Hisbah U/mu'azu Detachment

Hisbah U/mu'azu Detachment Official page for updates, Da’awah, community awareness, and activities of Hisbah U/Muazu Detachment. Working for discipline, peace, and moral values.

Assalamu Alaikum.'Yan'uwa maza da mata na wannan gunduma, wannan hoto an ƙirƙire shi ne ta hanyar fasahar AI (Artificial...
25/07/2026

Assalamu Alaikum.

'Yan'uwa maza da mata na wannan gunduma, wannan hoto an ƙirƙire shi ne ta hanyar fasahar AI (Artificial Intelligence). Sai dai saƙon da ke cikinsa yana da muhimmanci, kuma muna isar da shi ga daukacin al'ummarmu, musamman mazauna Gundumar Mu'azu da Kinkinau.

Muna roƙon Allah (SWT) Ya ƙara wa kowa ƙwarin gwiwa da hikima wajen kula da tarbiyyar waɗanda ke ƙarƙashin kulawarsa, domin gina al'umma ta gari.

Amin.

25/07/2026


23/07/2026

Big shout out to my newest top fans! Adam Abubakar, Abul Hisham, Dan Izala, Abdoul M Usman, Itz Real Engr Ismail, Sa'adu B Musa, Abdulmumini Bala Kabawa

Jami'in Hulda da Jama'a(P.R.O) na Gaishe ku. kuyi masa addu'a Allah yasa ya gama da duniya lafiya.19/07/2026.
19/07/2026

Jami'in Hulda da Jama'a(P.R.O) na Gaishe ku. kuyi masa addu'a Allah yasa ya gama da duniya lafiya.

19/07/2026.

Fadakarwa daga Hisbah
17/07/2026

Fadakarwa daga Hisbah

Assalamu Alaikum.Tunatarwa Ga Masu Faɗa a Ji da Iyaye Kan Muhimmancin Tarbiyyar YaraHisbah U/Mu'azu Detachment na kira g...
12/07/2026

Assalamu Alaikum.

Tunatarwa Ga Masu Faɗa a Ji da Iyaye Kan Muhimmancin Tarbiyyar Yara

Hisbah U/Mu'azu Detachment na kira ga dukkan shugabannin al'umma, masu faɗa a ji, iyaye da masu ruwa da tsaki da su ƙara himma wajen kula da amanar tarbiyyar yaran da Allah Ya ɗora musu.

A wannan lokaci da ake ci gaba da fuskantar matsalolin lalacewar tarbiyya, ya zama wajibi kowa ya sauke nauyin da ke kansa. Ana ci gaba da samun matsaloli irin su shaye-shaye, shirye-shiryen da ke lalata tarbiyya, haɗa DJ a wuraren da bai dace ba, da sauran ɗabi'u marasa kyau da ke jawo gurɓacewar tarbiyyar matasa.

Abin takaici, yanzu har ana samun ƙananan yara masu shekaru ƙasa da goma sha biyu (12) suna faɗawa cikin shaye-shaye da sauran munanan ɗabi'u. Wannan babban abin damuwa ne da ke buƙatar haɗin kan iyaye, shugabanni da daukacin al'umma.

Mu sani cewa Allah Madaukakin Sarki zai tambaye mu game da amanar da Ya ba mu. Saboda haka, kada mu yi shiru idan muka ga abin da ke lalata tarbiyyar al'umma. Wasu na da ikon taimakawa wajen dakile miyagun ayyuka amma suna yin sakaci ko ƙin ba da haɗin kai.

A baya-bayan nan an samu rahotannin yawaitar ayyukan da s**a saɓa wa addini da ɗabi'a, ciki har da zina, shaye-shaye, da kuma wasu munanan laifuffuka da ke barazana ga makomar al'ummarmu. Wannan yana nuna cewa lokaci ya yi da kowa zai tashi tsaye domin kare tarbiyyar 'ya'yanmu da makomar jikokinmu.

Muna kira ga kowa da kowa da ya ba da gudummawarsa wajen yaƙi da duk wani abu da ke lalata tarbiyyar al'umma. Idan muka haɗa kai, da izinin Allah za mu samu al'umma mai tarbiyya, zaman lafiya da kyawawan ɗabi'u.

Allah Ya kiyaye al'ummarmu, Ya shiryar da 'ya'yanmu, Ya kuma ba mu ikon sauke amanar da Ya ɗora mana. Amin.

Hisbah U/Mu'azu Detachment
12/07/2026

12/07/2026

Assalamu'alaikum Al'ummar musulmi.

Masha Allah.Ranar Juma'a data gabata kenan 26/06/2026 jami'an Hisbah tare da limamun masallacin juma'a na Seeta bnt abdu...
01/07/2026

Masha Allah.

Ranar Juma'a data gabata kenan 26/06/2026 jami'an Hisbah tare da limamun masallacin juma'a na Seeta bnt abdul'aziz dake kasan makabarya.

Allah ya kara ma jami'ai iklasi, Allah ya boya ku da gidan Aljanna.

01/07/2026

Allahu Akbar.Marigayi Rabi'u Musa Shugaba ya kasance jami'in Hisbah kafin rasuwarsa.mutumin kirki.Muna roƙon Allah Maɗau...
29/06/2026

Allahu Akbar.

Marigayi Rabi'u Musa Shugaba ya kasance jami'in Hisbah kafin rasuwarsa.

mutumin kirki.

Muna roƙon Allah Maɗaukakin Sarki Ya ci gaba da haskaka kabarinsa, Ya gafarta masa, Ya yi masa rahama, Ya sa Aljannatul Firdausi ta zama makomarsa.

Ya Allah kasa mucika da imani.

29/06/2026

Muna taya Kwamandan Hisbah na Unguwar Mu'azu murnar dawowa gida lafiya daga gudanar da ibadar Hajji.Muna roƙon Allah Maɗ...
25/06/2026

Muna taya Kwamandan Hisbah na Unguwar Mu'azu murnar dawowa gida lafiya daga gudanar da ibadar Hajji.

Muna roƙon Allah Maɗaukakin Sarki Ya sanya an yi Hajji karɓaɓɓe, Ya gafarta zunubai, Ya karɓi addu'o'i da ibadu, Ya kuma sa wannan tafiya ta zama alheri da albarka gare shi da iyalansa.

Allah Ya maimaita mana da alheri.

Barka da dawowa daga aikin Hajji, Allah Ya sa Hajji Mabrur. 🤲🕋

Hisbah Media Team 25/06/2026

Allah ya ka kara ma jami'an Hisbah kwarin gwiwa akan aikin da sukeyi.
24/06/2026

Allah ya ka kara ma jami'an Hisbah kwarin gwiwa akan aikin da sukeyi.

Address

Na'ibi Street U/mu'azu Kaduna
Kaduna South

Telephone

+2347037674096

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Hisbah U/mu'azu Detachment posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

Share