Kenan shima Annabi kana tuhumarsa da yin kwana 2 be wanke kansa ba? (Wal iyazu billah)
3) binciken masana ya tabbatar da ƙazanta ce take kawo kwarkwata, wannan ilimi ne da duk duniya ta sani, ko a ina Mal. Lawan ya samo cewa- banda larabawa?
4) a iya ɗan ƙaramin bincike na, kaf cikin gama garin mutanan Saudiyya babu me kwarkwata, sbd yadda larabawa suke kula da kansu fiye da sauran ƙabilun duniya, indai har waƴannan gama garin ƙazaman larabawa basu da kwarkwata, ta yaya kake tunanin akwai kwarkwata akan fiyayyan-halitta?