Izala Online

Izala Online Wannan shafine Wanda zai dinga kawo maku kratuttukan Malaman Sunnah, a duk fadin Nigeria.

TSARABA...  GAME DA HUDUBAR INYASS WACCE YAYI A SUDAN   WACCE  ACIKI YA BAYYANA CEWA QUDURCE CEWA KOMAI ALLAH NE WANNAN ...
04/08/2020

TSARABA... GAME DA HUDUBAR INYASS WACCE YAYI A SUDAN WACCE ACIKI YA BAYYANA CEWA QUDURCE CEWA KOMAI ALLAH NE WANNAN SHINE HAQIQANIN MA'ANAR LA'ILAHA ILLALLAHU.

GA LINK DIRECT MASU FAHINTAR LARABCI SU SHIGA SU KARANCE TA GABAKI DAYA ZASU GA ABINDA MUKA FADI TARE DA TA'ALIQINSA AKAN MAGANAR AHMADU TIJJANI INDA TIJJANI YACE WANNAN HALITTUN GABAKI DAYANSU ALLAH. NE. YA BAYYANA DA SURARSU DA SUNAYENSU DA SIFFOFINSU, SAI.INYASS YA GASKATA WANNAN FAHINTA TA AHMADU TIJJANIY

FADAKARWA:

NA DAYA:
KA KARANCE HUDUBAR GABAKI DAYA ANAN NE ZAKA FAHINCI IRIN KWABAR DA INYASS YAYI A WANNAN HUDUBAR.

NA BIYU:
IDAN MUKA GA AN GOGE WANNAN HUDUBAR A NAN GABA DAGA WANNAN SHAFI WANDA WANNAN LINK DIN DA ZAN BAYAR BA ABIN MAMAKI BANE DOMIN WANNAN BA BAQON ABU BANE YAN TIJJANIYYA SUNA BOYE KASUSSUNANSU DA LITTAFANSU IDAN AUKAJI AN. FARA BANKADO MUSU ASIRI.

YA ALLAH KA SHIRYI MASU NEMAN. GASKIYA KU SHIGA NAN KU KARANTA KUYI HUKUNCI DA KANKU:

Daga Dan uwanku Abubakar zubair abu Aisha

👇

متى كانت زيارة الشيخ للسودان ؟من معه فى الصورة ؟

28/07/2020

Bayani akan Addu'a bayan sallar Farilla

28/07/2020

Nasiha daga bakin Sheikh Dr. Tukur Adam Al Mannar Kaduna.

23/07/2020

Sako zuwaga Shugaban tsageru

ABUBUWAN DA SUKE JAWO S**A, ZAGI, DA CIN MUTUNCIN MALAMAI GUDA (13)1- Rashin ɗaukar karatu agaban malamai, se ɗauka a li...
23/07/2020

ABUBUWAN DA SUKE JAWO S**A, ZAGI, DA CIN MUTUNCIN MALAMAI GUDA (13)

1- Rashin ɗaukar karatu agaban malamai, se ɗauka a littattafai.

2- Mutum ya ƙone bai tafasa ba, Wato baza su tsaya suyi karatun ba Allah Allah suke suma su ɗare minbari, Allah Allah suke suma su zama masu fatawa su zama masu lakca yaƙi haƙura yayi karatu.

3- Nuna illimin Alhali babu illimin, bai ma yi illimin ba amma zai nunawa mutane shi mai illimi ne.

4- Yana dubawa a littattafai wani malamin yayi magana akan wani malamin wani malamin ma haka, maganar da su kayi da ijtihadi ko ta'awali ko Saboda wani dalili na illimi kamar Abinda muka sani (illimin jarhu da ta'adil) wanda an kafa shine domin tantance hadisan manzon Allah (s.a.w) domin ware ingantacce da wanda ba ingantacce ba Saboda haka shi idan yana karanta waɗannan sai yace to ah ai magabata sun sossoki junansu, don haka mai zai hana nima inyi s**a ga wadanda muke tare dasu, wannan shima sai yaje fashi cikin wata talaɓa ɓiya da ba zai iya fita ba.

