25/08/2026
﴿ذَ ٰلِكَ بِأَنَّ ٱللَّهَ لَمۡ یَكُ مُغَیِّرࣰا نِّعۡمَةً أَنۡعَمَهَا عَلَىٰ قَوۡمٍ حَتَّىٰ یُغَیِّرُوا۟ مَا بِأَنفُسِهِمۡ وَأَنَّ ٱللَّهَ سَمِیعٌ عَلِیمࣱ ٥٣﴾ [الأنفال ٥٣]
Ma’ana:
Hakan kuwa saboda lallai Allah ba Ya sauya wata ni’ima da Ya yi wa wasu mutane, har sai su kansu sun sauya abin da yake cikin zukatansu da halayensu. Kuma lallai Allah Mai ji ne, Masani.
Wato: Allah ba Ya kwace wa mutane ni’imar da Ya yi musu, sai idan su ne s**a sauya biyayya zuwa saɓo, godiya zuwa butulci, da kyakkyawan hali zuwa mummunan hali. Wannan yana nuna cewa zunubai da sauya kyakkyawan hali suna daga cikin dalilan gushewar ni’ima.