BIN Annabi SAW NE Kawai shiriya

BIN Annabi SAW NE Kawai shiriya RIKO DA ALQUR'ANI DA HADISI SHINE ZAMAN LAFIYA GA MUSULMAI PAGE FOR SHARING
AN ISLAMIC ARTICLES | AUDIO |
VIDEO | THEMES |
JAVA APPS | EBOOKS
& OTHERS

25/05/2020

Hotuna: Yadda Sallar Idi Ta Gudana A Wasu Manyan Masallatan Jibwis Na Kasa. Assalamualaikum Warahmatullah Wabarakatuhu Dafari Munayiwa Kowa ...

17/12/2018
06/04/2018

Muna Godiya Ga Dukkanin Al Ummah

03/08/2017

*MUHADARA!! MUHADARA!!.*
*GAGARUMAR MUHADARA DAN
TAYA DAN'UWA ALH. JAMILU
SHESHE MURNAR AURE.*
*MAUDHU'I.*
*AHLUB BAITI.*
Malamai Masu Gabatarwa.
° *SHEIKH DR. ABDALLAH USMAN G/
KAYA (HAFIZAHULLAH) .*
° *SHEIKH LAWAN ABUBAKAR
SHUAIBU TRIUMPH (HAFIZAHULLAH).
*
° *SHEIKH ABUBAKAR ABDUSSALAM
BABAN GWALE (HAFIZAHULLAH).*
Gurin da za'a gabatar.
*SHESHE BAKIN BISHIYA KOFAR
GIDAN ALH. HAMISU MAI FADA.*
Ranar Alhamis
10/11/1438
03/08/2017
Lokaci :- Magrib Zuwa abunda ya
sawwaka.
*IDAN ANYI RUWA SAI RANAR
ASABAR INSHA ALLAH.*

