Tafarkin Tsira

Directions

Tafarkin Tsira Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Tafarkin Tsira, Kano.

ABUBUWA 30 DA SUKE RABA SOYAYAYA .MUSAMMAN TSAKANIN MAAU’RATA1. Rashin gaskiya da yawan ƙarya.2. Rashin amana.3. Cin ama...
03/10/2026

ABUBUWA 30 DA SUKE RABA SOYAYAYA .
MUSAMMAN TSAKANIN MAAU’RATA

1. Rashin gaskiya da yawan ƙarya.
2. Rashin amana.
3. Cin amanar juna.
4. Yawan zargi ba tare da hujja ba.
5. Rashin girmama juna.
6. Yawan zagi da cin mutunci.
7. Fushi da saurin ɓacin rai.
8. Kishi da ya wuce iyaka.
9. Sauraron maganganun mutane fiye da na abokin zama.
10. Kwatanta abokin zama da wasu.
11. Rashin nuna godiya da yaba wa juna.
12. Rashin kula da bukatun juna.
13. Yawan gardama kan ƙananan abubuwa.
14. Ɓoye matsaloli maimakon tattauna su cikin hikima.
15. Amfani da sirrin gida wajen kunyata abokin zama.
16. Rashin kula da lokacin da ake bukatar kulawa da tausayi.
17. Yawan amfani da waya da kafofin sada zumunta har a manta da juna.
18. Shigar da iyaye, abokai ko wasu mutane cikin kowace matsala.
19. Matsalolin kuɗi da rashin fahimtar yadda ake tafiyar da su.
20. Rashin cika alkawari.
21. Girman kai da ƙin neman afuwa.
22. Rashin yafiya da riƙe tsofaffin laifuka.
23. Rashin kyakkyawar mu’amala da iyalan abokin zama.
24. Rashin kula da addini da ibada.
25. Rashin samun lokacin zama tare da tattaunawa.
26. Yawan ɓoye sirri mai muhimmanci.
27. Cin mutuncin abokin zama a gaban mutane.
28. Rashin tausayi lokacin da ɗayan yake cikin damuwa.
29. Son kai da neman a biya bukatun mutum shi kaɗai.
30. Rashin tsoron Allah da rashin kiyaye haƙƙin juna.

Muhimmin abu: Soyayya ba kalamai kawai ba ce; tana buƙatar amana, girmamawa, haƙuri, sadarwa mai kyau, yafiya da tausayi. Idan waɗannan s**a samu, soyayya tana samun ƙarfi; idan s**a lalace, soyayya na iya raguwa ko ma ta gushe.

03/10/2026

Daga cikin lokutan da ake son yawaita Istigfari akwai farkon yini da kuma karshensa

01/10/2026
FALALAR ZIKIRI DA AMFANIN SA. 1. Yawan zikri yana korar sheɗan2. Yawan zikri yana jawo samun yardar Allah3. Yawan zikri ...
04/01/2026

FALALAR ZIKIRI DA AMFANIN SA.

