08/07/2026
YADDA AKA GABATAR DA BIKIN YAYE ƊALIBAN AL-AKRAM ISLAMIC ACADEMY KUDAN KARO NA FARKO
A ranar Talata, 7 ga Yuli, 2026, makarantar Al-Akram Islamic Academy Kudan ta gudanar da bikin yaye ɗalibanta karo na farko a ɓangaren Junior Secondary School (JSS 3). Bikin ya gudana cikin tsari da armashi, tare da halartar iyayen ɗalibai, malamai, baƙi da sauran masu ruwa da tsaki a harkar ilimi.
An fara taron ne da addu’a, sannan aka gabatar da karatun Alƙur’ani Mai Girma. Bayan haka aka shiga kai tsaye cikin shirye-shiryen da s**a haɗa taron.
Gabatar da Takardun Bincike (Paper Presentations)
Ɗaya daga cikin abubuwan da s**a fi jan hankali a wannan biki shi ne gabatar da takardun bincike (Paper Presentations) da ɗaliban da aka yaye s**a shirya.
Jimillar ɗalibai 17 ne aka yaye, kuma kusan kowannensu ya gabatar da bincikensa a gaban mahalarta taron cikin ƙwarewa da jajircewa.
Takardun da ɗaliban s**a gabatar sun taɓo fannoni daban-daban na rayuwa, ilimi, fasaha da ci gaban al’umma. Daga cikin batutuwan da aka gabatar akwai:
* Cyber Safety and Digital Footprint Awareness – Khadija Sulaiman
* The Importance of Educating the Girl Child – Mubaraka Halilu
* Mental Health Awareness – Fatima Ibrahim
* Social Media and Mental Health – Sadiya Bashir
* Vocational Skills vs University Degree – Khadija Umar
* How Technology is Used in Modern Classrooms – Fatima I. Junaidu
* Climate Change and Local Actions – Khadija Isiya
* Critical Thinking – Muhammad Hamisu
* The Rise of Artificial Intelligence (AI) – Hammad Hamisu
* Time Management in the Age of Distractions – Ali Abdulƙadir
* Financial Literacy – Muhsin Khalid
* Modern Agriculture – Husaini Nuhu
* Modern Leadership – Sa’adatu Hasan
Kowane ɗalibi ya gabatar da nasa binciken tare da cikakken bayani da hujjoji, inda s**a bayyana muhimmancin batutuwan ga rayuwar al’umma da ci gaban ilimi.
Domin sauƙaƙa fahimta ga mahalarta taron, Malama A’isha Aliyu ta kasance tana fassara bayanan da aka gabatar zuwa harshen Hausa.
Hakika, ɗaliban sun nuna ƙwazo, jajircewa da ƙwarewa wajen gabatar da takardunsu, abin da ya samu yabo daga mahalarta taron.
Gasar Muhawara (Debate Competition)
Bayan kammala gabatar da takardun bincike, aka shiga kashi na biyu na shirin, wato Gasar Muhawara (Debate Competition) tsakanin Senior Section da Junior Section.
An gudanar da gasar cikin natsuwa da gogayya mai armashi, inda kowane ɓangare ya nuna ƙwarewa, basira da hazaka wajen kare hujjojinsa.
Bayan kammala gasar da alƙalai s**a tantance sakamakon, an bayyana cewa:
* Junior Section – Maki 310
* Senior Section – Maki 285
Saboda haka, Junior Section ne ya lashe gasar da tazarar maki 25.
Wannan nasara ta nuna irin ƙoƙarin da ɗaliban Junior Section s**a yi wajen shiri da kuma nuna hazakarsu. Haka kuma, ta zama abin ƙarfafawa ga Senior Section domin su ƙara ƙaimi da himma a shirye-shiryen da za su biyo baya.
Wakilan Junior Section da s**a lashe gasar
Waɗanda s**a wakilci Junior Section a gasar su ne:
* Abu-ɗalib Ishaq
* Safinatu Auwal
* Amina Yunusa
Muna taya su murna tare da addu’ar Allah Ya ƙara musu ilimi, basira da nasara a rayuwarsu.
Godiya da Jinjina
Makarantar Al-Akram Islamic Academy Kudan tana miƙa godiya ga iyayen ɗalibai, baƙi, malamai da dukkan waɗanda s**a halarci wannan gagarumin biki.
Haka kuma, muna jinjina ga malamai da s**a yi aiki ba dare ba rana wajen tarbiyya da koyar da ɗalibai har s**a kai wannan matsayi.
Ba za a manta da ɓangaren Media na makarantar ba, waɗanda s**a taka muhimmiyar rawa wajen yaɗa bayanai da ɗaukar dukkan abubuwan da s**a gudana. Allah Ya saka musu da alheri.
A ƙarshe, muna taya dukkan ɗaliban da aka yaye murna, tare da yi musu fatan Allah Ya sa wannan ya zama mafarin samun manyan nasarori a rayuwarsu. Allah Ya ci gaba da ɗaukaka makarantar Al-Akram Islamic Academy Kudan, Ya albarkaci malamanta, ɗalibanta da iyayensu. Amin.
Ma'ahadur Rasul Al-Akram - Nigeria
9/7/2026