26/08/2026
INNĀ LILLĀHI WA INNĀ ILAIHI RĀJIʿŪN
Cibiyar Nazarin Afirka dake ƙarƙashin Haramin Abulfadlil Abbas mai Tsarki tana miƙa saƙom ta’aziyyarta ga Sheikh Ibrahim Usman Ali Na’ibi daga Garin Kano bisa rasuwar matarsa.
A sakamakon wannan babban rashi mai girma da raɗaɗi,Cibiyar Nazarin Afirka tare da dukkan ma’aikatanta da shugabanninta, tana miƙa saƙon ta’aziyya mai zafi da jaje zuwaga Sheikh da iyalansa masu daraja baki ɗaya.
Muna roƙon Allah Maɗaukakin Sarki Ya gafartawa marigayiyar yasa ta huta,Ya lulluɓe ta da yalwar rahamarsa da yardarsa, ya kuma haɗata da Manzo da iyalansa Tsarkaka.
Sannan yaba iyalanta da ‘yan uwanta
haƙurin wannan babban rashi.