1. Yawan zikri yana korar sheɗan
2. Yawan zikri yana jawo samun yardar Allah
3. Yawan zikri yana gusar da damuwa da baƙin ciki daga zuciya
4. Yawan zikiri yana jawo farin ciki da annushuwa da nasaɗi a zuciya
5. Yawan zikiri yana ƙarfafa zuciya da jiki.
5. Yawan zikiri yana haskaka fuska da zuciya
7. Yawan zikri yana jawo arziki
8. Yawan zikri yana jawo samun kwarjini da jin dadi da farin jini
9. Yawan yana jawo samun ƙaunar Allah ta'ala, samun ƙaunar Allah shine babban buri.
10. Yawan zikri yana jawo kusanci da Allah, har a wayi gari mutum ya samu matsayin ihsani.
11. Yawan zikri yana jawo komawa zuwa ga Allah ta'ala, cikin farin ciki
12. Yawan zikri yana buɗewa mutum kofa ta samun yarda, da kusanci (Alƙurbiyya) tsakanin sa da Allah ta'ala.
13.. Yawan zikri yana buɗewa mai yinsa babun ilmi, duk sanda ya yawaita ambaton Allah, zai ƙara sanin Allah ta'ala.
14. Yawan zikri yana buɗewa mutum matsayin ganin buwayar Allah ta'ala, da isar sa.
15. Yawan zikri zai sa Allah ya ambaci mai yawan yi, duk sanda ya Ambani Allah, shima zai ambace shi.
16. Yawan zikri yana raya zuciya domin zikri ga zuciya kamar kifi ne a cikin ruwa, yaya kifi yake kasancewa idan aka raba shi da ruwa? Haka mutum zai kasance idan baya ambaton Allah ta'ala.
17. Yawan ambaton Allah yana zama kamar abinci ga zuciya da rai.
18. Yawan zikri yana washe zuciya ya goge tsatsa daga cikin zuciya.
19. Yawan zikri yana kankare zunubi
20. Yawan zikri yana kare mutum daga ɗimuwa da gafala.
21. Yawan zikri idan yana sa tuna Allah a cikin yalwa da wadata , Allah zai fidda shi daga cikin halin tsanani.
22. Yawan zikri yana tseratarwa daga saukar azaba.
23. Yawan zikri yana jawo saukar nutsuwa da saukar rahma, da lulluɓewar Mala'iku,
24. Yawan zikri yana shagaltar da harshe ga barin giba da gulma da ƙarya Annamimanci, da ashariya.
25. Majalisin da ake zikri, sheɗan baya zama a wajan
Albarka tana sauka a Majalisin da ake zikiri.
26. Yin zikri yana kare mutum daga hasarar lokaci, da tashi da warin mushen jaki daga majalisi.
27. Duk wanda ya ambaci Allah a ɓoye, har ya yi hawaye don ganin girman Allah, zai shiga inuwar al'arshi ranar Alƙiyama.
28. Idan yawan zikri ya ɗaukewa mutum hankali, har ya zama baya rokon wata bukata, Allah zai bashi fiye da dukkan masu roƙo s**a roƙa.
29. Zikri shine mafi saukin ibada mara wahala kuma ga yawan lada.
30. Daga cikin falalar zikiri, yana jawo a dasawa mutum bishiya a gidan Aljanna, kamar yadda yazo a hadisi, Duk wanda ya ce Subhanallahil azeem wa bihamdihi.
31. Daga cikin falalar zikri, akwai Kalmomi guda biyu masu saukin faɗa akan harshe masu nauyi akan sikeli, abin ƙauna a wajan Allah, Subhanallahi wa bi hamdihi subhanallahil azeem.
32. Dawwama a cikin zikiri yana ƙare mutum daga taɓewa.
33. Za ka iya Zikri a kowane hali, babu sharaɗin sai da Alwala ko tsarki.
34. Yawan zikri haske ne, a duniya da ƙabari da makoma da siraɗi.
35. Yawan ambaton Allah shine tushen komai, idan ka sami arziƙin yawan sa ka gama sumun dukkan komai daga Allah.
36. Zikri yana kusanta abinda yake nesa, na buƙatu kuma yana nisanta abinda yake kusa, na damuwa da baƙin ciki.
37. Zikri yana tashin zuciya daga baccin gafala.
38. Yawan zikri yana jawo samun ɗanɗano mai faranta rai.
39. Mai yawan ambaton Allah, kada ka damu domin Allah yana tare da kai.
40. Yawan zikri yayi daidai da fita yaƙi da ciwar da dukiya mai yawa.
41.. Ambaton Allah shine tushen nuna godiya ga Allah, domin duk wanda baya zikri baya godiya.
42. Zikri yana jawo samun ni'ima daga Allah kuma yana tunkuɗe Sakar fushin Allah. Mafi darajar mutane a wajan Allah shine wanda harshen sa ya zamo ɗanye a wajan ambaton Allah ta'ala.
43. Allah ta'ala da Mala'ikun sa suna yin salati ga mai yawan ambaton Allah.
44. Yin zikri shine Asalin samun soyayyar Allah da tsira daga faɗawa cikin maƙiya Allah ta'ala.
45. Yawan zikri yana jawo a sami katon dausayi a cikin aljanna.
46. Majalisin zikri wajan zaman Mala'ikun Allah ne.
47. Dukkan ibadu da Allah ya yi umarni a yi babbar Manufar su shine yawan ambaton Allah.
48. Dukkan ibadar da ake ambaton Allah da yawa a ciknta tafi dukkan sauran ibadu kamar sallah bayan Tauhidi.
49. Yin zikri yana tsayawa a matsayin Sadaƙa da Aiyukan lada da ake yi da dukiya.
50. Ambaton Allah yana ƙara ƙarfin imani.
51. Yawan zikri yana sauƙaƙewa mutum duk wani abu mai wahala.
52. Yawan zikri yana jawo zaman lafiya da kwanciyar hankali.
53. Zirki yana zama kariya daga sharrin magauta da maƙiya, musamman zikirin safe da yamma, da lokacin bacci.
54. Yawan zikri yana ƙare mutun daga munafunci domin munafukai basa ambaton Allah da yawa.

