25/05/2026
YAUMUL ARAFAH.
Rana ce mai tarin falala.
Rana ce ta dagewa da ayyukan nagarta!
Rana ce ta dagewa da addu'ah .
Itace mafi alkhairin wuni da rana ta hudo a cikinta!
خير يوم طلعت فيه الشمس
Ka da mu shagala da wasu ayyukan da za su shagaltar da mu , daga samun falalar wannan wunin mai tarin falala da girma!
Mu dage da addu'ah!
Mu dage da addu'ah!
خير الدعاء دعاء يوم عرفة
Annabi SalallaHu AlaiHi Wasallam Ya ce :"Mafi alkhairin addu'ah (ita ce addu'ar da akayi) ranar arafah".
Mu dage mu yi naci mu yi fadanci ga ALLÃH Mu Roke sa Zai Amsa Mana Addu'o'inmu Insha ALLÃH.
وخير ما قلت والنبيون من بعدي لا إله إلا الله وحده لا شريك له، له الملك وله الحمد وهو على كل شيء قدير.
Annabi SallaHu ALaiHi Wasallam Yace:- " Mafi alkhairin abunda na fadi Ni da Annabawa da s**a gabace ni ( A ranar Arafah) Shi ne :-
LA ILA HA ILLALLAHU WAHDAHU LA SHARIYKA LAHU, LAHUL MULKU WA LAHUL HAMDU WA HUWA ALA KULLI SHAY'IN QADIIR".
MU Dage d fadin wannan :-LA ILA HA ILLALLAHU WAHDAHU LÃ SHARIYKALAHU LAHUL MULKU WALAHUL HAMDU WA HUWA ALA KULLI SHAY'IN QADIYR.
ALLÃH YA KARBI IBADUNMU.
✍🏼Abdulsalam Abdullahi
9-12-1445H.
16-6-2024 C.E
TV