27/04/2022
AN TARAWA MARAYU NAIRA MILIYAN 10 DA KAYAYYAKI MASU YAWA A KADUNA
Kwamitin Marayu dake ƙarƙashin kungiyar Izala reshen Jihar Kaduna a Majlisin Tafseer na Sheikh Dr. Abdulkadir Saleh Kazaure sun Sanar da cewa an samu Gudunmawar Naira Miliyan 10 da Buhun Shinkafa 120 da Buhunnan hatsi da Atamfofi da kayayyaki masu yawa daga Hannun al'ummah
Daga fara Tafsirin zuwa jiya ne aka tara wannan kudi da kayayyaki masu yawa inda aka raba su ga Marayun a fadin Jihar da kuma kwamitocin Marayu na Kanan hukumomin Kaduna da Makarantar Marayu ta kungiyar dake Kafin Allah Gaba.
ALLAH Swt ya sakawa kowa da alkhairi ya sanya a mizanin Lada ya taimaki masu taimakon al'ummar sa. Amin