5- Wata ƙila zai ce yana kwaikwayon ibn hazm Abu Muhammad aliyu ibn hazm Azahiry, wanda littatafansa Suna ɗauke da s**a ga malamai manya manya, Toshi a tarinhinsa akwai dalilai da yasa yayi haka :-
Na farko :- Yawanci karatun sa ba'a hannun malamai yayi su ba, kamar yadda Ashaɗiby ya faɗa a cikin Almuwafaƙat.
Na biyu :- Ya haɗu da ƙiyayyane mai zafi ta malaman zamanin sa, yaga bala'i iri iri, harƙona masa laburarinsa gaba ɗaya anyi, shi yasa idan ya tashi sai ya ragargaje su baki ɗaya, to kai me akayi ma a yanzu, an ƙona maka laburarin ka ne ko an matsa maka ne, don me zaka kwaikwayi ibn Hazm.

6- Jahiltar darajar wanda kake s**a, matuƙar baka zauna da mutum ba, ba kayi rayuwa dashi ba, yana yiwuwar ka jahilci matsayinsa. To kaga dole ka jingi na masa Abinda ba shine ba, wata ƙila da kasanshi da ba zaka faɗi abinda kafaɗa akan sa ba.

7- Wasu Suna tasirantuwa da irin abubuwan da ke faruwa a ƙasashen yamma na turai, na damukuraɗiya da freedom of speech, musanman ma waɗanda s**a rayuwa a can.

8- Ra'ayin riƙau na ƙungiyanci, saboda haka duk wanda baɗan ƙungiyar saba to baya kallonsa da daraja, Saboda haka sai ya taɓa wanda bana shi ba, Amma idan antaɓa nashi to baza'a zauna lafiya ba.

9- Hassada da rigima akan wani shugabanci.

10- Rashin tsayawa a tabbatar da abu, yayin da kaji an faɗi wani abu batare da bincike ba caraf sai ka ɗauketa kayi ta yaya tata, shikenan se a shiga s**ar wanda bai jiba bai gani ba.

11- (ALFARAG) :- Rashin abunyi, zaune yake bashi da abun yi, yana da lokaci ishaishe to kuma babu abinda zaiyi, ƙarshe se kaga ya shiga abinda ya shafi giba da annamimanci da s**ar wanɗanda ba suji ba basu gani ba.

12- Mutumin da ka taimaka masa ko karantar dashi mai makon ya dinga tuna Wannan wafa'i naka na cewa ka karantar dashi sai yaji bashi da wannan, duk ranar da yaji shima ya taka minbari ko ya iya tsayawa a cikin jama'a sai ya faɗa s**ar ka, bacin da shi yake yabon ka.

13- Neman shuhura :- mutum yana ganin bazai sami shahara ba sai ya soki malamai, ya taka kafaɗar wani sannan a hango shi.

DR. MUHAMMAD SANI UMAR R/LEMO, A Lakcar Dayi Akan Darajar Malamai Da Illimi A Kaduna Masallacin Al-manar.

✍🏼 Bukhari Musa Adam

المعتقد الصحيح الواجب على كل مسلم اعتقاده استقلالا، والرد على من أنكر تقسيم التوحيد ضمنا .الكنوي طالب شيخ موسى أسد السنة...
23/07/2020

المعتقد الصحيح الواجب على كل مسلم اعتقاده استقلالا، والرد على من أنكر تقسيم التوحيد ضمنا .الكنوي طالب شيخ موسى أسد السنة أطال الله عمره في خدمة الإسلام والسنة.

Allah ka Kara Kare mana Mallam Musa Yusuf Asadussunnah daga dukkan sharrinda ke kokarin bullowa.
23/07/2020

Allah ka Kara Kare mana Mallam Musa Yusuf Asadussunnah daga dukkan sharrinda ke kokarin bullowa.

Duk mai ilimi dayake da fahimta yasan cewa daban fahimtar da Sheikh Ibn Taimiyya yayi wa Hakika. Amman yan Dariqu sunce ...
23/07/2020

Duk mai ilimi dayake da fahimta yasan cewa daban fahimtar da Sheikh Ibn Taimiyya yayi wa Hakika. Amman yan Dariqu sunce Wai ai yan hakikansune Ibn Taimiyya yake nufi. Allah ka bamu ganewa.

23/07/2020

Amman idan anyi Magana sai s**e ba hakaba. Allah ka shiryar damu.

Allah ya jikan Mallam
23/07/2020

Allah ya jikan Mallam

GANIN ANNABI A FARKE: Haƙiƙa ko Ruɗu?Lallai ya tabbata cikin Hadisi Mutawatiri cewa; duk wanda ya ga Annabi (saw) a ciki...
16/07/2020

GANIN ANNABI A FARKE: Haƙiƙa ko Ruɗu?

