MSSN Jigawa S.L.U Branch

MSSN Jigawa S.L.U Branch KUNGIYAR MUSULMAI TA JIGAWA KARKASHIN JAMI'AR SULE LAMIDO UNIVERSITY KAFIN HAUSA DOMIN KAUKAKA KALMAR ALLAH DA KARANTAR DA AL'UMMAR MUSULMI.

MUSLIM STUDENTS' SOCIETY OF NIGERIA, JIGAWA AREA UNIT.Jigawa Higher Institutions Convention of Muslim Students (JHICOMS)...
29/10/2021

MUSLIM STUDENTS' SOCIETY OF NIGERIA, JIGAWA AREA UNIT.

Jigawa Higher Institutions Convention of Muslim Students (JHICOMS) at Binyaminu Usman Polytechnic Hadejia.

Ameer Shamsudden uthman
Sec. Mubarak Muhammad
PRO 1 Abubakar Muhammad
Sec 2 hauwa abdullahi
Treasurer: Mustapha Aliyu
PRO 2 zainab hashim
Programme coordinator: Hamza isah abdallah
Na'ibul ameer: Lawan Aliyu

✍️✍️✍️✍️
Abubakar Muhammad Guri
PRO MSSN
S.L.U BRANCH

09/09/2021

.

NA YI MANA NASIHA?

Matuƙar kana iya ɓata awanni 2, 3 ko fiye a 'chats' da karanta 'statuses' da 'posting' a social media, ko kallo 'season films' na awanni 3 - 5 a kullum, to tabbas da zaka daure, zaka iya sadaukar da abin da bai fi mintuna 30 ba, wajen yin Adhkar na safiya/maraice, ko Tilawar littafin Allah Mai tsarki (Alƙur'ani), ko motsa jiki, ko karanta wani littafi da zai amfani duniyarka da lahirarka.

Yanzu mun shiga wani lokaci da ɗabi'ar nan da Bature ke cewa 'Reading Culture' (ɗabi'ar karance-karance) ta ja baya, a wajen mutane da yawa, tun bayan yawaitar wayoyin hannu, daga shekarar 2010 - 2015, zuwa yau, 2021 [Sabre, 2019].

Ko a manyan makarantu (universities/colleges); mu ɗalibai, mu kan kukan an bamu takardu (handouts) ko littafai masu shafi da yawa, mu ƙi karantawa, da sunan shafukan sun yi yawa. Abin lura, idan har zaka iya zama, ka ɓata 1 ɗaya a kana iya karanta 'comment(s)', masana s**a ce; awa ɗaya ga mai ɗabi'ar karanta littafai, daidai take da karanta kalmomi 10,000 ko shafukan littafi 50 (50 pages) [Butler, 2014].

Shafuka 50 na iya karantuwa a wajen maras saurin karatu (slow reader) cikin awanni 3; ga matsakaici (average) awa ɗaya da rabi, ga mai sauri (faster) cikin ƙasa da awa ɗaya.

Lokaci! Shi ne kyauta mafi tsada da Ubangiji ya azurta bayi da shi. Kowa ya san, lokoci ba siyansa, ba kuma ya tariya (reverse). Manzon Allah ﷺ a hadisin "اغتنم خمساً قبل خمس", yana mana gargarɗi kan amfani da wannan dama ta rayuwa (lokaci). Don tun kana rayen ma, nauye-nauyen iyalin dake gabanka (reality na rayuwa), da wuya su barka ka yi atisayen gina kai, ta karatu, matuƙar baka gina ɗabi'ar ba tun kana matashi.

Idan kana zama da dattawa, in suna ma taɗin yadda s**a yi asarar samaratarsu, tare da nuna takaici na rashin amfani da lokacinsu, wajen gina kai da kuma karatu, in ka kwatanta dalilinsu na baya da kuma halin da matasan yau ke ciki, za ka ga tazarar ba ƴar kaɗan ba ce. Sai dai gyaran Allah.

08/09/2021

KUNGIYAR MUSULMAI TA JIGAWA KARKASHIN JAMI'AR SULE LAMIDO UNIVERSITY KAFIN HAUSA DOMIN DAUKAKA KALMAR ALLAH DA KARANTAR DA AL'UMMAR MUSULMI.

Address

Kafin Hausa

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when MSSN Jigawa S.L.U Branch posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share