15/08/2026
SAKON TA'AZIYA
Chairman Imam Muntaka Abdulmalik Yana Mika Sakon Ta'aziya ga Membobin mu Hajiya Hussaina Abdullahi Ahmad da Ahmad Abdullahi bisa Rasuwar Mahaifinsu.
Chairman Ya Bayyana kaduwa matuka da Jin labarin Rasuwar wannan Baba Namu Sannan Yayi Addu'ar Allah Yajikansa Yayi Masa Rahama da gafara.
Tuni Chairman Imam Muntaka Ya halarci Sallar Jana'izar Marigayin a yammacin jiya juma'a k**ar Yanda shari'ar Musulinci ta tanadar.
Haka Kuma Mataimakiyar shugabar Mata Hajiya Maimuna Abubakar ta wakilci shugaba Haj. Amira wajen jagirantar tawagar Mata zuwa ta'aziya a safiyar yau.
Signed state p.r.o Abbas umar Muhd