Misalin zikri,لااله الاالله وحده لا شريك له له الملك وله الحمد وهو على كل شيء قدير
duk wanda ya karanta wannan zikri ƙafa 100, da safe zai sami abubuwa guda biyar:
Kamar ya ƴanta bayi goma, sai lada 100, za a kankare masa zunubi 100, zai zame masa tsari daga sheɗan a wannan rana har zuwa yamma, babu kuma wanda yazo da wani abu da yafi nasa a wannan rana. Bukhari da Muslim.

HANYOYIN (14) NA YAƘI DA LAIFUKA. Laifuka (lefuka) sune ayyuka ko halayen da s**a saba wa doka, addini, da tarbiyya, kam...
26/12/2025

HANYOYIN (14) NA YAƘI DA LAIFUKA.

Laifuka (lefuka) sune ayyuka ko halayen da s**a saba wa doka, addini, da tarbiyya, kamar su fashi da makami, sata, fyade, kisan kai, shaye-shaye, cin hanci, da dai sauransu. Yaduwar lefuka na janyo tabarbarewar al’umma.

1. Wayar da kan jama’a game da illar laifuka da kuma muhimmancin bin doka.

2. Samar da tarbiyya tun daga gida da makaranta har zuwa wajen aiki.

3. Karfafa darussa irin su tarbiyyar halayya, addini, da zamantakewa a cikin makarantu.

4. Tabbatar da cewa doka tana aiki bisa adalci da gaskiya.

5. Hanzarta shari’u domin hana jinkiri wanda ke kara jawo rashin yarda da tsarin shari’a.

6. Hukunta masu laifi ba tare da son kai ko nuna banbanci ba.

7. Horas da jami’an tsaro yadda za su kare rayuka da dukiyoyi tare da girmama ‘yancin dan Adam.

8. Samar da kayan aiki da isasshen albashi don kauce wa cin hanci da rashin aiki yadda ya kamata.

9. .Samar da ayyukan yi ga matasa:

Rashin aiki yana daga cikin manyan dalilan da ke jefa matasa cikin laifuka.

Hukumomi su samar da guraben koyon sana’o’i da ayyukan yi don rage zaman banza da shaye-shaye.

10. Hadin gwiwar iyaye da shugabannin addini

11. Iyaye su kasance masu kula da tarbiyyar ‘ya’yansu.

12. Malaman addini su ci gaba da yin wa’azi da karfafa kyawawan halaye.

13. Talauci na sa wasu su rikide su zama barayi ko masu aikata laifi.

14 . Wasu laifuka na faruwa ne saboda matsalolin kwakwalwa da damuwa, don haka a Samar da cibiyoyin kula da lafiyar kwakwalwa domin taimaka wa masu bukata.

Yaki da lefuka aiki ne na kowa da kowa: gwamnati, iyaye, malamai, shugabannin addini, da matasa. Idan aka hada kai wajen amfani da hanyoyin da s**a dace, za a iya rage yawaitar laifuka kuma a gina al’umma mai lafiya, adalci da zaman lafiya.

Allah ta'ala ya ba mu lafiya da zaman lafiya.

Address

Kano

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Tafarkin Tsira posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

Share