23/06/2026
AZUMIN TASU'A(9) DA ASHURA(10) Zai K**a Gobe Laraba Da Jibi Al-Hamis Ina ALLAH Ya Kaimu.
Mafi Falalar Azumi Bayan Azumin Watan RAMADANA Shine Azumin Watan ALLAH Na AL-MUHARRAM. (Sahih Al-Muslim 1163).
Mafi Falalar Azumi A Watan AL-MUHARRAM Shine Azumin ASHURA.
Azumin ASHURA Ranar Ne ALLAH Ya Halakar Da FIR'AUNA Ya Tseratar Da (Annabi MUSA Alaihissalatu Wassalam) Da Mutanen Sa Banu-Isra'il.
Azumin Ranar TASU'A Don A Saɓawa YAHUDAWA.
Azumin ASHURA Guda Ɗayan Nan Yana Kankare Zunuban Shekara Guda. (Sahih Al-Muslim 1162).
Daga Abu Sa'id:
Naji Manzon-ALLAHﷺ Yana Cewa; Duk Wanda Ya Azumci Yini Guda Don Neman Yardar ALLAH, ALLAH Zai Nisantar Da Fuskarsa Daga Wutar (Jahannama) Tsawon Tazarar Tafiyar Shekara Saba'in. (Sahihul Bukhari 2840).
Manzon-ALLAHﷺ Yace; Wanda Ya Shiryar Da Wani Abu Mai Kyau Yana Da Lada Kwatankwacin Wanda Ya Aikata.