Qur'ani Da Hadisi

Qur'ani Da Hadisi Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Qur'ani Da Hadisi, Religious Center, Kano.

Manzon Allah (ﷺ) Ya ce:“Haƙiƙa, mafi munin mutane a wurin Allah a Ranar Alƙiyama shi ne wanda mutane suke guje masa domi...
11/08/2026

Manzon Allah (ﷺ) Ya ce:
“Haƙiƙa, mafi munin mutane a wurin Allah a Ranar Alƙiyama shi ne wanda mutane suke guje masa domin su kare kansu daga sharrinsa.”
[Bukhari]

An karɓo daga Abu Hurairah (Allah Ya yarda da shi) Ya ce:Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) Ya ...
27/07/2026

An karɓo daga Abu Hurairah (Allah Ya yarda da shi) Ya ce:

Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) Ya ce:

"Duk wanda ya yaye wa Musulmi wata damuwa daga cikin damuwoyin duniya, Allah zai yaye masa wata damuwa daga cikin damuwoyin Ranar Alƙiyama. Duk wanda ya rufe laifin wani Musulmi, Allah zai rufe laifukansa a duniya da kuma Ranar Alƙiyama. Duk wanda ya sauƙaƙa Mabuƙaci wani nauyi, Allah zai sauƙaƙa masa a duniya da Lahira. Allah yana taimakon bawansa matuƙar bawan yana taimakon ɗan'uwansa.

Duk wanda ya bi wata hanya domin neman ilimi, Allah zai sauƙaƙa masa hanyar zuwa Aljanna. Kuma babu wasu mutane da za su taru a cikin wani ɗaki daga ɗakunan Allah (masallaci) suna karanta Littafin Allah kuma suna koyar da juna shi, face mala'iku za su kewaye su, natsuwa za ta sauko a kansu, rahama za ta lulluɓe su, kuma Allah zai ambace a cikin waɗanda suke tare da Shi.

Kuma duk wanda ayyukansa munana s**a hana shi samun kaiwa gaci, asalinsa ko danginsa ba za su amfane shi da komai ba."

[Ibn Majah]

Manzon Allah (ﷺ) Ya ce:"Kada ku yawaita yin dariya, domin yawan dariya yana kashe zuciya ."[Tirmizi]
21/07/2026

Manzon Allah (ﷺ) Ya ce:
"Kada ku yawaita yin dariya, domin yawan dariya yana kashe zuciya ."
[Tirmizi]

Manzon Allah ﷺ Ya ce:“Ka yi watsi da duniya sai Allah Ya so ka; kuma ka yi watsi da abin hannun mutane, sai mutane su so...
06/07/2026

Manzon Allah ﷺ Ya ce:
“Ka yi watsi da duniya sai Allah Ya so ka; kuma ka yi watsi da abin hannun mutane, sai mutane su so ka.”
Sahih Jami’

Manzon Allah ﷺ Ya ce:Allah zai azabtar da waɗanda suke azabtar da mutane a wannan duniya (ba tare da wani sahihin dalili...
28/06/2026

Manzon Allah ﷺ Ya ce:
Allah zai azabtar da waɗanda suke azabtar da mutane a wannan duniya (ba tare da wani sahihin dalili ba).
[Muslim]

An rawaito daga A’isha (Allah Ya yarda da ita):Manzon Allah (ﷺ) yana karɓar alkawarin mubaya’a daga mata ne da baki kawa...
19/06/2026

An rawaito daga A’isha (Allah Ya yarda da ita):
Manzon Allah (ﷺ) yana karɓar alkawarin mubaya’a daga mata ne da baki kawai, bayan ya karanta Aya ta 12 cikin suratul Mumtahana “(…ba za su haɗa Allah komai wajen bauta ba.)”
Kuma hannun Manzon Allah (ﷺ) bai taɓa taɓa hannun wata mace ba, sai dai hannun macen da hannunsa na dama ya mallaka (wato bayinsa mata).

[Bukhari]

ku kiyayi Duniya da Mata
11/06/2026

ku kiyayi Duniya da Mata

Manzon Allah (ﷺ) Ya ce:"Mafificiyar addu'a ita ce addu'ar ranar arfa, kuma mafificin abun da Ni da Annabawan da su ka ga...
25/05/2026

Manzon Allah (ﷺ) Ya ce:
"Mafificiyar addu'a ita ce addu'ar ranar arfa, kuma mafificin abun da Ni da Annabawan da su ka gabace ni muka faɗa shi ne 'La ilaha illallahu waḥdahu la sharika lahu, lahul-mulku wa lahul-hamdu, wa huwa ala kulli shai’in ƙadir.'"
[Tirmizi]

Manzon Allah (ﷺ) Ya ce:"Mafificiyar addu'a ita ce addu'ar ranar arfa, kuma mafificin abun da Ni da Annabawan da su ka ga...
25/05/2026

Manzon Allah (ﷺ) Ya ce:
"Mafificiyar addu'a ita ce addu'ar ranar arfa, kuma mafificin abun da Ni da Annabawan da su ka gabace ni muka faɗa shi ne 'La ilaha illallahu wahdahu la sharika lahu, lahul-mulku wa lahul-hamdu, wa huwa ala kulli shai’in ƙadir.'"
[Tirmizi]

An rawaito daga Ibn Abbas cewa Manzon Allah (ﷺ) Ya ce:“Babu wasu kwanaki da ayyukan alheri s**a fi soyuwa a wurin Allah ...
20/05/2026

An rawaito daga Ibn Abbas cewa Manzon Allah (ﷺ) Ya ce:
“Babu wasu kwanaki da ayyukan alheri s**a fi soyuwa a wurin Allah kamar waɗannan kwanaki,” wato kwanaki goma na farkon watan Zul-Hijjah. Sai (Sahabbai) s**a ce: “Ya Manzon Allah! Ko jihadi a tafarkin Allah ma bai fi su ba?” Sai ya ce: “Ko jihadi a tafarkin Allah ma bai fi su ba, sai dai idan mutum ya fita da ransa da dukiyarsa, sannan bai dawo da komai daga ciki ba.”
[Ibn Majah]

Address

Kano

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Qur'ani Da Hadisi posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

Share