18/07/2026
INNALILLAHI WA INNA ILAIHI RAJI'UN
Kungiyar Agaji ta Jama'atu Nasril Islam (JNI) tana alhinin rasuwar Malam Sale Jere, ɗaya daga cikin farkon 'Yan Agaji na Masallacin Sultan Bello, Kaduna.
Marigayin ya sadaukar da rayuwarsa wajen hidimtawa addinin Musulunci da al'umma cikin aminci da jajircewa. Muna roƙon Allah Maɗaukakin Sarki Ya gafarta masa, Ya yalwata masa rahama, Ya haskaka kabarinsa, Ya sanya Aljannatul Firdausi ta zama makomarsa, Ya kuma bai wa iyalansa da al'ummar Musulmi haƙurin jure wannan babban rashi.
Amin Ya Rabbal Alamin.