11/07/2017

KA KARANTA ANATSE.
Misali.
Anyi wani mutun mai dukiya sosai
da sosai a wani qauye.
mutumin yafi kowa kud'i a
qauyensu kuma duk-kanninsa da
y'an uwansa suna amfa'nuwa da
kud'insa mahaifiyarsa ce kawai bata
amfa'nuwa da kud'insa kasancewar
bai da'mu da ya kula da ita ba.
Amma duk-kannin y'an uwansa
suna amfana da dukiyarsa. Don
haka nema ya zama shugaba a cikin
gidansu. Domin duk dokar da ya
kafah to kowa biyayya yake masa.
Sai dai duk da yawan dukiyar da
Allah ya bashi. Kwata-kwata bayayin
Sallah.
Kuma baya tina Uban gijinsa.
Sannan baya tina lahira.
Wata rana wannan mutumin yana
zaune akan kujerarsa ta qasaita. Sai
wani mutumin kirki yazo wajensa ya
riqa yima nasiha akan Sallah.
Sai mutumin yace: ai ni bana
buqatar inyi Sallah domin inada
dukiya mai yawa. Kuma y'an uwana
suna sona sosai
don haka babu abinda na rasa to me
zaisa inyi Sallah?
Mai nasiha yace masa: ai ita bautar
Allah badon duniya akeyinta ba.
ka tsaya kayi tinani y'an uwanka
dukiyarka kawai sukeso idan ka
mutu. Bazasu iya amfana maka
komai ba. Kai ko ragemaka rad'ad'in
azaba bai zama lallai suyi ba. Koda
kuwa sunada ikon yin haka.
mai dukiya yace qarya ne. Ai yadda
y'an uwansa suke sonsa to zasu iya
masa komai koda kuwa ransu zai
fita.
Mai nasiha yace: kanaso kaga
za'hirin abinda nake gaya maka?
Mai dukiya yace: Eh.
Sai mai nasiha yasa yaransa s**a
d'auko wani qa'ton akwa'ti. Sanna
yacema mai dukiya. Ko zaka iya
shiga cikin akwa'tinnan mu d'aukeka
mukaika gida mu gayama y'an
uwanka ka mutu.?
Mai dukiya yace: ba matsala. mai
dukiya ya shiga cikin akwa'ti ya
kwanta.
Aka d'auki akwa'ti. Aka kai gidan mai
dukiya. A katarad da mutanen gidan
sun taru suna hutawa a wata far-
fa'jiyar gidan.
Sai Aka gaya musu mai dukiya ya
mutu.
Nanfa s**aita iface iface. Suna kuka
mai tsanani.
Sai s**azo sunaso a bud'e musu
akwa-tin domin suyi masa kallon
qarshe.
Amma sai mai nasiha yace' A'a baza
a bud'e akwa-tin ba.
Sukace me yasa baza abud'e ba?
Mai nasiha yace: ku dai kun sani
cewa d'an uwanku baya Sallah don
haka yana mutuwa sai wani qa'to
miciji yazo ya shiga cikin akwa-tin
domin ya riqa yimasa azaba a cikin
kabari.
Amma akwai hanya 1 tak da za'a iya
bi. A ceceshi.
Hanyar kuwa itace: idan aka samu
mutum 1 daga cikin y'an uwansa
yazo ya sha'fi qafa'funsa to za'a
kwashe shekarun wannan d'an
uwan za'a baiwa mai dukiya. Kunga
idan akabashi shekarun. To ransa
zai da'wo zaici gaba da rayuwa.
Kuma zai tuba. Ya riqa yin Sallah ta
yarda Allah s.w.t zai yarda dashi.
ko a cikinku akwai wanda zai
taimaka masa ya bada shekarusa ga
mai dukiya?
Sai qannansa da yannesa s**ace
bazasu bada shekarunsu ba. Saboda
mai dukiya ya rayu. Tsawon shekaru
masu yawa amma baya Sallah don
haka bazasu bada shekarunsu ba.
aje akaishi kabari a haka.
Mai dukiya yana cikin akwa-ti yanajin
abinda ke fa'ruwa. Kawai sai yaji
ransa ya 6a'ci.
Mahaifin mai dukiya yazo yanata
kuka. Sai yace a bud'e masa akwa-ti
domin yaga d'ansa. Amma mai
nasiha ya gayama mahaifin irin
maganar da ya gayama y'an uwan
mai dukiya.
Mai dukiya yana kwance
a cikin akwa'ti yanaji abinda yake
faruwa sai ya riqa cewa a ransa
wannan mahaifina ne. Nasan zai
taimaka mini.
Amma sai mahaifin yace kukaishi
kabari ku binneshi.
Mai nasiha yace: to a kira y'ay'ansa
da matarsa wata qila su ceceshi.
Mai dukiya yana kwance a kwa'ti.
Yana cewa aransa ai y'ay'ana da
matata suna matuqar qaunata. Don
haka nasan zasu ceceni.
Amma sai matar taqi yarda. Y'ay'an
kuma s**ace aimu ya'ra ne muna
buqa'tar mu sha'qata a wannan
duniya. Don muji da'd'in dukiyar da
mahaifinmu ya bari. Don haka
akaishi kabari a binne.
Mai nasiha yace: Wannan mutumin
yayi doguwar rayuwa yana fa'futika
domin y'an uwansa da y'ay'ansa.
Amma yanzu an rasa ko mutum 1
daga cikinsu da zai ceceshi daga
wuta. Don haka muje mukaishi
kabari.
Duk wannan abu da yake faruwa
mai dukiya yana kwance a cikin
akwati yanaji. Kuma yana kuka.
Sai 1 daga cikin qannansa tace: ai
ba'a gayawa mahaifiyarsa ba.
Mai nasiha yace: aje a kirata.
Sai s**ace: ai bata iya tafiya. Koda
yaushe A kwa'ce take akan gado.
Mai nasiha yasa aka d'aukota. Aka
gaya mata ha'lin da ake ciki.
Mai dukiya sai cewa yakeyi aransa ta
yaya zata ceceni alha'li masoyana
sun ka'sa cetona. ita kuma tunda ta
daina tafiya na manta cewa inada
uwa
kawai sai mahaifiyar ta riqa kuka
tace ta yarda zata bashi shekarunta
da s**a rage.
Sai aka tambayeta don me zaki
ceceshi alha'li dukiyarsa bata
amfa'nar dake ba. Kuma ba
kyautata miki yake ba?
Sai tace: AI 'DANA NE. Nice na d'auki
cikinsa na riqa ciyar dashi daga jinina
ya hanani bacci da cin abinci. Don
haka bazan bari ya shiga wuta ba.
Mai dukiya yayi sauri ya fito daga
akwa'ti yana kuka ya nemi afuwar
mahaifiyarsa ya da''fa qafa'funta.
Sannan yace: Mahaifiyata daga yau
kece Aljannah ta ta duniya. Kuma
zan riqi Sallah ta zame mini
mabud'in Aljannah A lahira.
Admin 9. ALLAH S.W.T KA TAIMAKI
IYAYEN MU. Ka shige musu gaba