Lallai ya tabbata cikin Hadisi Mutawatiri cewa; duk wanda ya ga Annabi (saw) a cikin mafarki, yana bacci to lallai shi ɗin ya gani a bisa haƙiƙa, ba wani sheɗani ne ya rikeɗe ya zo a kamanninsa ba.
Babu saɓani a kan wannan. Saboda abu ne da aka sani bisa dole a Addinin Muslunci.

To amma daga baya an samu wasu Sufaye suna iƙirarin ganin Annabi (saw) a farke - ba a mafarki ba -, -wai- har suke iƙirarin haɗuwa da shi ido da ido, har ya ba su wani abu na ilimi ko ibada, na zikirori da wuridai da salatai.
Ta wannar hanya aka samu Ɗariƙun Sufaye, kamar Ɗariƙar Tijjaniyya, wacce Shehu Tijjani ya yi iƙirarin ya haɗu da Annabi (saw) a zahiri, ya gan shi a farke, har ya ba shi Ɗariƙa. Ta haka s**a samo "Salatul Fatih".

To Sufaye suna raya cewa; suna da madogara a kan wannar da'awa tasu, inda suke cewa; hujja a kan haka ita ce Hadisin da Imamul Bukhari ya ruwaito a cikin Sahihi nasa kamar haka:
«من رآني في المنام فسيراني في اليقظة، ولا يتمثل الشيطان بي»
صحيح البخاري (9/ 33)

"Duk wanda ya ganni a cikin mafarki to zai ganni a farke, saboda Shaiɗan ba ya kamantuwa da ni".

To da wannan Hadisi Sufaye s**a ce lallai ana ganin Annabi a farke a nan Duniya. Amma sai dai sauran Malaman al'umma gaba ɗaya sun yi watsi da wannar fahimta, saboda dalilai guda biyu:

1- Lafazin Hadisin yana da rikitarwa, saboda dalilai masu yawa.
2- Kuma ko da ya tabbata Annabi ya faɗi haka, to lallai Hadisin bai Nassanta GANIN ANNABI A FARKE A DUNIYA BA.

Saboda haka, idan muka dauki dalili na farko, wato kasancewar Hadisin yana da rikitarwa, Malamai sun faɗi haka ne saboda wasu dalilai:
(1) Wannan lafazi (فسيراني في اليقظة) ya saɓa ma sauran lafuzan da s**a zo cikin sauran Hadisan.
(2) Abin da Sufaye suke zato daga Hadisin, na cewa; Hadisin yana nuna za a IYA GANIN ANNABI A NAN DUNIYA, ya saɓa ma wasu dalilai na Shari'a da Hankali da Waƙi'i, da Ƙiyasi da Lura.

To in mun ɗauki dalili na farko, wato cewa; lafazin (فسيراني في اليقظة) ya saɓa ma sauran lafuzan da s**a zo cikin sauran Hadisan, za mu ga cewa; da ma Malaman sanin illa da kuskuren da ke cikin Hadisi ingantacce suna da wata ƙa'ida kamar haka:
الباب إذا لم تجمع طرقه لم يتبين خطؤه

"Hadisin da ya zo a wata mas'ala, idan ba a tattara dukkan hanyoyinsa da riwayoyinsa an yi nazarinsu ba to kuskuren da ke cikinsa ba zai bayyana ba".

Manyan Malaman Hadisi ne s**a gindaya wannar ƙa'ida, kamar su Imam Aliyu bn al-Madeniy inda ya ce:
«الباب إذا لم تجمع طرقه لم يتبين خطؤه»
الجامع لأخلاق الراوي للخطيب البغدادي (2/ 212)

Imam Ibnu al-Mubarak ya ce:
«إذا أردت أن يصح لك الحديث فاضرب بعضه ببعض»
الجامع لأخلاق الراوي للخطيب البغدادي (2/ 295)

Imam Ahmad ya ce:
«الحديث إذا لم تجمع طرقه لم تفهمه والحديث يفسر بعضه بعضا»
الجامع لأخلاق الراوي للخطيب البغدادي (2/ 212)

Imam Ibnu Ma'een ya ce:
«لو لم نكتب الحديث من ثلاثين وجها ما عقلناه»
الجامع لأخلاق الراوي للخطيب البغدادي (2/ 212) المجروحين لابن حبان ت حمدي (1/ 35)

Saboda haka wannar ƙa'ida ce a wajen Malaman Hadisi, dole a tattara dukkan hanyoyi da lafuzan Hadisi don a tantance dadai daga kuskure.

