21/10/2021
MAULIDI NA (1)DAGA FASSARAR LITTAFIN NURUL BASARI NA SHEIKHUL ISLAM.
بسم الله الرحمن الرحيم
وصلي الله علي الفاتح المبعوث رحمة للعالمين.
نور البصر في مدح سيد البشر في سيرة النبوية.
إِدِّكَارُ الأَحْبَابِ بَلْبَلَ بَالِي #فَغُرُوبِي تَهْمِي لِذَالبَلْبَالِ
إِدِّكَارُ الأَحْبَابِ
yawan tuna masoya (wato shugaba maaiki da sahabban sa da iyalin sa)ko kace tuna tarihin masoya wato shugaba da jamaar sa.
بلبل بالي
Ya motsar da zuciya ta ya hana ta natsuwa,maana ya motsar da soyaiyar da ke zuciya,domin masoyi yana motsuwa iadan antuna masoya.
wannan shi ke nuna masoyi na haqiqa,domin wani ko ya tuna masoya babu abun da zaiji,amma shi masoyi na haqiqa dama bai manta ba ballantana ya tuna,yawan tunanin shi ne ruhin zuciya domin shi ke motsar da ita.
فغروبي تهمي
hawaye na tana ta zuba,ko gugunan hawaye na tana ta zuba.
wato anan shehu ya sifanta idanun sa masu jawo hawaye da ke zuba daga ruwan idon sa saboda tuna masoya da ruwan da ake debowa da guga daga rijiya ko wani wurin kamar kogi da manyan guguna,idan aka ba wannan fassara maana ta guguna na hawaye.
لذالبلبال
Saboda wannan motsuwa ta tuna masoya halina ya kasance haka.
فَاشْتِيَاقِي إِلَيهِمُ وَغُرَابُ ال #بَينِ أَغْرَي الجُفُونَ بالتّهْمالِ
فَاشْتِيَاقِي إِلَيهِمُ
duk begena ya tabbata ne zuwaga wannan masoya.
والغراب البين
Sedai cewa ita hankakar rarraba..
wato larabawa su kan bada misali ne da hankakar rarraba idan abu ya nisanta saboda:
Lokacin da Annabi Nuhu ya hau jirgin ruwa shida mutane masu imani,to sai ya tura hankaka ta je ta binciki wurin da za su iya sauka wato inda babu ruwa,
sai hankaka ta tafi bata dawo ba
Wato tai nisa ta tafi inda baa aiketa ba.
to sai larabawa ya zama su na buga misali da duk abun da yai nisa ba zai dawo ba da hankaka ta rarraba.
Wato shehu na nufin ni mai yawan shauqi zuwaga zamanin Shugaba ne,saidai shi wannan zamani ya nisanta wato ya wuce ba zai dawo ba.
Shi ne yake cewa
Begena ya tabbata zuwa gare su,saidai halin da ake ciki shi ne hankakarnan ta rarraba,wato mai raba masoya da masoyi imma idan ya zama zamanin su ba daya ba,ko kuma suna nesa ta yadda mutum ba zai iya haduwa da su ba.
أغري الجفون بالتهمال
wanda hakan ya cunama makyaftai na yawan zubar hawaye.
وأَنَا سَهرَانُ وهَزْهَزَنِي هَبْ #بُ رِياح مِنَ البِقَاءِ العَوالِي
وأنا سهران
Ni inamarashin barcin dare,wato shehu nacewa na kasa barcin dare saboda tuna wannan masoya.
هب الرحياح من البقاع العوالي
Motowar iska daga wurin da ake kira da awaly.
هزهزني
shi ne ya girgiza ne.
Shi awa'li ko a'liyatu wani wuri ne agarin madina.
idan kaje za ka samu wannan wuri ya na wurin gabas masu kudu da madina.
To kasan shi masoyi yana bada misali da motsuwar soyaiya da iska mai motsawa,maana yana nufin tuna wannan wurare yana motsar da ni kamar yadda isak ke motsar da itace idan ta so daga wurin da ake kira da awaliy.
amma wannan ba shi ne manufa ba.
domin su bayin Allah su na jin kan shin masoyan su komi nisa, kamar yadda iska ta dakkoma Annabi yakub kanshin rigar Annabi yusuf daga nesa.
to irin su shehu suna tare da jin kamshin masoyi shugaba komi nisa a duk lokacin da iskar soyaiya ta kada daga zuciyar su, ko kuma idan ta kada na zahiri daga wurin da ake kira da awali sai ta dakko kanshin wannan masoya zuwa gare su, abun da ya zama muujiza ga Annabawa ba mamaki irin sa ya zama karama ga bayin Allah.
Atakaice
tasowar iska mai cike da kanshin
masoya wadda take raurawar dani saboda tasowar ta daga wurin da ake kira da awali, wato wdda ta ke hana ni natsuwa,to itace ta hana ni barcin dare.
فتَنَتْنِي تِلكَ البِقاءُ وهَاجتْ #،فِكرتِي إذخُصّت بخير الرِّسالِ
فتنتني تلك البقاء
sona da Wancanin ka wurere,wato wadancan wurare da nike tunawa,to wannan so shi ne ya ya dame ni.
هاجت فكرتي
tunani na inji shehu ta motsa ko takan motsa,saboda tuna wannan wurare.
إذ خصت بختم الرسال
Saboda cew Ankebanci wannan wuri
Da mai tambarin manzanci.ko cika makin manxanci.