29/05/2017

Dr. Muhd Sani Umar R/lemo
Ramadaaniyyat-Kashi Na Biyu- (1)
Suratu Maryam
1. An saukar da ita a Makka kafin
hijirar Musulmai ta biyu zuwa kasar
Habasha.
2. Tana da ayoyi 99 a lissafin
mutanen Makka da Madina, amma a
lissafin mutanen Sham da Kufa
kuwa ayoyinta 98 ne.
3. Babban jigonta shi ne magana a
kan Tauhidi wato kadaita Allah da
bauta da kore masa ɗa ko abokin
tarayya, da tabbatar da zuwan ranar
tashin alƙiyama. Tubalan gininta
kuwa su ne ƙissoshi wadanda s**a
cinye kimanin kaso biyu bisa uku na
Surar.
4. An kira ta da suna Suratu Maryam
domin gabanin a saukar da ita babu
wata Sura da ta ba da labarin
Maryamu (AS) da ɗanta Annabi Isa
(AS). Sai daga baya ne Surar Ali
Imrana ta s**a da batu irin wannan.
5. An ambaci sunan Allah "Mai
rahama" har sau goma sha shida,
kamar yadda kalmar "Rahama' ta
maimaitu sau shida a cikinta, domin
mayar da martani ga mushirikai
masu jayayya da wannan suna.
Kamar yadda ya zo a Suratul Furkan
aya ta 60.
6. Allah ya ambaci labarin Annabi
Zakirya a farkonta don ya zama abin
koyi ga masu koyi, izana ga masu
ɗaukar izina. Ya bayyana yadda Allah
yake saukar da rahamarsa ga
zababbun bayinsa, ya biya musu
bukuta komai yadda ake ganin ba za
ta samu ba bisa ga lissafi na
ɗan'adam

*COMPLETE Karatun Littafin ﻤﻭﻘﻒ ﺍﻠﺸﻴﻌﺔﺍﻹﻤﺎﻤﻴﺔ ﺍﻻﺛﻨﯽ ﻋﺸﺮﻳﺔ ﻤﻥ ﺍﻠﺻﻭﻔﻳﺔ(Acikin Darussa 11)*Tare da: *Sheikh Ibrahim Usman (...
04/05/2017