Dan haka ya kamata mu yi nazarin hanyoyin Hadisan da lafuzansu, don gano inda kuskure da matsalar da aka samu a wannan Hadisi suke.

To, shi dai wannan Hadisi na ganin Annabi (saw) a mafarki Sahabbai goma sha biyu (12) ne s**a ruwaito shi ko fiye da haka. Su ne Abu Huraira, Abu Ƙatada, Anas, Jabir, Ibnu Mas'ud, Abu Sa'eed al-Khudriy, Abu Juhaifa, Ibnu Abbas, Ɗariƙ, Aliyu bn Abi Ɗalib, Abu Bakrah, da Abdullahi bn Amr (ra). Amma duk cikinsu babu wanda aka ruwaito ganin Annabi (saw) a farke (wato a lafazin "فسيراني في اليقظة") daga gare shi sai Abu Hurarah shi kaɗai. Ma'ana; wannar riwayar da aka yi daga gare shi ta saɓa ma ta sauran Sahabbai (11).

To shi Hadisin Abu Huraira, Bukhari ya ruwaito shi a wurare guda uku (3), Muslim a wuri ɗaya, haka Abu Dawud, Tirmiziy, Ibnu Majah da Imamu Ahmad a wurare 10 ko fiye da haka.

To duk da cewa; inda aka ruwaito waɗannan Hadisan a cikin littatafan Hadisi ya kai wuri (44) ko fiye, amma duk da haka a wuri ɗaya ne kaɗai daga wurare uku (3) Bukhari ya ruwaito Hadisin daga Abu Huraira da lafazin "فسيراني في اليقظة" a yanke ba shakka.

Amma ga yadda sauran s**a zo kamar haka:
(فقد رآني)، (فقد رآى الحق)، (فكأنما رآني في اليقظة)، (فسيراني في اليقظة أو فكأنما رآني في اليقظة).

To a nan sai mu lura da abubuwa kamar haka:
(1) Bukhari ya ruwaito Hadisin mafarkin a wurare shida (6), daga ciki ya ruwaito Hadisin Abu Huraira (ra) a wurare uku (3), amma daga ciki wuri ɗaya ne tak ya zo da lafazin (فسيراني في اليقظة).

(2) Muslim, Abu Dawud da Ahmad sun ruwaito Hadisin Abu Hurairan (ra), da irin Isnadin Bukhari, amma da lafazin shakka, kamar haka (فسيراني في اليقظة أو لكأنما رآني في اليقظة).

(3) Ibnu Hajar ya ambaci cewa; a wajen Isma'iliy - (المستخرج على صحيح البخاري للإسماعيلي) - yadda lafazin yake shi ne: (فقد رآني في اليقظة) a maimakon faɗinsa (فسيراني). Inda ya ce:
"ووقع عند الإسماعيلي في الطريق المذكورة "فقد رآني في اليقظة" بدل قوله: "فسيراني".
فتح الباري لابن حجر (12/ 383)

TO WANNAN SHI YA NUNA CEWA; WANNAN LAFAZI KUSKURE NE, BA SHI NE LAFAZI NA DADAI A HADISIN BA, HAR MA MALAMAI S**A YI ISHARA GA CEWA; LAFAZI NE "SHAZZI" BA "MAHFUZI" BA.

Ibnu Hajar ya naƙalto daga al-Maziriy ya ce:
وقال المازري: إن كان المحفوظ فكأنما رآني في اليقظة فمعناه ظاهر
فتح الباري لابن حجر (12/ 385)

In ka ji ana maganar "Mahfuz" to kishiyarsa shi ne "Shazzi", wanda ya saɓa ma sauran riwayoyi na Hadisin.

Kuma shi ne abin da Ibnu Hajar ɗin ya ambata cewa:
"وشذ بعض الصالحين فزعم أنها تقع بعيني الرأس حقيقة"
فتح الباري لابن حجر (12/ 384)

Saboda haka a bisa haƙika wannan lafazi da ya zo a Hadisin Abu Huraira (ra) ya saɓa ma sauran lafuza na riwayoyin Hadisin nasa, kuma ya saɓa ma Hadisan sauran Sahabbai. Saboda haka riwaya ce ta kuskure. Ba za a kafa hujja da ita ba.

