30/09/2026
A madadin Zawiyyatu As-Habis Safeenah Tijjaniyya Faidha Ibrahimiyya, Li-Sheikh Ahmad Rufa’i RTA, Kawo Kaduna,
Muna farin cikin gayyatar ’yan’uwa masoya Fiyayyen Halitta, Annabi Muhammad Sallallahu Alaihi Wasallam, zuwa babban taron Mauludi, tare da Maukibi, wato Zagayen Garin Kawo.
Wannan gagarumin taro zai gudana ne a ranar:
LAHADI, 4 GA OKTOBA, 2026.
Za'a fara MAUKIBI, wato ZAGAYE, zai fara ne da misalin ƙarfe 9:00 na safe.
Wurin tashi na zagaye shi ne Kofar Gidan Sheikh Muhammad Inuwa Fagge RTA, inda za a ratsa yankuna da layukan Kawo, har zuwa banban Filin Kwallon Kafa na Kawo.
Akwai dokoki da ƙa’idoji na zagaye waɗanda ake so kowa ya kiyaye, domin samun nasara da kuma tabbatar da tafiyar zagayen cikin tsari da lumana musamman makarantun islamiyoyi da kungiyoyin sha'irai.
Bayan haka, da dare, da misalin ƙarfe 8:30 na dare, za a gudanar da babban MAULUDIN ANNABI MUHAMMAD SALLALLAHU ALAIHI WASALLAM, a Filin Kwallon Kafa na Kawo, Kaduna.
Ana gayyatar malamai, shugabanni, matasa, dattawa, maza da mata, da ɗaukacin masoya Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam, domin halartar wannan babban taro na tunawa da rayuwa, ɗabi’u da koyarwar Fiyayyen Halitta, Annabi Muhammad Sallallahu Alaihi Wasallam.
UBAN TARO:
Mai Martaba Sarkin Zazzau,
Amb. Ahmad Nuhu Bamalli.
MAI MASAUKIN BAKI:
Alh. Dahiru Yahaya,
Sarkin Kawo.
SANARWA:
Kwamitin Maukibi da Mauludi na Garin Kawo.