*COMPLETE Karatun Littafin ﻤﻭﻘﻒ ﺍﻠﺸﻴﻌﺔ
ﺍﻹﻤﺎﻤﻴﺔ ﺍﻻﺛﻨﯽ ﻋﺸﺮﻳﺔ ﻤﻥ ﺍﻠﺻﻭﻔﻳﺔ
(Acikin Darussa 11)*
Tare da: *Sheikh Ibrahim Usman (Abu Malik)*
*>> Anya Ko 'Yan Dariqun Supaye sunsan
Matsayinsu a mahangar 'Yan Shi'a da suke daukar
su a matsayin 'yan uwa, Abokai ?*
*>> Yi kokari ka sauke Darussan wannan littafe
domin kaji haqiqanin Kallon da 'Yan Shi'a suke wa
Supaye*
001 http://darulfikr.com/s/15336
002 http://darulfikr.com/s/17102
003 http://darulfikr.com/s/18013
004 http://darulfikr.com/s/18329
005 http://darulfikr.com/s/18948
006 http://darulfikr.com/s/19259
007 http://darulfikr.com/s/19540
008 http://darulfikr.com/s/19748
009 http://darulfikr.com/s/20026
010 http://darulfikr.com/s/20098
011 http://darulfikr.com/s/20298
A ci gaba da aika ma wasu. Wanda ya nuna ma
wani aikin alheri yana da irin ladarsa.

-

01/05/2017

WAJIBI NE MUSULMI YA TSAYA
INDA SHARI'A TA CE YA TSAYA:
Daga AshSheik Dr. Ibrahim Jalo Jalingo Hafizahullah
Ba daidai ba ne musulmi ya
wuce-gona-da-iri game zatin
Annabi mai tsira da amincin
Allah; saboda nuna kauna da
girmamawa a gare shi; Imamul
Bukhaarii ya ruwaito hadithi na
3,445, da Imamu Muslim hadithi
na 1,691 cewa Annabi mai tsira
da amincin Allah ya ce:-
(( ﻻ ﺗﻄﺮﻭﻧﻲ ﻛﻤﺎ ﺃﻃﺮﺕ ﺍﻟﻨﺼﺎﺭﻯ ﺍﺑﻦ
ﻣﺮﻳﻢ ﺍﻧﻤﺎ ﺍﻧﺎ ﻋﺒﺪ ﻓﻘﻮﻟﻮﺍ: ﻋﺒﺪ ﺍﻟﻠﻪ
ﻭﺭﺳﻮﻟﻪ)).
Ma'ana: ((kada ku wuce gona da
iri cikin yabona, kamar yadda
Kirista s**a wuce gona da iri
cikin yabon Dan Maryam, ni ba
kowa ba ne face bawa, ku ce:
bawan Allah kuma manzonSa)).
Ga dai abin da Annabi mai tsira
da amincin Allah ya ce wa
al'ummarsa na hana su wuce
iyakar Sahari'ah cikin yabonsa;
watau su yi wata karya game da
shi da nufin yabo da
girmamawa. Sai dai kuma abin
bakin ciki a nan shi ne kadan ne
kwarai daga cikin wannan
Al'ummah tamu suke yin amfani
da wannan gargadi na Annabi
mai tsira da amincin Allah.
Misali: Ya zo cikin littafin
Jawaahirul Ma'anii 1/147 nassi
kamar haka:-
(( ﺍﻭﻝ ﻣﺎ ﺧﻠﻖ ﺍﻟﻠﻪ ﺗﻌﺎﻟﻰ ﺭﻭﺡ ﻣﺤﻤﺪ
ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﺛﻢ ﻧﺴﻞ ﺍﻟﻠﻪ ﻣﻨﻬﺎ
ﺃﺭﻭﺍﺡ ﺍﻟﻜﺎﺋﻨﺎﺕ ﺛﻢ ﻛﻮﻥ ﺍﻟﻠﻪ ﻣﻦ ﺟﺴﺪ
ﺍﻟﻨﺒﻲ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﺃﺟﺴﺎﺩ
ﺍﻟﻤﻼﺋﻜﺔ ﻭﺍﻷﻧﺒﻴﺎﺀ ﻭﺍﻷﻗﻄﺎﺏ )).
