11/07/2025
SHEIKH LAWAN TRIUMPH!
Maganar guda 3 ce:
Copied
1. Masuss**a ne ya faro hayaniyar ta hanyar murɗe fassarar hadisin Ummu Haram, ya ce ta na cire kwarkwatar, don ya ƙaryata littafin Bukhari gaba ɗaya.
2. Malam Lawan ya zo karatun aikin Hajji, sai ya zo gurin hidimar kula da Mahajjata da Annabi Sallallahu alaihi Wasallam ya yi, tare da kula da marasa lafiyarsu, har ya bayar da misali da Ka'abu bn Ujrata, wanda kwarkwata ta fara bayyana a kansa saboda jinya. Nan Malam Lawan ya bayyana yanda kwarkwata ta ke damun Larabawa, tare da nuna cewa ita ba ta kasance wani aibu ba a gare su, ya kuma yi amfani da wannan gaɓar don nuna cewa ko da fassarar da Masuss**a ya yi wa hadisin Ummu Haram daidai ce, to wannan ba zai zama hujjar ƙin karɓar hadisin ba. Amma fa shi Malam Lawan bai fassara larabcin hadisin da cire kwarkwata ba, ya fassara ne da gyara gashi.
3. Can kuma sai a ka jiyo wani malami ya ɗauki bayanin Malam Lawan ya lanƙwasa shi da cewa ai Malam Lawan ne ya ce a na cire Kwarkwata. Daga nan kuma waɗanda ba sa karatu ko saurarar karatu s**a fara zagi cewa Malam Lawan, ba Masuss**a ba, ya zagi Annabi Sallallahu alaihi Wasallam!
A ƙarshe dai, Shari'a Commission ta jihar Kano ta gayyaci Malam Lawan a yau, kuma ya kunna musu abinda ya faɗa, kuma sun sallame shi tunda ba su ga inda ya yi laifi ba.
Sai dai, ɗaliban Abduljabbar, da wasu masu son fitina, sun ja tinga, har suna kira da a ƙaddamarwa Malam Lawan a duk inda a ka ganshi. Ɗaliban Sunna da jami'an tsaro kuma sun ce, ahir! Kar a je nan wajen! Wanda kuma ya ƙi ji, to ba ya ƙi gani ba!
Ni kuma na ƙara da cewa, maimakon zage-zage, duk wanda bai gamsu ba, to don Allah ya nemi zama da Malam Lawan, ko ya turo malaminsa, ko ya kai ƙara kotu, don a fito da laifin da a ke zargin Malam Lawan ɗin ya aikata, ko kuma gaskiyarsa ta wanke shi!
A kwana lafiya!
Mubarak Ibrahim Lawan