2- Dalili na biyu; ko da a ce wannan lafazi na (فسيراني في اليقظة) ba kuskure ba ne, to a bisa haƙiƙa ba NASSI ba ne a kan GANIN ANNABI A NAN DUNIYA. A cikin Hadisin babu inda aka bayyana cewa; ganin nasa a nan Duniya zai kasance. Don haka "ihtimali" zai shiga cikinsa. Wannan ya sa wasu Malaman s**a fassara lafazin da cewa a Lahira ake nufi.
Imamu Nawawiy ya ce:
"وإن كان "سيراني في اليقظة" ففيه أقوال:
أحدها المراد به أهل عصره ومعناه أن من رآه في النوم ولم يكن هاجر يوفقه الله تعالى للهجرة ورؤيته صلى الله عليه وسلم في اليقظة عيانا
والثاني معناه أنه يرى تصديق تلك الرؤيا في اليقظة في الدار الآخرة لأنه يراه في الآخرة جميع أمته من رآه في الدنيا ومن لم يره
والثالث يراه في الآخرة رؤية خاصته في القرب منه وحصول شفاعته".
شرح النووي على مسلم (15/ 26)

Saboda haka ko da an sallama cewa; lafazin (فسيراني في اليقظة) "Mahfuzi" ne ba "Shazzi" ba, ma'ana; ya tabbata daga Annabi (saw), TO BA NASSI BA NE A KAN HAƊUWA DA ANNABI DA GANINSA A NAN DUNIYA, shi ya sa Malamai s**a yi tawilinsa, saboda an samu dalilai masu yawa da s**a tabbatar da cewa; Annabi (saw) ba zai dawo wannar Duniya a irin wannar rayuwa ba, b***e har a ce ya haɗu da wani mutum, har a yi ƙaryar an karɓi wani abu na Addini daga gare shi.

3- Daga cikin abubuwa da suke bayyana cewa; wannar ma'ana da Sufaye s**a riƙe kuskure ce, ai ya tabbata mutane da yawa sun yi mafarkin Annabi (saw), amma kuma daga baya ba su zo sun ce sun gan shi a farke ba. Alhali - a bisa fahimtar Sufayen - indai mutum ya yi mafarkin Annabi (saw) to dole sai ya gan shi a farke ido da ido, saboda Annabi (saw) in ya faɗi abu dole sai ya faru. Ibnu Hajar ya ce:
أن جمعا جما رأوه في المنام ثم لم يذكر واحد منهم أنه رآه في اليقظة وخبر الصادق لا يتخلف
فتح الباري لابن حجر (12/ 385)

4- Kuma hatta cikin Sahabbai sun yi mafarkin Annabi (saw), amma ba a ruwaito da Isnadi ingantacce, cewa; wani cikin Sahabban ya gan shi a farke ko ya haɗu da shi ba. Duk da tsananin buƙata zuwa ga haɗuwa da shi ɗin, don warware matsaloli da saɓani da s**a yi afkuwa a zamaninsu, amma ba a taɓa jin wani Sahabi ya ce: ya ga Annabi a farke har ya ba da mafita ko ya warware wani saɓani da s**a yi ba, wanda har yaƙe - yaƙe sun yi a tsakaninsu.

Saboda haka a bisa haƙiƙa LAFAZIN (فسيراني في اليقظة) KUSKURE NE, YA SAƁA MA SAURAN HADISAN. Da ma kuma ƙa'idar Malaman Hadisi - kamar yadda Ibnul Madeeniy ya faɗa - ita ce:
«الباب إذا لم تجمع طرقه لم يتبين خطؤه»
الجامع لأخلاق الراوي للخطيب البغدادي (2/ 212)

Sai ka tara riwayoyin Hadisin, sannan sashe ya fassara sashensa, kamar yadda Imamu Ahmad ya faɗa:
«الحديث إذا لم تجمع طرقه لم تفهمه، والحديث يفسر بعضه بعضا»
الجامع لأخلاق الراوي للخطيب البغدادي (2/ 212)

Saboda haka, a ƙarshe, kar ku yi mamaki don Ƴan Ɗariƙu sun yi jayayya, sun ja sun kafe a kan wannan lamari, saboda idan s**a sallama ba a ganin Annabi a farke, to dole su yarda cewa; Shehu Tijjaniy maƙaryaci ne, ya musu ƙarya ya ce: -wai- ya haɗu da Annabi (saw), har ya ba shi Ɗariƙa, wani kuma aka ba shi "Salatul Fatih". Ka ga girma ya faɗi kenan, ka ga daga nan duka Ɗariƙar ta rushe A to Z, gayya ta watse.

Address

Sabon Gari
Kaduna

Telephone

+2349071229648

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Izala Online posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share