Ma'ana: ((Farkon abin da Allah
Ya halitta shi ne ran Muhammad
mai tsira da amincin Allah,
sannan ya halitta sauran
rayukan halittu daga shi
(wannan ran) sannan kuma Allah
Ya halicci jikkunan Mala'iku da
Annabawa da Manyan waliyyai
daga jikin Annabi Mai tsira da
amincin Allah))!
Tabbas babu gaskiya cikin
wannan magana da ta zo cikin
wannan littafi na Jawaahirul
Ma'aniy; domin ijama'in
Musulmin kwarai ya kullu a kan
cewa Annabi mai tsira da
amincin Allah yana daga cikin
zurriyyar Annabi Adam ne ba
wai shi Annabi Adam din ba ne
yake daga cikin zurriyyarsa;
saboda Allah Madaukakin Sarki
Ya ce cikin Suratul Hijri aya ta
28-29 :-
(( ﻭﺇﺫ ﻗﺎﻝ ﺭﺑﻚ ﻟﻠﻤﻼﺋﻜﺔ ﺍﻧﻲ ﺧﺎﻟﻖ
ﺑﺸﺮﺍ ﻣﻦ ﺻﻠﺼﺎﻝ ﻣﻦ ﺣﻤﺎ ﻣﺴﻨﻮﻥ .
ﻓﺈﺫﺍ ﺳﻮﻳﺘﻪ ﻭﻧﻔﺨﺖ ﻓﻴﻪ ﻣﻦ ﺭﻭﺣﻲ
ﻓﻘﻌﻮﺍ ﻟﻪ ﺳﺎﺟﺪﻳﻦ )).
Ma'ana: ((A lokacin da
Ubangijinka Ya ce wa Mala'iku
lalle ne ni Mai halittan wani dan
adam ne daga wani irin laka
busashshe, daga wani irin bakin
tabo jirkitacce, to idan na
daidaita shi, kuma na busa raiNa
cikin shi, to sai ku fadi kuna
masu yi masa sujjada)).
Sannan kuma Ya ce cikin
suratus Sajdah aya ta 7-8 :-
(( ﺍﻟﺬﻱ ﺃﺣﺴﻦ ﻛﻞ ﺷﻲﺀ ﺧﻠﻘﻪ ﻭﺑﺪﺍ
ﺧﻠﻖ ﺍﻻﻧﺴﺎﻥ ﻣﻦ ﻃﻴﻦ. ﺛﻢ ﺟﻌﻞ ﻧﺴﻠﻪ
ﻣﻦ ﺳﻼﻟﺔ ﻣﻦ ﻣﺎﺀ ﻣﻬﻴﻦ)).
Ma'ana: ((Shi ne wannan da Ya
kyautata dukkan kome da Ya
halitta shi, sannan Ya fara
halittar jinsin mutum ne da laka,
daga nan Ya yi zurriyyarsa daga
wani irin daskararren jini da
kuma wani irin ruwa
kaskantacce)).
Allah Ya taimake mu Ya tsare
mana imaninmu. Ameen.

Muhadara mai taken:*MUTANE BAKWAI (7) DA ALLAHTA'ALA ZAI MUSU INUWA RANARALKIYAMA*Daga bakin: *_Umar ShehuZaria_*Lahadi ...
30/04/2017

Muhadara mai taken:
*MUTANE BAKWAI (7) DA ALLAH
TA'ALA ZAI MUSU INUWA RANAR
ALKIYAMA*
Daga bakin: *_Umar Shehu
Zaria_*
Lahadi 03 Sha'aban, 1438,
(30/04/2017).
MUTANE 7 DA ALLAH TAALA ZAI
MUSU INUWA RANAR ALKIYAMA
http://darulfikr.com/s/20662
Daga: *ZAUREN FIQHUS
SUNNAH*
Ayi Sauraro Lafiya.
Kasance da darulfikr domin
samun karatukan malaman
sunnah a saukake.
Darulfikr.com taku ce domin
yada sunnah.

_

Address

Kaduna

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when BIN Annabi SAW NE Kawai shiriya posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share