20/11/2025
SHARUDDA 4 DA MASUSSUKA YA GINDAYA KAFIN ZUWA MAKABALA
1- Dole zaa Basu damar ciga da Yan soshiyal midiya din su suma da zasu dunga yada makabalar kai tsaye, don kaucewa yada bangaranci.
2- Kuma so suke yi a nuna shi live, basa so a sirrinta.
3- Basu yadda Malaman Izala su kewaye Sheikh Masuss**a shi kadai ba, guda daya zaa ware suyi zaman tare da shi idan kuma Malamai da dama zaa yi zaman da su suma zaa baiwa bangaren Masuss**a damar shiga da malamai a bangaren sa adadin yadda zaa baiwa bangaren Izala.
4- Dole alkalan makabalar su zama daga bangarori daban-daban, Bangaren Shi'a da Darika da Kur'aniyyu da sauran su, ba wai kawai Yan Izala ba, kuma sai an lissafa musu sunayen su.
Sun tabbatar da cewar idan aka sake aka saba daya daga cikin dokokin to baza su halarci zaman ba.
Manunya, ta ruwaito cewar zuwa yanzu sun amshi takardar gayyata, suna sauran batun sharrudan da s**a gidaya kafin bayyana a gaban kwamitin.