إِيهِ فِكرِي مدحَ الأمينِ ولا تع، # بأ ,قصورًا عَن درك ذاكَ المَجَال
فكري
Ya kai tunani na,wto shehu yana magana da tunanin sa ne aanan,tunanin na zuciya da na kwakwalwa.ko kuma tunani na soyaiyar shugaba, domin tunani acikin wani abu to ya kan bada wata hikima ta Allah.
ko kuma kamar yadda muka sani Allah ne yai umarni ai tunani acikin abubuwa da yawa, to idan aka yi shi da zuciya mai kyau Allah zai cika hikima acikin sa, to shehu tunanin sa ya tafi wurin so da yabon shugaba:
جل فكري في معالي #أحمد الجم النوال
to shiyasa shehu yake kiran wannan tunani nasa da ya fitar da wannan yabo da Allah ya zuba acikin sa, domin Allah nacewa:
إِنَّ فِى ذَٰلِكَ لَءَايَٰتٍۢ لِّقَوْمٍۢ يَتَفَكَّرُونَ.
amma acikin sufanci sai muce ruhin shehu mai haske shi ne yake kiran tunanin shehu, domin idan ruhi yai haske sai ya rinjayi kowace gaba ta jikin dan ADAM wurin tafiya zuwaga Allah daganan sai ya motsar da tunani wurin isar da manufar Allah ,to shiyasa shehu yace:
فكري
Ya kai tunani na
إيه مدح الأمين
ka kara min,ko kai tai mana zance na
yabon amintancen Allah,ya kai tuna ni na kaita fitomin da yabon amintacce.
صلي الله عليه وسلم.
ولا تعبأ قصورا
Kada ka damu da Takaitawa acikin wannan yabo,wato karka taba takaitawa.
عن درك ذاك المجالي
ga barin riskar wannan fage,wato kaita yabo har ka isa zuwaga fage na masoya masu yabon shugaba
Wato ya kai tunani na,kaita kara min yabon amintacce,ko kaita min magana da yabon amintacce,karka sake ka damu da takaita wannan yabo,kai tayin wannan yabo har ka isa zuwaga fage na masu yabo ko masoya ko kuma fage na fadar shugaba, domin yabo yakan kai mutum wannan fage.
عَلِّلينِي بِمَدْحِهِ ونشُرِيهِ #نَشْرُ مَدحَ الأَمِينِ نَشرَ المَقَالِ
علليني بمدحه
Ki shayar da ni sha na biyu,ko kace ki shayar dani yabon sa sha bayan sha wanda babu yankewa acikin sa ya ke wannan tunani.
ko shagaltar da ni da wannan yabo.
Da yabon sa,wato ki shagaltar dani ko ki shayar dani da yawan yabon sa..
ya na magana ne da tunanin sa ko ruhin sa.
وانشريه
Ki watsa wannan yabo ki daidaita shi acikin jikina da harshe na har ya bayyana kowa ya ji shi.
نشر المدح الأمين
Watsuwar yabon shugaba amintace.
نشر المقال
To shi ne ya zamo abun watsawa ko daidaitawa aciki zance na da magana ta.
domin kowa da labarin da yake yadawa, ni yabon sa shi ne abun yadawa awurina.
قَلِّدينِي بِمَدحِهِ بِعُقُودٍ #تَزدَرِي في البَهاءِ نَظمَ اللَّئَالِ
قلديني بعقود
ya ke wannan tunani, Kiratayamin tsakiya ko muce sarka zinare maanar ki rataya a wuyana.
sarka ta zinare, wato abun da ake ratayawa a wuya na sarka kamar zinare ko murjani kodai wata sarka mai tsada .
wato yana nufin ya ke tunani na,kimin ado da yabon shugaba kamar yadda ake ado da da sarkar zinare da ake sakata awuya.
من مدحه
Saboda yabon shugaba
صلي الله عليه وسلم.
تزدري
wanda zata wulakanta ko wadda zatafi,wato ki ratayamin sarka mai tsada ta zinare wadda zata fi kuma ta wulakanta duk sarkuna da ake sakawa a wuya.
Nan shehu yana nufin yakai tunani na,ko ya ke wannan hadara ta shugaba.
ki bani damar yabon ki fiye da na sauran masu yabo.
anan ya sifanta yabon shugaba da sarka mai tsada da ake sakawa awuya.
تزدري
wadda zata wulakanta ko tafi
نظم اللآلي في البهاء
Tsararren lua' luai acikin kwarjini.
Luuluu,wani abu ne mai tsada da ake ado da shi,ana samo shi ne acikin ruwa,..
Kasan luu luu idan antsara shi aka jera shi yana matukar kyau.
To shi ne shehu ke nufi da yabon sa ya zama cikin tsari tamkar wannan lua'luai masu kyau da tsari.
maana tafi ta sauran masu yabon shugaba
Abun nufi shi ne
ki ratayamin tsakiya ko sarka ta zinare saboda yabon shugaba,
wannan sarka tafi ko ta wulakanta tsararren luuluu masu kwarjini a ido.
Allah ya kara yarda ga shekhul islam.
Amma a sufanci irin na su shehu maanar ba ta tsaya kan misalin zinare ko iya tsara waka kamar luuluu ba.
A sufance hakan na nufin sunayen matsayi ne da bayin Allah ke samu wanda kowa keda alamar sa a fadar shugaba.